1⃣3⃣

1.9K 269 6
                                    

*Hello readers! How are you doing, I'm so sorry for the sluggish post, kunsan jiki da jini se a Sannu. I noticed something that I wanted to clear some people's doubt a little. About Assisted conception babu inda na rubuta Artificial insemination Haramun ne, babu idan kuma akwai pls notify me ASAP! Kafin na rubuta HIKMAH I made sure nayi bincike kafin na rubuta, Abu daya nake son mu fahimta a rayuwar Hafsa da Aminu, hakuri, neman yardar Allah da kuma shawara. Babu abu daya dasu Hafsa sukai. In life, we need to understand not all desires are best for us, Kamar haihuwar Lulu a ynzun babu alkhairi sede may be Ko nan gaba...... Ina fatan kun fahimceni*

Mom dai dakko wayarta tayi ta Fara neman layin Alhajin sama, dukda cewar ba Wai tana jin dukkan abinda suke cewa ba, amma tana Dan tsintar Wasu abubuwan. Suna gama wayar ta Kira sunan Aminu Wanda Ya shagala sosae wajen kwantar da kai yana lallamin Hafsa tareda kara kasheta da harshen shi. Seda Mom ta kira shi sau biyu sannan a dan rikice yace

"Mo....Mom"

Dan Murmushi kawai Tayi sannan tace

"Alhaji yace ka wuce station don su sun rigada sun je"

"To Mom"

Ya fada Yana kallon Hafsa wadda tayi laushi matuka dan Aminu Ya riga ya gama da ita, kalamanshi sinking kawai suke cikin zuciyarta suna Kara bin circulation pump.

A Bompai anan aka kulle Cynthia da mukarrabanta, suna isa Mom ta kira Alhaji ta sanar dashi isowarshi, Ko mintina hudu basu cika ba sega shi ya fito, bayanshi Wasu guards ne rike da bindigogi duk wani motsinshi akan idanunsu, Da gudu Hafsa ta isa gareshi ta rungumeshi tana jin wani sanyi na ratsata, shima rungumeta Yayi yana patting bayanta yana fadin

"Is ok Hafsa na, everything will be ok "

Kanta ta cigaba da gyadawa yayinda hawaye suka cigaba da sakko mata babu kakkautawa, hannunta ya kama suna gaisawa da Mom sannan yana fadawa Aminu

"Ku shigo ciki Dan already commissioner of police ya iso"

Gaba daya ciki suka dunguma, mutane nata gaishe da Alhaji kasancewarsa a Yanzun shi ne Deputy governor Borno state, a wani katon hall suke zazzaune, yana shigowa kowa ya mike har seda ya zauna sannan suka zazzauna suma, Hafsa se rarraba idanu take don ganin Cynthia amma ina babu ita babu dalilin ta, a gurin Alhaji Bukar Mahaifin Aminu, Dada, Nafi'u, Salima, Habibu, se CP da police officers guda uku.

Ko gaisawa basu samu Anyi ba, CP da kanshi ya ciro file din case din da akai compiling aka turo daga Abuja, kallon Hafsa yayi wadda itama shi take kallo, baice mata komai ba se umarni da ya bayar akan a shigo da Rebecca.

"Rebecca? "

Hafsa ta furta a hankali cikin tantamar abinda ke faruwa, jin footsteps yasa Hafsa Juyawa nan da nan ta Mike a hanzarce ganin Cynthia Anyi handcuffing dinta, dukda alamu sun nuna cewar tabbas rayuwa ta canza mata amma ko tsufa Cynthia tayi Hafsa zata ganeta, ta rame tayi baki, fuskarta a daddauje da alamun duka taci a hannun police officers din Don kowa yasan yadda Nigerian police suke idan ka shiga hannu tamkar zaki yaga Nama Haka suke.

Tunda suka hada ido da Hafsa Cynthia ta Fara kuka Tana hade hannayenta guda biyu Kamar me rokon gafara, rokon gafarar take don Tun ranar da ta gudu da Lulu hankalinta kullum a tashe yake, kullum da Hafsa take kwana da ita take tashi a zuciyarta tasan bata kyauta ba, tasan batai yiwa wannan couples din adalci ba, matsayin Wanda suka dinga neman haihuwa idanu rufe suka samu kuma ta rabasu da sanyin idaniyarta.

