4⃣7⃣

2.5K 271 11
                                    


Na jima ina bacci se daf da Zuhr sannan na tashi, Dama ya lafiyar kura balle tayi zawo. Normally Ni me son bacci ce balle kuma sanadi yazo, ai se inda Mai ya Kare min. Da na tashi baya nan, ni daya ce a dakin, cikin takatsantsan na shiga toilet na Tara ruwa cikin katon bath, Allah yasa akwai heater toilet din kuma ya tafasa. Duk zafin da nake ji haka na daure nayi sitbath din sosae Dan nasan shi zaisa naji dadi. Daga nan nayi wanka nayi alwala sannan na fito. Wani sabon yanayi naji a jikina tamkar wata sabuwar halitta, naijini so empty, kamar an canja ni.

Carpet na shimfida Nayi sallah, na jima Inayi mana addua kafin na gangaro kan iyayena. Na jima zaune amma banji motsinshi ba. Mikewa nayi na bude wardrobe, actually duk Wanda ya gyara wardrobe dinnan zai iya gyara tattalin arzikin Nigeria. Komai neat and well arranged. Wani lace cream na hango da red design a jikinshi, cirowa nayi Dinkin skirt da riga ne, ina sawa suka zauna daidai. Na Dan gyara fuskata na gyara gadon, Inata tunanin inda ya tafi. Parlor na fito na samu babu kowa, Dama ba datti Yayi ba balle ace gyara akai.

Ina hango kofar kitchen naji wata azabbabiyar Yunwa, zama nayi ina tunanin ta inda zan Fara, Dan yunwar nan bazata jira nayi girki ba, emergency ce. Sallamar Maina yasa na dubi kofar da sauri, shi ne din ya shigo tareda Zama gefena, yace

"Kin tashi? Ya jikin? Akwai inda yake miki ciwo? "

Kaina a kasa na girgiza Kai ina dan Murmushi, inajin dadin concern dinshi a Kaina, ina fatan farin cikinmu Ya daure. Hannunshi yasa ya dago fuskata amma duk yadda yaso nayi magana Ko na hada ido dashi naki, gaba daya wata irin kunyarshi nakeji, ji nake inama kasa ta bude na fada. Kanshi Ya gyada duk ya damu yace

"Kiyi min magana mana, Haba Baby, daga abu daya se ki ta jin kunyata kuma? "

Juyar da kaina nayi Ina wasa da yatsuna, a raina Ina fadin Ni kawai ka bani Abinci shi ne abinda nake bukata. Kamar yaji se cewa Yayi

"You must be hungry I know, taso muje kici abinci"

Wata Ajiyar zuciya na sauke, kafin ya Mike tuni na mike, Nidai a parlon banga dining area ba Ashe hade suke a kitchen, dazun da na shiga da safe ban lura ba Sam. Dining din yana extreme na kitchen din, ya hadu iya Haduwa, kujera ya jamin na zauna sannan ya zauna shima. Tea Ya hadamin me kauri, yana aje min na Fara sha, amma ko rabi banyi ba na aje saboda abinda na gani cikin plate, Noodles ce, Irish da kwai fried. Kallo daya zakayi kaji ka koshi, saboda yadda noodles din ta sankare, Irish din yayi deep brown, Kwan kuwa rabi a kone yake. Idanuna na lumshe dan Bazan iya cewa Bazan ci ba, nasan it takes a lot of effort kafin yayi wannan girkin, kuma nasan saboda Ni ne.

"Bar tea din haka, muci abinci"

Kallonshi nayi nace

"Bakai breakfast ba Kaima? "

Kanshi Ya girgiza yace

"Inata jiranki ki tashi"

Se naji babu dadi, hakan yasa na saka masa fork a gabanshi nima nasa daya, a tare muka kai bakinmu, na farko noodles din Anyi overcooking dinta, Irish ya kone amma ko laushi baiyi ba, Kwan kuwa daci yake saboda yadda yasha wuta. Muka Kalli juna mukai Murmushi sannan muka hadiye da kyar, da yayi Loma ta biyu kwace fork dina Yayi yace

"Baby, kiyi hakuri ban iya girki ba, gashi duk na bata abincin"

Murmushi nayi nace

"Kayi kokari kuma naji dadi amma Bari a daura sabo"

Kanshi Ya girgiza yace

"A'a bazaki shiga kitchen ba, shiyasa nace su Mummy su dawo Ko Dan abinci"

Dariya nayi nace

"Sooner or later zanyi girki, so Bari na Fara yau"

Kafada ya dage yace

"Naki wayon, tashi muje mu ci a waje"

HIKMAH Where stories live. Discover now