1⃣9⃣

2.2K 233 4
                                    


Cikin lokaci da bai cika watanni uku ba mukai wata irin shakuwa tsakanina da Abdallah, kullum se mun hadu dashi dukda sun tashi a anguwar mu amma Haka yake sammako yazo se ya wuce school kuma, da safe da yake wani junction nake zuwa nabi school bus zuwa school, to kusan Ina fitowa yana jirana muyi trekking tare, kullum tafiyar cikin farin ciki da annashuwa muke muna planning yadda rayuwar mu zata kasance, yadda muke tare dashi babu abinda na ke hangowa Kamar Munyi aure ni dashi. Shima kuma hakan take Dan bai taba missing fada min yadda yake sona ba, Tun Ina nokewa Ina jin kuka Har na ware na Fara maida martani, some times ma na fishi zakewa. Haka idan na dawo to tare zamu tako Har gida, sannan idan weekends ne to Har makaranta zai raka ni sannan mu dawo tare. Abin mamakin koda wasa ban taba Haduwa da wani ba, babu Wanda Ya taba ganinmu.

A kwana a tashi babu wuya wajen ubangiji, na shiga SS2, ranar wata Thursday ina kitchen da yake Baffa da Mama dukkansu suna routine Monday and Thursday fasting , ina kitchen ina hada musu abin shan ruwa. Doll man nake son yi musu saboda Mama tayi min complain Tana constipation( kasa yin bayan gida). Shikafa na Fara parboiling, na aje ta a gefe, fridge na dakko Minced meat na hada da parboiled rice din, nayi seasoning sosae sannan na rufe. Wani fresh cabbage na dakko, cikin nutsuwa na dinga bare shi ina sawa cikin tukunya wadda already na zuba mata ruwa, seda na bare Wanda zai isheni sannan na rufe na daura a gas. Irish na Fere a guda guda nayi parboiling, na samu fresh tomatoes da garlic nayi blending shima na daura a wuta nasa Mai ya zama Kamar sauce, da yayi yadda nake so se na dakko Irish dina na jefa a ciki. Wannan cabbage din already yayi laushi saboda tafasar da yayi, shinkafar na dinga zubawa Ina nadewa ina sawa cikin sauce, na dakko fresh sweet pepper da ball pepper na cire hancin da yayan ciki na cika taf da shinkafar suma nasa cikin tomato sauce din na rufe don a samu penetration na komai. Ina kammalawa nayi kunu da juice saboda indai girkina mun hori a hannun Mama, Tun shekaru shida take samu grinding, bare, juya, zuba, wanke. Haka dai abubuwa shiyasa na tashi da son abin a raina. Ina gamawa na zuzzuba a inda ya dace sannan na koma daki inda na samu Missed calls din Abdallah kusan bakwai, wani irin muguwar faduwar gaba ta kama ni saboda tunanin abinda zaisa yayi min 7 missed calls. Jikina na rawa nayi returning masa call din, bugu daya Ya dauka yana fadin

"Haba my life, ina kika shiga haka. Inata kiranki"

Ajiyar zuciya na sauke jin he sounds normal and good kawai ya Kira Dan Ya tsoratar Dani ne, bata rai nayi tamkar yana ganina nace

"Dama lafiyar ka kalau ka kirani sau bakwai ka tayar min da hankali"

Murmushi yayi Har seda naji sautinshi a kunnena yace

"I badly wanted to hear your voice, shi ne kawai"

Murmushi nayi nace

"God, you scared every part of my being wallahi"

Dariya yayi wadda jinta kawai ke tsuma zuciya da gangar jikina, Abdallah is surely the death of me saboda ina mishi so me zafin zafi, kowanne bangare na jikina yana begenshi. Daga nan muka cigaba da hirar mu Har aka Kira Sallar Maghrib shi ne mukai sallama Se dare kuma a daura, haka yake routine a rayuwarmu. Amma duk wannan shakuwar tamu bata hanamu fada, idan muka tashi fada Se kuyi tunanin bamu taba shiri ba, kuma fadan on the silliest thing. Kamar ranarj Ya kirani da weekend da daddare nayi bala'in gajiya saboda naje gidan Anty Fadila wadda ciki yake bata wahala, komai ni nayi a gidan Se bayan Sallar ishai Hamma Mustapha yazo muka tafi. Ina shiga gida Ko parlor ban zauna ba nayiwa Mama seda safe na wuce dakina nayi wanka sannan na kwanta, cikin kamkanin lokaci kuwa bacci ya daukeni, har baccin Yayi nauyin da duk kiran da Abdallah yayi min Banji ba, seda asuba na bi call din yaki picking, banmasan kin picking Yayi ba, tunanina may be yaje massallaci Ashe shi fushi yake. Wasawasa seda mukai kwana uku bai kira ba, ban kira ba. Iya jigita Munyi donni har seda Mama ta tambayeni ko akwai abinda ke damuna nace mata babu komai, amma Hatta yadda nake activities dina duk na rage, na zama very moody Hakanan. Se a Rana na hudu na dauki wayata don na kirashi amma Ego da pride suka hanani, zuciyata tana nuna min abinda take so ne fa kada nayi kuskuren katse call din, Haka mind dina ke fadamin shi ne marar gaskiya, tunda ni na kira karshe amma baiyi calling back ba, wannan battle din yasa na jefar da wayar tareda dafe Kaina, inajin wani irin abu yana taso min daga zuciyata zuwa wuyana. Nasan is nothing but missing, nasan Yau na kai limit din da idan Banji muryar Abdallah ba akwai damuwa ta gaske kuwa, amma ego da pride Ya hanani. Har dare ina kwance sukuku duk inda na samu na kwanta Kamar ruwa. Can wajen isha naji Abu tamkar ya tokare min makoshina, cikin sauri na mike don Nemo inhaler ta amma na tuna ta Kare jiya kuma ba Wanda na fadawa, take kuwa ta tashi Inata fuzgar numfashin Har na fito parlor, a gigice Mama ta yo Kaina Tana fadin

HIKMAH Where stories live. Discover now