4⃣4⃣

2.4K 279 21
                                    

Babu Wanda yasan da zuwanmu banda Daddy shi kuma ya riga da ya koma Abuja saboda aiki, amma Mami babu Wanda ta fadawa zamu zo, shiyasa babu Wanda yazo daukarmu daga airport se cab ta samar mana drop muka tafi. Muna tafe Tana yimin bayanin guri guri, immediately I fell in love with Maiduguri over and over, saboda dama tuntuni ni inason garin. Se Misalin goma da wani abun muka isa gidan, Tun daga kofar gidan nasan Babban gida ne na masu hannu da shuni, ginin kadai ya isa fada maka masu mallakin gidan ba abun wasa bane, Alhajin sama Yayi deputy governor, Abba Yanzun shi ne chief of staff na Borno, Alhaji Bulama da bangani ba Mami tace min shi kuma Babban Dan kasuwa ne a garin. To iyaye kenan baazo kan 'ya'yansu ba balle kuma su jikoki irinsu Yaya Ibrahim, ai sede a rufe baki da Sam barka.

Gidan Ya danyi Shiru, saboda mafi yawancin mutanen gidan sun kwanta, muna shiga wata matashiyar budurwa ta fito daga can part din gefe, kunnenta da ear piece a makale, Tana hangomu ta zare tareda ihun

"Ma! Oyoyo"

Kai Mami ta girgiza tace

"To town Crier, Announcer, dare ne yanzun"

Dariya ta saki amma ganina takure jikin Uwata yasa ta Kalli Mami sannan ta kalleni tace

"Ma, Lulun ce? "

Kafin Mami ta bata amsa tamin wata irin runguma da banda Ni Babba ce da se na samu fracture. Rungumeta nayi nima inajin dadi, sakina tayi ta Mika min hannu tace

"Nima cousin dinki ce, sunana Labiba amma zaki iya cemin Milk!"

Idanuna na dan bude da mamakin sunan, se kuma nayi Murmushi nace

"Hikmah!"

Shaking hands muka kara Har lokacin Mami na tsaye, seda muka gama tace

"Muje parlour nasan kin gaji"

Dukkanmu muka shiga wani tangamemen parlour, yayi kyau Kamar kada na fita a ciki, babu kowa se wata budurwa itama da batafi saa ta ba tana ta jerking, kafafunta cikin ruwa, hakan ya bani dariya, Dan idan Tun Yanzun sha daya batai ba Anyi tsome tabbas zuwa sha biyu tayi bacci kenan. Mami ce tace

"Nikam Nasiba bana hanaki tsoma kafa cikin ruwa ba, idan bacci kikeji ki tafi ki kwanta ki saita alarm. Amma you can't cheat nature"

Tayi abinda aka ce mata, amma wani ihu da ta buga Tazo ta rungumeni Ni kaina seda na firgita, there and then na fahimci inda na gado hayaniya, ashe a maiduguri na dakko. Kafin wani lokaci mutane sun firfito Dan ganin lafiya, da yake ba bacci sukai ba sun kwanta ne kawai. Da fuskokin dana hadu dasu jiya da Wanda basu nan Haka na dinga binsu da kallo, hug kuwa seda na gaji. Ga gajiyar hanya banda burin da ya wuce naji na kwanta amma ina haka muka zauna anata hira, Yan mata wajen shida, duk jikoki sun nanike ni. Har wajen sha daya sannan Dada tace aje a kwanta ko Dan na huta. Se naji duk na wartsake koda zaa kwana a Haka Bazan gajiya ba.

"Ma, zamu tafi da ita dakinmu mu kwana"

Nabila ta fada tana kallona, Kai Mami ta girgiza tace

"Yanzun an samu canji daga Ma, na koma Mami. So kowa Yayi cancelling Ma a ranshi. "

Murmushi nayi Dan nasan saboda na Fara kiranta da Mami shi yasa. Binta nayi na canja kayana zuwa kayan bacci sannan na kwanta gefenta Kamar jiya. A Haka bacci me dadin gaske yayi gaba Dani. Duk da naso Naga Mijina kafin na kwanta amma ganin babu Wanda Yayi zancenshi yasa nima na share kawai.

Washegari, bayan Munyi Sallar asuba Mami ta daukeni dakunan kakkanni na naje muka gaisa, a karshe dakin Ummiey ta barni ta koma nata. Munata hira da ita dukda tayi tayi na kwanta amma naki. Can Sega Yan matan gidan sunzo muka hadu dasu munata hira, ka rantse da Allah mun dade da sanin juna. Hirar Har ta gangaro kan Maina, babu Wadda ta kusheshi banda shawarwari da suke bani akanshi tareda gwada min son da yake min, se naji na kagu mu hadu na ganshi.

HIKMAH Where stories live. Discover now