"Mom Tana tareda Lulu ne?"
Kai Mom ta girgiza tace
"I can't tell gaskia, abinda babanki yace na fada miki kenan"
Da sauri Hafsa ta Mike ta wuce dakinta ta bar Yaran dukkansu Sunyi Shiru babu me fadin wani abu, Tana shiga dakin Ta dakko wayarta ta Fara neman layin Ambassador, shi dinma kokarin dialing number ta yake zai sanar da ita yanxun zai taho daukar Yaran se gashi ta rigashi. Ko sallama batai mishi ba tace
"If you are free kazo ka dauke su Zahra, by 3am zamu bi flight zuwa Nigeria"
Yadda take Maganar baki daya ta hautsina shi don yasan babu lafiya daga sautin muryarta, amma bai Ko tambayeta ba se cewa Yayi
"Inshaaa Allah"
Daga Haka ya katse kiran ya fito, Hafsa mikewa tayi jikinta a bala'in sanyaye ta shiga harhadawa Yaran kayansu tsaf ta kammalla kuma har lokacin Ko daya a cikinsu babu Wadda ta biyo ta, suna tareda Mom Tana basu labarin batan Lulu dukkansu seda sukai hawaye saboda tausayinta da na yarinyar, shiyasa suka ga she need space.
Misalin hudu na yamma Ambassador Ya kira Hafsa akan yana jiranta a downstairs, mikewa tayi daga Kan praying carpet din da tunda ta hada kayan ta dana Yaran ta hau Tana Kai kukanta ga mahallici akan ya sassauta mata ya bata Ikon yarda da rungumar abinda zata tarar a Nigeria, Haka kurum jikinta ke bata Lulu is not together with Cynthia Dan tasan da tuni Aminu Ya fada mata, Se kawai ta saki kuka hannunta rikeda carpet din, wani irin matsanancin Tsoro yana addabar zuciyarta, bakinta nata maimaita kalmomin neman dauki daga Allah Har ta samu kukan Ya tsaya amma hawaye bai dauke ba, kafarta ta bude ta shiga fito da kayansu Zahra, Idanunta Sunyi jawur saboda tsabar kukan da tayi, a hankali ta shiga dakin Mom tace dasu
"Papa yazo yana downstairs"
Bata kuma fadar wani abu ba tayi kasa Janye da trolley dinsu, yana jiyo footsteps dinta ya mike tsaye tareda tsurewa benen idanu Har zuwa lokacinda ta bayyana gabanshi, fuskarta kusan rabi a rife take da veil din da ta yafo, idanu ya tsura mata gaba daya yanayinshi Ya canja daga murmushin da yake zuwa wata irin fuska me cikeda alhini.
Bata zauna ba kuma ta kasa bude baki balle tayi mishi magana Don data bude to tabbas kuka ne zai kubce mata and ita kuma abinda bata so kenan, kuka a gaban mutane.
Bayanshi tabi ganin Yayi hanyar barin parlon, jikin matarshi ta Embassy yake tsaye hakan yasa ta tsaya bayan an loda kayan a booth din motar, cikin sanyin murya yace
"Antyn Zahra kiyi hakuri, rayuwa tana zuwar mana yadda bama expecting Dan ba kowanne so ne yake zama samu ba. Kiyi hakuri Allah yana sane dake. "
AI yana rufe bakinshi Hafsa ta kara fashewa da kuka don ita daya tasan abinda takeji cikin zuciyarta, tayi kuka sosae bai hanata ba don yasan shi ne kadai saukin da zataji. Seda ta gama dake ya rigada yasan labarinta hakan yasa tace
"Dazun Alhaji yace mu taho Nigeria an kama Cynthia amma inajin a jikina Lulu is not with her"
Tana fada ta Kara kifa kanta jikin motar Tana sheshekar kuka, yayinda Ya dinga kwantar mata da hankali cikin tattausan kalami, a ranshi yana raya da ya halasta babu abinda zai hanashi rungumeta ya rarrasheta in the best of way amma hakan bazai yiwu ba sede da kalaman kawai. Seda ta nutsu sannan su Zahra suka fito suka rungumeta suna mata adduar Allah Ya kiyaye hanya.
Misalin uku na dare jirginsu Ya tashi zuwa Nigeria inda Zaiyi trans in a Egypt kafin ya karasa Birnin Lagos. Tunda sukai boarding flight din Hafsa take Karatun qurani cikin wata iPad dinta, Mom na gefenta Tana bacci, har seda gari yayi haske kafin Hafsa ta rufe iPad din ta runtse idonta, gabadaya tunanin abinda zata tarar take, bakinta banda Innalillahi wa Inna ilahil rajiun babu abinda yake maimaitawa, a hankali wani bacci yazo Ya saceta ba ita ta farka ba seda suka sauka a airport dake Egypt, awanni goma sha biyu zasui kafin su tafi hakan yasa suka nufi hotel suka huta, sukaci Abinci da sallaoli sannan sukai wanka.
