3⃣7⃣

2.2K 246 19
                                    

Bani na isa Zaria ba se gab da Maghrib, lokacinda na shiga dakina Kaina Kamar zai tsinke saboda azabar ciwo, ga wani palpitation daya sakani gaba, idanuna har dusudusu nake ganin wannan yasa nasan tabbas Bpna Ya hau. Bana sallah hakan yasa na kira Mama wadda tana zaune jugum ta rasa abinda ke Mata dadi gani take baayi min adalci ba, ta Yaya Baffa zai iya yin hakan, gani take an zalunce ni ne kawai. Tana cikin wannan yanayin Sega wayata tana shigowa, kasa dauka tayi dan gani take da zarar ta dauka zan fahimci halinda take ciki. Sau biyu ina kira bata dauka ba, hakan yasa na hakura na gwada number Abdallah, inajin ta shiga naji tamkar an tsoma ni cikin ruwa saboda yadda naji dadi a raina, amma har ta gama ringing Baa dauka ba. Kashe wayar nayi baki daya na kwanta tareda runtse idanuna, duk wani tunani daya taho min Se na kawar dashi saboda Ina bukatar adequate rest Ko na samu Bpn ya sauka. Cikin raina Inata maimaita Hasbunallhu wa niimal wakil! Cikin kamkanin lokaci naji komai ya Fara lafawa ban jima Ba bacci ya daukeni. Tunda na kwanta nake wani irin mafarki me tayar da hankali, a firgice na tashi Ina maimaita adduar Wanda Yayi mummunan mafarki Ko ya kasa bacci

_Audhu bikalmatillahi tammati, min gadabihi, wa iqamihi, Wamin sharri ibadihi, Wamin hamazati shayadin, wa an yahduru!_

Tashi nayi na kuuna standing fan sannan na tafi bayi nayo alwala, time na duba naga daf ake da Fara kiran Sallar asuba, hakan yasa na Fasa komawa kawai na hau sallaya Ina kaiwa Allah kukana. Seda nayi asuba sannan na duba timetable naga Se 9am nikeda class hakan yasa na koma na kwanta, bacci sosae nayi se takwas da yan mintuna sannan na tashi. Wanka nayi Nazo nadaura Abinci, kafin na gama na shirya na duba Bpna Naga ya sauka sannan naci Abinci.

Karfe Tara saura Minti biyar muna zaune nida Nanah, gaba dayanmu babu me magana Se Amjad ke ta janmu da hira ganin da gaske Shiru shirun muke ji yasa kawai ya rabu damu, amma ni bansan ya Nanah takeji ba, Nikam komai baya birgeni, lecture ma Dan dole na zota dan nasan Urinary physiology ba saan wasa na bane, if not da Bazan shigo ba.

Muna nan zaune se bayan awa daya sannan class rep yayi making announcement cewar bazai samu damar zuwa ba, Ko Damuwa banyi ba, inajin yadda mutane ke zaginshi amma hankalina yayi gaba, so nake kawai naga Abdallah naji dalilin da yasa ya shareni for good 3 days. Ko su Nanah Ban jira ba na tafi office dinshi. Ko knocking banyi ba, Ina zuwa na tura kofar da karfina na shiga ciki, yana tsaye Ya zura hannayensa cikin jeans pocket dinshi, Wanda color ya zama pale brown, top din jikinshi milk ce me taushi, babu rubutun komai a jiki se tambarin designer din, fuskarshi tayi fayau, idanunshi sun fada ciki kamar Wanda Yayi jinya. Kallona yake kamar yadda na zuba mishi ido, dauke kanshi Yayi tareda fadin

"Zan sameka a office, se mu karasa maganar"

Se a lokacin na fahimci Ashe bashi daya bane, Juyawa nayi naga wani mutum Wanda sun kusa sa'oi da Abdallah Ahmad ban taba ganinshi ba. Murmushi yayi min sannan ya fice bayan Ya ja mana kofar. Zagayowa Abdallah yayi gabana ya tsaya kamar 3 feet away,

"Hikmah please sit"

Ya fada a hankali Kamar me rada, dagowa nayi dukda kwarjinin da yayi min amma seda na zabga mishi harara nace

"Kanada wannan bakin Dama? Abdallah me Kake nufi? is that treatment a bye bye? "

Kanshi Ya dafe yana girgizawa yace

"I've messed up Hikmah, kina tunanin cikin hayyacina zan iya cewa na fasa? duk ranar da aka ce miki Abdallah ya fasa aurenki, to kisa a ranki I'm insane, I'm possessed wallahi. Bazan taba yin hakan ba, Bazan taba cutar ki ba. Yanzun ki zauna muyi magana"

Yayi nasara Dan kalamansa Sunyi tasiri sosae cikin zuciyata, a hankali jikina a sanyaye na zauna inajin haushin Kaina da nayi tunanin cewar Abdallah zai iya rabuwa Dani, zai iya yaudarata. Se naji babu dadi.

"Zainab its very hard Kinji, amma I got you farin Cikina. Ban taba fada miki ba saboda da farko ban taba kawowa cewar hakan zata iya faruwa ba. Kinsan VC shi ne Mahaifina, Mrs Hassanah Uba ita ce Ummiey ta. Sun rabu Tun kafin na gama secondary school, I taught may be zasu maida aurensu but basu mayar ba, kowannensu yaje Yayi aurenshi abinshi. I came from a broken family, shiyasa Bana son aure , a da ina ganin duk aure haka yake ayi a rabu, later na gane namu ne Haka, saboda kaddarar mu kenan. Papa yayi auri wata lecturer Hajiya Talatu, matar nan is cruel ban taba ganin azzaluma irin ta ba, seda ta maida Papa se abinda tace shi yakeyi. Tazo da yarinyar ta Mupheeyda wadda take completely opposite of her sede Kinsan Hausawa sunce barewa bata gudu danta yayi rarrafe, she's more poisonous than uwarta, shiyasa muka daina shiri, her only weakness is I, tana sona Hikma, so Wanda banda mugun halayenta da nayi dace. Anyi zancen Zamui aure na ki amincewa kuma daidai lokacin kika shigo rayuwata shiyasa na tabbatar kafin na shawo Kanki naje gidanku, naje komai ya tafi daidai, sede ranar da mukai waya last ina fitowa Papa ya kirani na sameshi parlonshi, tunda na Tarar da Anty Talatu zaune nasan akwai matsala, kafin naje ta gama mishi famfo akan sede na aureku ku biyu...... "

HIKMAH Where stories live. Discover now