3⃣3⃣

2.3K 296 35
                                    

*_To that amazing soul F. U Lema..... Thank you for the love. Shatuuu has received your message. Thank you one love_*

Kwanaki a hankali suka cigaba da tafiya babu wani abu daya canza daga yanayin yadda nake rayuwa, kullum idan na tashi banda kuka babu abinda nakeyi Matsawar zan kebe ni daya, na kasa yin hakuri dukda yadda kullum Hamma Aiman ke bani baki, Rana bata taba zuwa ta fadi bai kirani ba, shiyasa yake da matsayi me girma cikin zuciyata, inajin tamkar banida wani Dan Uwa Se shi. Shikam Uban gayyar Hamma Mussadiq tamkar surikai Haka muke dashi, kunyata yakeji sosae, ko idan yazo Ya sameni a parlor, Se yayi ta sunkuyar da kanshi bazai ma sake ba balle ya dade, har ranar seda Mama ta Tambayeshi me ya hada mu amma cewa Yayi babu komai, amma idan yazo bana parlor zai dade amma da zarar Na fito zai Mike Ya tafi. Har ga Allah bana jin zafinshi, ni godiya nake mishi cikin zuciyata at least ya sanar dani matsayina, Wanda nasan yayi dana sanin hakan.

Mama ta maida ni asibiti sau uku follow up amma amsar kullum daya ce jinina baya sauka, ranar Haka ta sani a gaba ta dinga kuka akan na fada mata Meye matsalata? Nima se kuka na rasa yadda zan saka raina Inji sanyi. Nidai alkawari na dauka Bazan taba fadawa kowa a gidannan halin da nake ciki ba. Amma Bazan iya jurar kallon hawayen Mama ba.

"Mama Dan Allah kiyi hakuri, bansan yadda zan miki bayani ba. kiyi hakuri tunanin Abdallah nakeyi"

Dif kukanta ya dauke tana kallona cikeda mamaki da damuwa, idanuna na kawar Kamar gaske, to ya zanyi dole nayi mata karya,

"Hikmah dama Baki manta yaronnan ba? Daman har Yanzun kina tunaninshi. Ina ce mun wuce gurin Hikmah, Baki yadda da kaddara ba? Baki yadda komai na rayuwa MUKKADARI NE daga Allah ba? Haba Hikmah ina tauhidinki Ya tafi"

Hawayena na share na matso na rungumeta a jikina, Mamata da babu kamarta. Idan Har wannan da ba ita ta haifeni ba tana min wannan son to inaga Uwar data haifeni? Wanne irin so zata min nima Wanne zan mata? na ayyana a raina. Shikenan na kashe Maganar, daga wannan lokacin na kara kaimin addua sosae sannan na Fara dangana da hakuri wannan yasa hankalin kowa ya kwanta.

Bari na barku haka bari na koma zuwa rayuwata, mabudin dukkan Wasu Alkhairi. Da farko Kamar yadda kowa ya sani haduwata da Abdallah Ahmad Abdallah ba haduwar Arziki bace, Babu Maganar da na tsana a duniyata irin zancenshi saboda a ganina babu Wanda ya taba wulakanta ni irinshi. Amma wani abu da Allah shi shi ne yasan daidai, shi yasan what tomorrow will be. Duk yadda mutum ya kai zurfafa kiyayya akan abu to Allah yana iya canja lamarin labari yasha banbam, hakan ce ta Faru tsakanina dashi.

Mun koma school bayan dogon hutun session da muka sha, kowa a wannan hutun zakaga yadda yake kyau, fresh da kiba amma bandani, kallo daya zamanin kaga tamkar nayi wata doguwar jinya ne, ni a ganina gwara doguwar jinyar akan ciwon da zuciyata take min, akan halinda na samu Kaina a ciki, ni Kaina na gaji da halinda nake ciki, na gaji da jina babu walwala, na gaji da rufe bakina bana magana, duk yadda nake son ganin hakan ya faru amma kwatakwata zuciyata da kwakwalwar Kaina are not complying.

Dayake level 3 zamu shiga kuma normally level 3 students basuda accommodation a campus din ABU , so Tun a gida aka sama min accommodation a Empire Apartment dake nan wajen school amma Zaa iya trekking zuwa school. Daki daya ne da toilet se kitchenette attached.

Nafi awanni biyu ina gyara sannan na Gama, Nanah na Fara kira tace min bata dawo ba se next week, mun Dan taba hira sannan mukai sallama. Su Mama na kira sannan na sanar musu isowata, sosae Mama ta dinga Nanata min Zancenta na kullum nasiha da karbar rayuwa a yadda ta zowa mutum. Da wannan mukai sallama na koma na kwanta hade da lumshe idanuna. Na tabbatar da ace lokacin ina Hikmah ne to babu yadda zaayi Naso dakinnan ni daya , Dan bana son kadaici ko Yaya yake, amma Yanzun har wani dadi nake ji ganina ni daya.

Seda nayi Sallar ishai sannan na fita inda Wasu eateries suke don naci Abinci. Ina zuwa nayi placing order sannan na tafi can VIP section karshen gurin na samu seat na zauna, sweet din dake aje kan table din na dauka na bare sannan na jefa bakina ina bin mutanen dake zazzaune yawanci ka kallesu suna cikeda walwala da farin ciki dukda Yan tsirari ne, a raina na ayyana dukkansu sunsan iyayensu, a gidajensu suke amma ni gani bansan su waye iyayena ba, bansan me yasa na Baro hannunsu bansan yadda rayuwar su take ba ko sunada rai, ko sun mutu? Ko me yasa na rabu dasu. Itace tambayar da kullum nake yiwa Kaina Kamar sau biyar ko fin Haka a duk ranar duniya. Tsorona daya ace saboda an haifeni illegally shiyasa aka jefar Dani, tunanin wannan yasa na kifa Kaina akan table din na some Sana'a ta, Nama manta a inda nake da abinda ya kawo ni amma inajin zuciyata na wani irin zugi, kaina ya Fara Sara min. Na kusan mintina goma a Haka, su basu kawo order ba ni ban tafi ba, ban kuma daina kuka ba seda naji an ja kujerar dake gefena an zauna sannan nayi saurin dagowa ba tareda na iya goge fuskata ba.

HIKMAH Where stories live. Discover now