*Please take a moment and pray for Ladingo.... Has daughter Fareesa has gone missing, May Allah almighty protect her wherever she's and may she return home safely Unharmed*
Wani irin Murmushi na farin ciki Maina Ya saki yana zaune office dinshi Ya gama clerking patients na ranar, Sanye yake cikin tuxedo shirt da Armani jeans Wanda suka kayatar dashi, Maina is handsome and charming, badai Yayi shiga Ka kusheba, sake kallon system dinshi yayi yana Kara karanta email din da ya shigo na releasing dinsa da akai zuwa Russia dan Karin Karatu. Kanshi Ya shafa yana adduar bayannar Lulu kafin ya kammalla karatunnan, Dan idan ya gama bata nan to Bashida wani excuse kuma na rashin aure. Yasan dole ne ya auri ko Wacece, don Alhajin sama ya bashi last chance akan idan ya dawo shekaru hudu kenan to ko bai kawo Macen da yake so ba, Alhaji yace aure zai masa.
Duk satin duniya se yayi istikhara na neman Zabin Allah, amma for once bai taba jin jiran da yake yiwa Lulu bata lokaci bane, shidai kawai yana jin wani abu me girma yana jiranshi. To daya zauna bata lokacinshi yaga is more better yaje Yayi Neurosurgery (likitan laka) shekaru uku yake ganin Zaiyi tunda dama yanada exposure sosae kan aikin.
Ammiey na kitchen itada Rukayya da Nafisa suna hada burabiskon shinkafa, Gabaki daya gidan Ya turare da kamshin abincin. Ga wata lafiyayyar taushe da Amna ta hada. Suna kammallawa kowa ya fito Rukayya nata bacin rai Dan duniya babu abinda ta tsana Kamar shiga kitchen bata so bata kuma kaunar hakan, amma ya zatayi tunda Salima ta haife ta, gwara gwara gidan Hafsa idan kaje ita da kanta take girkinta, to Lokuta da dama can take guduwa. Dukkansu parlour suka zauna Nafisa na kara tambayar Ammiey Wasu abubuwan. Tana ta bata amsa Tana jin dadi, kafar ta tasa ta hauri bayan Rukayya ganin yadda take tura baki Tana canja canja channels
"Aike kam Naga me tsautsayin da zai kwashe ki, yarinya bata son a more ta Se son jiki Kamar kasa. "
Dariya Amna da Nafisa sukai hakan ya kular da ita, dake ita ce karama, Alhaji Nafi'u ya bata da yawa, shiyasa ta raina kowa kuma basu shiri da Ammin tasu.
"Tashi kije Ki cire Naman nan daga oven, ki saka cikin tray ki kawo dining. "
Tashi tayi Idanunta har sun kawo ruwa tace
"To Ammiey amma kina ganin dariyar da suke min ko?"
"Sunyi din, wuce kiyi abinda na saki"
Ta fada tana hararar ta, kanta ta gyada ta wuce kitchen din tana tunanin irin sharrin da zatayi musu gurin Abba. Ta nufi kitchen din se taji sallamar Maina ai da gudunta ta dawo tana ihu
"Oyoyo Yaya! Oyoyo Yaya!! "
Gabaki daya suka mike kowanne farin ciki fal fuskarshi, rungumeshi Nafisa tayi tana ta ihu, kanta ya rankwasa yana cireta daga jikinshi yace
"See this girl, Bakisan kin girma bane? "
Turo bakinta tayi tana shafa kanta, se muryar Abba sukaji yana fadin
"Maina daga zuwanka zaka fara dukar min 'Yata"
Sake shagwabe fuska tayi tana diddira kafa ta nufi gurin Abban tana fadin
"Abba, Tun dazun Yaya Amna take ta duka na."
Bude baki Amna tayi cikeda mamakin Iskancin Nafisa, Abba ya dubi Amna yana doka mata harara yace
"Ke zaki bar gidannan Yanzun nan ta mun rigada mun miki aure. No room for disturbance."
Baki Ammiey ta tabe tana fadin
"Kai ta biyeta dai Tana hada Ku fada da Yayanka."
Dauke Kai yayi yana shigowa ciki suna gaisawa da Maina Wanda ke ta dariyar dramar gidannan. Dukkansu tare suka zauna dan cin Abinci se lokacin Ammiey ta tuna da wannan Nama da tace a ciro daga oven, cikin sauri ta Mike ta nufi kitchen din, Tana budewa Har ya Fara konewa, ranta a mugun bace ta fito rikeda tray, sede kafin tayi magana wayarta ta Fara ringing. Aje musu tray din tayi ta tafi gurin wayar. Kamar bazata dauka ba ganin Maman Fainusa ce amma Se ta dauka suka gaisa Kamar yadda suka saba. Sannan Maman Fainusa tace