Basu suka isa Lagos ba se bakwai na yamma, nanma kwana suka kara yi Wanda Hafsa gani take tamkar da gayya hakan ke faruwa, Don ta kagu ta ganta a Kano, inda a man aka kama Cynthia, maimakon a maidata Abuja kasancewar sune asalin masu case din se kawai akai transferring case din Kano.
Washegari da wurwuri suka wuce airport, jirgin da ya Fara tashi daga Lagos zuwa Kano suna cikin passengers din. Suna isa airport akai komai daya kamata suka fito. Mom ce ta Fara hango Aminu tsaye jikin motarshi Baka, Da dukkan alamu ya Dan jima Don se kallon hanya yake, Girma Ya fara kamashi Don a shekaru Arbain da doriya kadan ne babu, yana sanye da kubta kalar brown an zuba mata hand embroidery design coffee, kanshi hula ce ta asalin maiduguri, kafafunshi cikin wani ubansun Mister half cover, hannunshi dake rikeda wayarshi daure da wani agogo me igiya coffee na kamfanin Invicta. Kallo daya zakai mishi Kasan tabbas asiri a rufe yake, dukiya an Tara ta Don a lokacin yana matsayin Head of marketing and sales na bankin First bank na gaba daya Nigeria. Sede komai Yayi yadda akeso amma babu mata balle da, mutane Sunyi Sunyi Yayi aure amma yaki Dan ganinshi Hafsa na Raye wacce Macen zai zauna da kuma, ai sede idan Hafsa bata numfashi.
Tunda Alhajin sama ya sanar dashi shi zaije dakko Hafsa wadda ya manta rabonshi da ita, shidai abinda zai tuna tunda ta bar Nigeria bayan Ya saketa bata kara dawowa ba, Anyi rasuwa, Anyi bikukkuwa, Anyi suna amma Hafsa sede a waya, duk yadda Hafsa take da Salima sau biyu a shekarun Salima na haihuwa amma bata zo ba. Shiyasa guilt ke damunshi Har yakan samu kanshi da tantamar anya shidin yana son Hafsar? Tunda ya kasa zama da ita lokacinda take bukatar shi the most, dukda yana ganin hakan shi ne kadai saukin su amma baiyi tunanin hakan zata kasance ba Dan Yayi yunkurin maida aurensu sede Hafsa Sam taki bashi Hadin Kai.
Suna zuwa inda yake tsaye gaba daya Hafsa dashi kanshi Aminu dukkansu sakin baki sukai suna kallon junansu, wata irin kewa, wani irin bege, wata irin kauna wadda suka daskare gaba daya lokaci daya suka taso musu, wani yanayi me wuyar a fassarashi dukkansu suka shiga, babu bakin magana amma idanunsu kadai ya isa zama Dan Aiken.
Mom dai tsayawa tayi ganin Ikon Allah ganin yadda kauna take zuba a gurin, wani irin tausayinsu Ya lullube ta, Har Idanunta na kawo hawaye, gefen mayafinta ta sharce fuskarta sannan tayi gyaran murya Dan tasan sudai basa duniyar da muke ciki, Hafsa ce ta Fara janye Idanunta hawaye wani na bin wani, a wahalce Aminu Ya bude bakinshi tareda fadin
"Mom barka da zuwa, how was d flight?"
Kanta ta gyada masa tana fadin
"Tiring, but Alhamdulillah! "
Kanshi Ya gyada tareda bude mata baya ta shiga sannan ya zagayo ya budewa Hafsa gefenshi, babu musu ta shiga ta zauna har lokacin kuka take, kukan kewa, bege da kuma farin cikin ganin abinda zuciya ke muradi shekara da shekaru, a wannan takin ita kanta Hafsa ta manta dalilin zuwanta Nigeria saboda farin gani da tayi, seda Aminu Ya fara driving sannan yace da ita cikin barbarci
"Se yaushe Zaki daina kuka ne"
Juyowa tayi a hankali ta kalleshi sannan tace itama cikin barbarci Dan Mom ba fahimta take ba, iya zamanta a maiduguri basics din kawai ta iya amma bata iya yarawa sosae ba.
"Bansani ba nima, may be se ranar da dukkan bururruka na suka cika, ranar zan daina kuka"
Kanshi Ya gyada yace
"Inshaaa Allah ranar ta kusa zuwa. It's been long da muka hadu dake, kullum zuciya na kukan rashinki, eyes are longing to see you Hafcy, every night da kyar bacci ke daukata saboda rashinki, Hafcy yaushe zaki bamu abinda muke so? Yaushe Zaki bar zuciyoyinmu su huta? Yaushe zaki?..... "
Kukan da Hafsa ta keyi yasa dole yayi Shiru, se taji Kamar an bubbude mata duk Wasu channel na jikinta, a hankali son nan nashi da ya daskare ya fara narkewa yana bin circulation dinta, kafin mintuna ya zagaye ko ina cikin jini, tsoka da dukkan komai na jikinta.
_Jakadiyar kainuwa_