9⃣

2.8K 241 5
                                    

Mama na shigowa na kara bude baki Ina kuka, zama tayi gefena tace

"Hikma"

Dagowa nayi na dube ta sannan na share hawayena ina Kara kwabe bakina Dan ni auta ce kuma yar shagwaba ce, jikin Mama na kwanto ita kuma tana shafa bayana sannan tace

"Banason ki Kara shiga sabgar Mus'ab kina jina? "

Kaina na gyada sannan ta Kalli Hamma Mussadiq tace

"Je ka Nemo min Mus'ab yanzunnan"

Tare suka mike suka fita na zauna na share hawayena na Fara cin Abinci abuna, Ina gamawa na shiga nayi wanka.  Inada wani abu matsawar zaayi min Abu nayi kuka a kuma rarrashe ni to ya wuce a gurina, har abada kuwa, bana riko I've a free mind, shiyasa Zaiyi wahala kiga abu yana damuna.

Seda akai Sallar azahar sannan na fito parlor babu kowa se Anty Fadila da lion, naji kashedin Mama hakan yasa Ko inda suke ban kalla ba na nufi dining na dakko ruwa sannan na dawo na zauna gefe guda batareda nayi wani kwakkwaran motsi ba, channel din da suke kalla banaso amma Haka na share saboda gudun laifi. Can Anty Fadila ta dubeni

"Hikma jeki ki zubowa Mus'ab Abinci mana"

"Tohm anty"

Na fada Ina satar kallonshi, wata muguwar harara ya zabga min, fuskarshi a murtuke yace

"Idan kika kara a step se naci ubanki, Shegiya gurguwa"

I hate it when I'm referred to gurguwa, Raina baci yake Har bansan na Harare shi ba, me neman kuka aka jefa da kashin awaki, aikuwa Ya Mike a fusace yayo Kaina, dama a tsaye nake hakan yasa naja da baya don neman tsira amma ko guri ban samu ba ya iso tareda sa kafarshi Ya take min kafata ta hagu, Anty Fadila da sauri ta Mike tareda isowa inda Muke tsaye idanuna har sun cicikko da kwalla saboda nasan tsabar mugunta ce kawai.

"Mus'ab Meye Haka wai? Dan Allah ka saketa"

Wani mugun kallo Yayi min sannan ya dawo da dubanshi gurin Anty Fadila wadda ta bata rai yace

"Na tsani yarinyar nan, dangin mayu, wallahi I'm sure duk daga inda yarinyar nan ta fito mayu ne IYAYENTA"

Ya fada yana emphasizing akan iyayenta, tuni na kura mishi idanuna lokaci daya naji wani irin abu yana mamaye min jikina duk kuwa da karancin shekaruna Wanda basufi 13 years ba.

"Mus'ab at least yar uwarka ce, me yasa Kake irin Haka? "

Anty Fadila ta fada muryarta na nuna bacin rai, Kallona tayi fuskarta babu walwala ni kuwan tuni idanuna sun Fara zubar da hawaye, wata dariya Mus'ab ya saki irin ta rainin Wayo yace

"Kin jiki da wata magana Fadila, waye yar Uwata? Wannan dangin mayun? Wannan yar tsintu..... "

"Stop it Mus'ab, Kai me yasa Kake Haka ne? "

Anty Fadila ta katseshi cikin hanzari kar ya karasa amma ina abin ya dakeni, Ya girgiza ni tareda sake saka zuciyata cikin wasiwasi.

"Kinsan Dalili? Saboda I hate her! Ta karbe min dukkan Wasu Abu da nake kalla matsayin farin ciki, Dan Haka nayi alkawarin da hannuna zanyi destroying dinta Nima.... "

Tari mukaji hakan yasa mukai saurin kallan daga inda sautin yake, Baffa ne bayanshi Hamma Mustapha da dukkan alamu daga airport suke, ni tsabar abubuwan da Mus'ab ya saka ni bai Bari na tuna Yau ce ranar da Baffa zai dawo daga Calaba ba, inda yaje wani seminar. Dukkansu daga Hamma Mus'ab Har Anty Fadila Sunyi kuri da idanu, ni kuwa da sauri na shiga goge hawayen fuskata Don banga dalilin kukan ba, idan Har zan cigaba da kuka saboda Mus'ab ina ganin Har duniya ta nade Bazan daina ba, Ko a karamin tunanina ban kawo da gaske ya tsaneni Kamar yadda yasha fada amma Yau na yarda saboda kallon da yakemin irin kaga kashi dinnan.

HIKMAH Where stories live. Discover now