5⃣

2.5K 277 14
                                    

"Aminu I'm bleeding, ka take motar nan, kada cikinnan Ya fita"

Hafsa ta fada muryarta a dashe saboda ciwo ga hawayen dake tartsatsi a fuskarta, her only fear shi ne kada cikin ya fita. Hannunta Aminu Ya rike idanunshi akan titi yace

"Don't worry Hafcy, babu abinda zai faru"

A wancan shekarun health care delivery system na Nigeria ba standard Yake ba, hakan yasa Aminu nufar wani private facility da ita, suna zuwa aka karbe ta, cikin kankanin lokaci aka tsayar da bleeding din sede alamu sun nuna cikin ke son fita ta karfi da yaji. Seda tayi bacci kafin Aminu Ya samu ganin likitan Wanda fitowarsu kenan, bayan sun zauna yace

"Man, Munyi kokarin ganin cikin bai fita ba sede dole a kiyaye Don cikin na rawa "

Zufa Aminu ya goge wadda ta karyo masa yace

"Likita Meye mafita kenan? "

Seda ya gama Rubutun da yake yace

"Zamu riketa anan na sati daya Ko zuwa lokacinda zata zama stable, zata zauna on bed rest complete, banda aiki Kaima zaka daina having affairs da ita Har se cikin Yayi kwari. "

Kanshi Ya gyada sannan ya karba prescription yaje Ya siyo sannan Yayi settling bill. A take ya Kira Dada ya sanar da ita halinda ake ciki, sosae hankalinta yayi matukar tashi, Dama Alhaji Bukar na nan, da kanshi ya kaita har airport tayi catching next flight Se Abuja, kafin taje har Salima ta isa. Dukkansu seda sukai hawayen ganin halinda Hafsa ke ciki, tayi baki tayi rama Har lokacin baccin wahala take. Suma acan Maidugurin hankalinsu ya tashi sede Aminu Ya kwantar musu amma dukda Haka seda Alhaji Abbas yazo Wanda yana cikin Abujar yazo wani meeting dake tsohon general ne, shiyasa zafi Ya hadu da zafi ya bada wuta, tunda ya daura idanunshi kanta yaji dukkan wani fushi da fada ya kauce se tsabar tausayin Aminu da Hafsa ya kamashi.

Lokacinda Hafsa ta farka jikin babu laifi da sauki sede weakness da take ji Wanda aka tabbatar mata zai tafi Se a hankali. Tundaga wannan ranar bata kara bleeding ba se Dan spot da take gani jikin pant dinta. Seda tayi sati uku a asibiti, Yan dubiya kam babu adadi tunda daga ita har mijinta masu mutane ne, hakan yasa akai ta tururuwa dukda restricting shiga da ake Wasu lokutan. A hankali karfin jikinta Ya fara dawowa ganin Haka yasa aka sallameta Dada tace da ita zata wuce Maid, ko musu Aminu baiyi ba Haka aka tafi da ita, don shima jikinta tayar masa da hankali yake tareda bashi Tsoro.

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya sede tun ranar da Aminu da Hafsa sukai wannan dashen hankalinsu bai Kara kwanciya ba, daga anga Hafsa ta samu sauki ko kwanaki Bazaa kara ba wani zai dawo, ana tunanin ko cikin idan ya wuce watanni hudu zai daina bata wahala amma abu Kamar wasa Har cikin yakai watanni shida babu wani improvement. Ranar wata alhamis Aminu Ya dawo maiduguri daga Abuja anan ya tararda shockest sight of his life, Yana parking a Katon inda aka tanada na parking motoci, cikin saukakken kananan kaya yake, yana tafiya Kamar wani dawisu tsabar gayu da jin Kai, part dinsu Ya Fara dosa Kamar yadda ya saba sede kafin ya shiga yaga Dada ta fito a gigice, cikin Tashin hankali Wanda Ya kasa boyuwa a saman fuskarta, shima da hanzari ya nufeta yana fadin

"Dada lafiya? "

"Ina lafiya Aminu? Hafsa ce"

Seda yaji tamkar kanshi zai tarwatse tsabar yadda kalaman suka dakeshi, Hafsa again? Muryar Dada ta katseshi da

"Muje mu wuce asibiti, kada yar mutane ta mutu"

Ai ganinshi kawai Yayi gaban inda Hafsa ke durkushe Tana kelaya amai, ga jini kacakaca a inda take tsugunne, ga murkususu da take faman yi, jin Dada ta ambaci mutuwa, babu bata lokaci yasa hannunshi Yayi sama da ita, dukda jinin dake jikinta, a yau yasha alwashin a zubar da cikin koda kuwa wannan ne kadai rabonsu, Se lokacin yaji haushin kanshi, Ina amfanin badi ba rai Sunyi abinda ba Haramun ba, babu yarjewar kowa, babu neman Zabin Allah, Se lokacin ya tuna bai taba neman Zabin Allah ba shidai Hafsa tayi ciki ta haihu Ko Ta yayane, to Allah ya basu cikin ya dauke kwanciyar hankalinsu wani musiba kenan, tunda sukaje Germany Har zancen lokacin babu Wanda zuciyarshi ta kwanta, daga wannan se wannan.

