Inason labarina ya gangaro lokacinda na Fara zuwa ABU, Lokacinda na Fara rayuwa a ABU saboda nayi tsintuwa, babbar tsintuwa wadda Bazan taba Mantawa da ita ba. Rayuwar gaba daya understanding shi ne komai, na yadda Allah yana bude maka wata kofar bayan Ya rufe wata, amma bamu realising hakan har Se gaba. Ko ni ban fahimci inda rayuwata take nufa ba seda na hadu da ABDALLAH, nasan zakuce Abdallah again? Yes Abdallah again.
Amina hostel shi ne hostel dina a ABU, Kamar yadda nace muku direct entry na samu to level 2, ban wani sha wahala ba, saboda I believe duk Wanda Yayi SBRS to bana tunanin akwai school din da zaije yaji wahala kuma. Ko a karatu ko a copping stuffs na environment da yanayin lectures. Shiyasa ko kadan banyi wahala ba. Lecture sosae Ya kankama, babu laifi na dan Fara Sabo da mutane, musamman roommates dina, dukda kowacce course dinta daban amma idan muna tare irin da daddare Zaa zauna ayi hira kowacce akan gadonta, muna muntata juna saboda kowa yasan limit dinsa, ba Wanda ke crossing boundaries dinshi.
Ranar alhamis lokacin Munyi watanni biyu a second semester Dan tuni na share first semester, kuma ni nayi highest points a class dinmu, so yawancin duk an sassani hakanan.
Komai ya zama very deep, ana ta test ga exams ta kusa. Ni daya na taho daga hostel, Ina sanye da Abaya Off White se na dauki wani karamin veil peach na rufe kaina dashi. Daidai kofar dakinsu Nanah na tsaya tareda lekawa nace
"Nanah zamu makara fa! "
Da sauri ta janyo veil dinta ta fito, hannunta jotter ce Se handout Ko hand bag bata dakko ba. Tare muka jera muna tafe muna hira yawanci duk akan exams ne. Nanah Habib sunanta, gaba dayanmu Human physiology muke karantawa, asalinta yar Maiduguri ce, sede Ita Tundaga level 1 ta Fara, fresher ce Ko nace jambite ce. Muna shiri da ita sosae a class, shiyasa muka kulla kawance abinmu. Se Amjad shikuma Dan bauchi ne, tare muke dashi, he's a good friend also.
Muna zuwa class muka zauna inda muka saba zama, mu ba a karshen class ba, ba kuma a farko ba, a middle na ajin, anan muke zama abinmu. Cardiovascular physiology muke dashi, lecturer mace ce Mrs. Hassanah Uba. matar bata fashi bata latti amma Yau kam abin mamaki Har to Nine bata zo ba, kasancewar exams ta kusa, babu Wanda ya damu duk se muke dudduba handouts dinmu, masu discussion nayi, a Haka Har Karfe Tara daidai naji class din yayi Shiru, tsit babu ko motsin kirki, hakan yasa na dago da sauri dan ganin waye ya shigo, OMG! Oh Allah! Tsarki Ya tabbata ga Allah makagin abinda nake gani a gabana, shi ne abinda ya Fara zuwa raina.
Namiji ne me suna namiji, ba muna mata ba, Bashida haske amma skin dinshi bai cika duhu ba, yafi kama da caramel color, fuskarshi round face ce, wadda Allah Ya halitta mata komai daidai da ita, komai fits a inda yake, babu abinda zaka kalla kace da Haka yake da yafi! No everything is just perfect as it is. Yanada average height kuma jikinshi daga yadda yake a tsaye irin kamammen jikinnan ne. Dukkanmu yawancin mu da muke class din kallonshi muke, baga mata ba baga maza ba.
Seda ya gyara tsayuwarshi, ya daidaita system dinshi da tuni ya fito da ita daga cikin back pack dinshi, eyeglasses ya sanya sannan ya ciro chilled Faro daga Jakar ya daddaka, wajen rabi sannan Yayi recapping bottle din, ya aje a gefe.
Anan ya dago idanunshi Yana bin class din da kallo cikin wani unreadable expression na wajen mintina biyar, se kuma ya saki Murmushi Wanda yasa cleft dinsa lotsawa, naga hakan saboda tsira mishi idanu da nayi ne. Can yace cikin murya wadda turanci Ya mamaye ta
"I'm Abdallah Ahmad Abdallah...... "
Banma karasa jin abinda ya fada ba, kawai na saki Tsaki, Ashe class din duk Sunyi Shiru, kuma kowa ya jiyo yana kallona. Ganin Haka na bata rai amma Se naji shima Yayi Shiru bai karasa abinda yake fada ba, se ma sakkowa da yayi ya nufo inda nake, dauke kaina nayi inajin yadda zuciyata ke wani irin bugawa saboda ban taba kawowa yaji tsakin da nayi ba, yadda takun kafarshi ke isowa kunnena, haka zuciyata ke tsananta bugawar da take.