1⃣1⃣

2.5K 267 3
                                    

*_Kwana biu na buya babu post.... I'm sorry things came up beyond my control... Thanks for the care and my heart goes out to every lover of 💕HIKMAH 💕_*

*NEBRASKA*

A hankali matar dake tsaye gefen bed side drawer dake cikin katon spacious bedroom dinta, Tana Sanye da Jeans trouser se katuwar rigar sanyi wadda tsayinta Ya kai kusan gwiwarta Ko ma Ya zarta kadan, kanta hula ce ta saka wadda ta bawa gashinta damar fitowa, kafafunta ruf suke da indoor socks, hannunta rikeda wani karamin frame Wanda ta tsura mishi idanu dukda bata juyo ba amma kallon is so intense, kuma duk abinda akewa wannan kallon to tabbas abun me soyuwa ne cikin zuciyar me kallon, a hankali ta jiyo jin an bude kofar bedroom din an shigo, Hafsa ce, ta kara girma bawai kiba, A'a shekaru sun ja, tayi kyau me sanyi sede kana kallonta Kasan lallai dukda shekarun da aka dauka na batan Lulu bai Bar zuciyarta ba, bata taba tashi ta koma ga Allah ba tareda kukan rashin yarta ba, kullum abin tamkar Sabo Haka yake kara zuwar mata, batasan Har yaushe ne zata daina jin kewar rashin Lulu ba.

Idanunta na digar da hawaye Wanda Ya zame mata jiki, Wanda kullum ne se ta zubar dashi sede idan ranta ya dauke, amma wannan "K" yake constant kenan. Miss A'isha ta shigo wadda girma Ya sameta, ya kara kamata kasancewar shekaru da suke kara karuwa yau da kullum. Gaba daya ta kankance fuskarta da skin dinta duk wrinkles saboda yadda menopause yayi aikinshi. Cikin damuwa ganin yadda yarta ke cikin halin damuwa shekara da shekaru, da ace akwai abinda zata mata ta dauke mata damuwar da tayi amma Allah kadai Keda wannan Ikon. Hannunta tasa ta dafa ta tana kallonta cikeda damuwa da kuma tausayi tace

"Hafsa yaushe ne zaki yi hakuri ki manta komai? Forget your past and move on Hafsa, wannan kukan babu abinda Zaiyi miki banda Karin damuwa da tashin hankali. Haka kike son muyi ta zama kenan?"

Sosae Hafsa ta kara sautin kukanta Dan babu abinda ta tsana a duniya irin Mom tace ta manta past dinta, manta past dinta na nufin manta Lulu Wanda babu Uwar da zata manta danta koda mutuwa Yayi balle nata da jikinta yake bata tana da rai kawai nufar Haduwa ce Allah baiyi ba.

Mom ce ta zaunar da ita, sannan ta zauna tareda fadin

"Hafsa bansan yadda ake jin rashin da ba amma nasan pains din rashin grand daughter, babu yadda zaayi Ki manta da Zainab Nima I don't hope so, idan nace bury your past Ina nufin kiyi hakuri ki daina kuka, ki dauka kaddarar Ku ce a Haka daga ke har Aminu da Zainab din, dole Ki tuna Zainab amma not this way Hafsa, it's been long shekaru goma sha biyu ba wasa bane. Ki karba kaddara da hakan Allah zai miki sakayyya mafificiya"

A hankali Hafsa ta goge hawayen fuskata tace

"Mom hankalina kwatakwata yaki kwanciya, nasan shekaru goma sha biyu ba wasa bane, amma kullum ina tunanin ko a Wanne Hali take ciki? Ko wacce irin rayuwa take? "

Hannunta tasa ta rufe fuskarta tana kara sakin wani matsanancin kukan, shafa bayanta Mom ta dinga yi tana fadin

"Allahu A'alam.... Allah kadai yasan a Ina take, wacce rayuwa take. Hafsa trust in Allah and in his doings bazamu sha wahala ba. "

Kanta ta gyada Tana goge fuskarta, seda ta nutsu kafin Mom tace

"AMB. Bashir yana downstairs yana jiranki"

Da sauri Hafsa ta kalla Mom wadda har ta isa kofa, tace

"Mom amma nace miki I don't want to meet him ever again Ko? "

Juyowa Mom tayi ta kalleta for some seconds kafin tace

"Then ki yadda ki koma gidan Aminu "

Mikewa Hafsa tayi Idanunta har sun cicikko jin sunan abinda tafi kauna duk duniya, kallon Mom tayi tace

"I'm not, har Se ranar da na riko hannun Lulu zan koma gidanshi, Kice Bashir Ya tafi kawai"

Dariya Mom tayi tace

HIKMAH Where stories live. Discover now