Daidai isarsu inda motar Aminu take, daidai parking din Ammar (Babban yayansu Hafsa) yana fitowa Ya zare glasses din idanunshi yana fadin

"Subhanallah! Aminu lafiya? Hafsa ce? Ku shigo mu tafi asibiti "

Kusan a breath daya Yayi Maganar saboda yadda ya firgita, babu bata lokaci suka shiga sukaiwa Teaching hospital maiduguri tsinke, suna zuwa aka dubata akace CS zaai mata don sakaci zai iya sa yaron mutuwa, babu bata lokaci Ammar yasa hannu Kamar yadda Aminu yace, seda aka dauki Leda daya na jini daga Aminu daya daga Ammar sannan aka shiga da ita, gaba daya Dada banda Jan carbi babu abinda take,  can Sega Anty Yana matar Alhaji Bulama ta taho Itada Ummiey Mamansu Ammar, sun hado kaya. Ko mintina ashirin baayi ba aka fito da babyn wadda wata nurse ta fito da ita, Gabaki daya suka mike sede nurse din ta girgiza Kai tace

"Mace ce kuyi hakuri itama ta wahala Se anyi mata Yan dabaru"

Daga Haka ta wuce su zuwa ward inda suka cigaba da dakon fitowar su Hafsa, Ko awa baayi ba Sega shi an gunguro ta akan gado inda akai ward da ita, Haka suka bisu jiki a sanyaye da adduoi dauke a bakinsu.

Bata dauki wani tsawon lokaci ba ta farka, nan dangi suka dinga shigowa yi mata barka, itakam Tana kwance ta lumshe Idanunta Tana tunanin Haka ciki yake? Haka ake shan wahala? To Meye su Ya kaisu neman ta har Haka? Indai ta kara samun ciki ne to ta hakura ta yafe itakam.

Nurse din ce ta shigo ta dubi na ciki tace

"Se kun ragu Don ta samu ta huta"

Lokaci daya suka Fara fita aka barta itada Dada, babyn dake nannade cikin shawl pink aka miko mata bayan an tashe ta ta zauna, Idanunta ta kafe akan Babyn wadda ta rasa kammanin wa ta dauka, yarinyar kawai kyakyawa ce, ta zura yatsanta a bakinta tana sucking, Dada ta leko Tana kallon yarinyar yar mitsitsiya kasancewar ta preterm bata isa haihuwa ba, yatsa ta kai ta dungure mata kai tace

"karama yar Baka ta Hana yata sakat"

Murmushi Hafsa tayi ganin yadda yarinyar ta bude idonta ta kurawa Hafsa ido, that motherly love a take Ya mamaye Hafsa, Rungume ta tayi nan nurse din ta koya mata yadda zatai breastfeeding babyn Haka nan shigowar Aminu Yayi wukiwuki dashi, Ko ya manta da Dada na gurin kawai ya Rungume Hafsa da babyn tareda kissing goshin Hafsa yace

"You nailed it baby, you've given me every happiness in my life sweetheart"

Karbar yarinyar yayi Hafsa kuwa melting kawai take da kalaman Aminu, Dada kuwa ta fice tuni, yana zaune ya gyara mata ta saka ta a nono tuni yarinyar ta Fara sucking. Kallon juna sukai suka saki Murmushi babu farin ciki irin ganin danka a hannunka.... Allah ka rabamu da infertility!

Bayan Aminu Yayi Sallar ishai suka taho da iyayensu maza, don duba Hafsa shi baima karasa ba, Ya nemi wani call center ya Fara kiran Miss A'isha Kamar tasan da labarin kuwa Tayi picking, seda suka gaisa ya bata albishir din haihuwar Hafsa Kamar zata tashi sama dan murna balle yace daga ita Har babyn duk lapiya suke, Haka sukai sallama bayan Ya roketa akan Tazo ta gansu shima da kyar ta amince Don babyn Hafsa kawai zata zo.

Seda Hafsa tayi kwanaki bakwai a asibiti kafin aka sallameta amma banda babyn saboda jaundice (shawara) dake damunta ga wata irin Mura da zazzabi datake fama dashi, Haka suka cigaba da zama kullum ciwon yarinya gaba yake karawa, Haka nan a wannan Dan tsukin Miss A'isha ta iso ta tadda wata sabuwar. Rashin lafiyar yarinyar tuni hakan ya Fara tayarwa da kowa hankali Dan wani lokacin sede a saka mata oxygen, a Haka sukai kwanaki talatin amma jikin baby kam se a hankali kullum aka kwanta gani ake Kamar zata mutu kafin Washegari.

Yours Truly
_Jakadiyar kainuwa_

HIKMAH Where stories live. Discover now