"Cynthia shi ne sunan da nayi amfani dashi lokacinda muka hadu dake Anty, asalin sunana shi ne Rebecca, ban taba zuwa Abuja ba Kamar yadda nayi miki karyar ni din yar Abujan ce, bani da hadi, asalina ma ni Inyamura  ce a jihar Edo. Tunda aka haifeni na tashi na tsinci Kaina as a cultist, a Haka na tashi kuma na girma akai. Fuskata tana masifar taimakona saboda Inada fuskar da kana kalla zaka fada trap dina, mutane da dama suna nuna min tausayi amma ni ba abar tausayi bace. "

Shiru tayi tareda share hawayen dake fuskarta da bayan hannunta, Babu Wanda ta taba bawa labarinta idan ba yau ba shima tasan babu kufcewa bata isa tayi meddling da mutanen ba, she never taught they're that powerful ba se Yanzun.

"Matar da ta kawo ni gurinki aiki nake mata, duk yadda nake tunanin a tsaye nake to tafi ni, hakan yasa ban taba samun space da zanyi wani abu ba, dalilin da na Fara neman hanyar guduwa Dan lokacin sacrifice Ya kusa kumatu ina bukatar yaron da zan Kai. Se kawai naji tana neman yarinyar da zata zame miki Nanny, naji tana bawa kanwar mijinta labarin baku taba haihuwa ba se wannan Shekarar, anan na tuna offering din da zan bayar has to be a precious child, Wanda iyayensa suke matukar so, wannan yasa nace tunda ni tasan halina why not ta barni Nazo gurinki, bata wani ja ba as if tasan manufata ta baki ni, a cewar ta dama anyiwa mata transfer aiki zuwa Ibadan kuma bata son takura ni. "

"Farkon abinda na Fara lura a rayuwarku shi ne matsanancin son da kuke yiwa Lulu, kuna sonta kuma kuna son junanku, sede inda na Fara samun gap shi ne a gurin Anty she's some how careless dukda yadda nake nuna mata ni abar tausayi ce amma a zahiri na fita gatan dukiya, mijinta Wato Abban Lulu kullum na kalleshi Se naga rashin yarda Dani a idanunshi, he always give me a suspicious look."

"Na hada dukkan yadda zan fita da Lulu amma na kasa samun wannan damar, kwatsam naji suna rigima akan birthday Lulu, I was super excited Haka na harhada plan dina nayi parking komai against wannan ranar. Ranar tana zuwa Tun safe da kika aikeni karbo cake na fita da kayyayaki na amma saboda hidimar da kike ciki baki Ankara ba. Inata fakon ki har aka gama party babu wani space na hakan seda cikin sauki kika bani ita nayi mata wanka anan ko dakin ban koma ba na fice da ita. "

Babu abinda ke tashi gurin banda kukan Hafsa wadda ta daura kanta akan kafadar Dada Se kuma Uhmmmm, lallai da zantukan na zaune.

"Muna fita dake komai cikin shiri yake ana jirana a Suleja, Mota na samu na hau cikin saa Lulu tayi bacci nako goyata a bayana har muka isa. Ina sauka Yan kungiyarmu nata murna an samu yarinyar offering. A ka'ida kafin akaiwa dodon Tsafi sacrifice Se an Kai offering asibiti an duba lafiyar sa. Washegari muka isa Jos cikin plateau state inda anan muke komai kuma nasan nayi nisan da Bazaa kama ni ba. Seda muka kwana biu dake Lulu ta saba dani kukan da take kadan ne. Ranar da muka kwana biu muka shirya mukaje asibiti inda akai running test da exrays komai normal sede kafarta ta hagu is deformed babu yadda zaayi offering da ita. Hankalinnu dukka ya tashi tunda ga samu ga rashi, munata controversy akan yadda Zamui tackling abin. "

"Muna nan muna tunanin yadda zaayi, a Haka Har dare yayi muka kwanta, abinda Bazan taba Mantawa ba muka tashi da safe da tunanin yadda zamu tackling Maganar da yadda zamu samu replacement din Lulu."

Se ta Kara saka hannayenta Tana wani irin kuka me tsuma zuciya, officer ne ya daka mata tsawa yace

"Useless fellow, bazaki cigaba ba"

A firgice Rebecca ta cigaba da fadin

"We walk up and couldn't find Lulu, she got missing"

"Miss what? "

Aminu Ya fada a firgice yana mikewa tsaye, wani wawan Mari dayan police din Ya bata hakan yasa tace

"Wallahi I said nothing but the truth, iya gaskiya na fada muku. "

Shiru gaba daya gurin aka dauka Har lokacin babu Wanda ya iya furta komai saboda su kansu sun San gaskiya ta fada kuma da gaske alama ce ta Allah Ya kubtar da ita daga mugun hannu.

Jakadiyar kainuwa

HIKMAH Where stories live. Discover now