Ban iya abu kadan ba, Ko damuwa nasa a raina bansan in cireta lokaci daya ba, bansan abinda mutane suke cewa overlooking ba. A'a yadda nake da naci da taurin Kai Haka nan zuciyata take idan ta takura min. Wannan abin da Abdallah yayi min yasa nayi kuka Har mukaje gida ban daina ba, shi kuma bawan Allah Maina duk tunaninshi saboda naga Mami ne, baisan ba haka bane. Seda muka je gida sannan nayi Shiru amma fuskata babu alamar walwala a tare da ita. Shima se ya kyaleni kawai ya cigaba da alamuranshi. Seda safe tukun na wartsake, ranar ma zai koma wannan conference din, so tunda nayi Sallar asuba na wuce kitchen na shirya masa breakfast. Na hada mishi ruwan wanka, sannan na Nemo masa kayan sawa. Ina kwance na dunkule cikin blanket ya fito daga toilet, kan stool Ya zauna tareda kallona yace
"Madam, taso ki shafa min Mai"
Fitowa Nayi a Blanket din, Nazo na dauka lotion din, munata hira Har na gama. Yace
"Awnnnnnn, Thank you Baby. Gobe zamu Je Kano, daga can mu wuce Zaria. So idan na dawo se muje shopping Ko? "
Kaina na gyada ina Murmushi nace
"Allah Ya kaimu"
Kaina ya shafa, ni kuma na fita na kawo mishi breakfast din. Tea kadai yasha yace nayi packaging Sauran, jiya ya makara, so yau baya son Yayi latti kuma. Har Mota na Kai shi ya tafi sannan na dawo, straight daki na koma bayan na kulle ko ina, nayi setting alarm na Fara bacci. Ban tashi ba se Karfe goma da rabi. Dakin na gyara, na dawo parlor na gyada, haka kitchen ma sannan na daura noodles na ci. Nayi wanka nayi sallah sannan na dawo parlor na kirashi
"Baby! Ya gidan "
Kallon gidan nayi nace
"Lafiya lau, ya conference din? "
Dan Tsaki yayi sannan yace
"Ki Bari kawai, Se ynzun zamuyi breakfast fa "
Idanuna na dan zare nace
"Kai suna wahalar min da kai fa, kenan Se yamma zaka dawo"
Yadda yayi Murmushi nasan dadi yaji nace zasu wahalar min da kai.
"To ya zanyi. Kiyi kallo kada kiyi tunani, I love you! Se na dawo"
Kaina na gyada Kamar yana kallona nace
"Take care"
Daga Haka mukai hanging, na kunna kallo, da can ni ba fan din kallo bace, shiyasa gaba daya na kasa concentrating Se wayata da nake ta dannawa, na duba Mami ko tayi min reply amma babu, duk se naji babu dadi, Dan tun ina hada masa breakfast na mata text amma babu reply. Shi Daddy dama ya kirani tun sassafe. Ina nan zaune muna chatting da Nanah da Najaatu, dukkansu tambayata suke ko Inada ciki, banda dariya babu abinda nake, nace kowacce Tazo Abuja ta duba da kanta.
Se naji knocking, mikewa nayi na leka ta door hole, anan na hango Nafisa tana waya, da murnata na bude tareda rungumeta nace
"Ashe zakizo da gaske?"
Se lokacin naga mutanen dake bayanta, tare muka shigo, daga kamannin su nasan suma cousins dinmu ne,
"Nafi wai bazaki aje wayar ba ne? "
Na fada ganin Har lokacin wayar take, kuma so nake tayi ta gama tamin introducing mutanen. Mikewa nayi na Fara entertaining dinsu, seda ta gama sannan tace
"Wannan Amaly ce, Uncle huzaifa na Edo state shi ne Babanta, wannan Munnira yar Anty Amina ce"
Kaina na gyada nace
"Sannunku da zuwa"
Ina tunanin familynmu babu Shiru Shiru sede idan Baa saba ba, kafin wani lokaci mun dinke Se hira muke. Suka tayani na hada dinner sannan suka tafi. Ina idar da Maghrib nayi wanka nayi kwaliyya sosae, na dinga tunanin abinda zan saka ma, nasa Atamfa, nasa lace, Haka shadda, material komai. Kawai na dakko wani Jeans na saka, ya kamani sosae tamkar shi ne skin dina na biyu, wata off shoulder top white silk ce sosae. Ko hula ban saka ba, na dakko Sarka nasa sannan na koma parlour. Ina zama ya turo kofar, Juyawa nayi cikin daukar hankali ina kallonshi, he looked so tired and exhausted. Babu necktie ya cire, suit din a kafadarshi, waya a hannu, briefcase dayan hannun. Inata kallonshi a raina Ina ayyana Meye Laifin wannan Mutumin dake gabana, ko sau daya bai taba nuna min komai ba banda zallar kulawa da soyayya. He loved me and he still loves me. Bai taba ganina ba, baisan yadda looks dina yake ba amma duk da Haka, he waited for me. Bai taba kallona yace min ya kafata take ba. Tunda na aureshi ban kara kunci ba, banni da farin ciki da kullum yake sani ba. To me yasa Dan naga Abdallah naji ina kuka, ina nufin Allah zanyiwa butulci akan duk daukaka ni da yayi, duk yadda ya juya alamurana.