Bayan Wata Biyu.
Bayan an tabbatar da dashen cikin da akai Ya dasu, Hafsa na dauke da ciki a jikinta Wanda ranar ta zame mata ranar farin ciki Har ta manta da Wasu matsalolinta. Murnar da tayi ba abar a bayyana bace don harda kukanta na murna. A wannan ranar aka sallame ta amma ko keyar Mum bata gani ba wadda ta dauke kafarta Tun ranar da tasan gaskiyar abinda ya faru, kimanin sati uku kenan. Ana gama mata duk abinda zatayi ta fito da kanta tunda jikinta Yayi kwari sosae ta samu lapiya, cab ta samu Ya kawo ta Har gida, Se lokacin ta tuna batada kudi hakan yasa ta roki alfarmar dakko masa a cikin gida, tana shiga living room din Mum na fitowa daga kitchen hannunta dauke da warmers cikin basket wadda niyyarta a ranar taje gurin Hafsa tunda tasan ko Abund ya riga ya faru bazai canja ba to tabbas tasan dukkansu Sunyi laushi.
"Mom kudi zaki bani na bar me cab a waje"
Wallet Mom ta bude ta ciro kudin sannan ta fita da kanta ta biya kudin ta dawo ciki inda ta tarar da Hafsa tana zaune, gefenta ta zauna Hafsa ta gaisheta ita kuma tana tambayar ta jiki,
"Am fit as you can see Mom "
Ta fada tana sakin murmushin jin dadi, kanta Miss A'isha ta shafa sannan ta umarceta tayi wanka suyi breakfast, Haka ta shiryo cikeda murna se shafa cikinta take Tana jin wani farin ciki marar misaltuwa yana addabar ta. She can't wait ta bawa Aminu wannan daddan labarin, tasan Se ya fita murna, cikin budadiyyar gown ta fito ta samu Mom Tana jiranta sede tunda aka bude warmers din ta toshe hancinta Se amai kuma ya biyo baya, sosae ta galabaita don babu komai a cikinta. Mom kam Se Jera mata Sannu take hankali a tashe, seda Tasha black tea sannan ta iya zama, lokaci daya Idanunta sukai zuruzuru ga waccan Ramar da tayi ga wannann daya tunkaro ta
"Hafsa karkiyi wata Jinyar kuma, da kin fada min kin daina son broccoli anymore"
Murmushin karfin Hali Hafsa tayi tace
"Mom I'm pregnant shiyasa"
Shiru Mom tayi ta tsira mata ido kafin koma ta Rungume ta cikin jikinta tana murna sosae ita ta manta Ashe dashen ciki sukai se Yanzun abin ya dawo mata.
Da daddare Hafsa ta dauki land-line ta kira office din Aminu amma bata sameshi ba, tayi Shiru Tana tunanin yadda zatai, can ta kira Maiduguri nanma Baa daga ba hakan yasa taji babu dadi a ranta. System din Mom ta dauka tareda tura mishi Email ko Allah zaisa ya gani.
Wasa farin girki! Tundaga wannan ranar Hafsa ta Fara laulayi me firgitarwa, gaba daya ta lalace gashi tunda Tazo Aminu bai waiwaye ta ba, shima ya gama kashe matsalar shi da su Alhaji dukda bawai sun sauka Duka bane amma abin Yayi sauki hakan yasa ya shirya zuwa America amma Kiran gaggawa yazo mishi daga Abuja akan Yayi reporting office, gaba daya Ko me yake hankalinshi yana Kan Hafsa, daida second daya Indai idanunshi a bude yake to Hafsa ce a ranshi sede duk hanyar da zasui communicating tamkar an toshe ta, gashi abubuwan da suka faru yasa yaji gaba daya son haihuwar Ya fitar mishi akanshi amma Hafsa na nan daram.
Sati uku da turowar wannan Email din na Hafsa sannan Aminu Ya gani, ranar murna Kamar zai zauce Dan farin ciki, duk wani Wanda yake kusada Aminu yasan da cikin har Yan maiduguri seda ya fada musu kuma yayi mamakin yadda suke murna suma, Habibu kam harda hawayen farin ciki na taya abokinshi murna. Duk yadda yaso zamewa ya tafi America abin ya gagara Haka yana gani sede suyi exchanging mail amma bata taba fada masa halin da take ciki ba, shi kuwa kullum yana siyan kayan taryar baby.
Cikin yana watanni uku wani dare Wanda Hafsa bazata taba Mantawa dashi a cikin rayuwar ta ba, saboda ita kanta bata saka ran zata rayu ba, Mom ta hada mata Salad taci dake yawanci shi tafi ci Se kuma wani lokacin tace tuwo ko abincin Nigeria Wanda Bazaa samu ba, Haka Mom zatai ta lallashinta Har ta hakura, sun gama ta kwanta wajen biyu na dare wani irin zazzabi me tsananin zafi Ya lullube ta, ta dinga amai Har Mum ta tashi a firgice ta kira Ambulance suka dauketa se asibiti, bayan shudewar mintuna Doctors ya fito yace da Mum idan sun yarda zaayi terminating cikin saboda wahalar da cikin yake bata, gashi akwai risk din cikin ya fita da kanshi idanma Baa zubar ba, Kai Mum ta girgiza cikin turanci tace
"This child is a precious one, gaskiya Bazan saka hannu a zubar dashi babu decision din Babanshi ba. A kyaleta kawai, I can't risk that"
Zuwa safe Hafsa ta girgije nan Mom ta fada mata yadda sukai da Doctor, Shima yazo ganinta Ya tuntube ta akan abin, ai take Hafsa tace Ina Babu wannan Maganar zaman asibiti kuwa ta gama kada suje suyi mata wani abu batareda saninta ba, Duk yadda Mom ke mata bayanin kin yarda tayi Haka akai discharging on request. Suna zuwa gida tayi wanka Tasha tea Se taji karfin jikinta, Mom ta fito hannunta rikeda key tace
"Hafsa Bari naje na dawo"
Kai Hafsa ta kada, Mom ta fice. Daki Hafsa ta koma ta Tarar Mom ta hade mata Duka kayanta cikin trolley, addua take Allah yasa Mum korata Nigeria zatayi, she can't wait to be in her husband embrace. Bayan wajen 3hours se Gata ta dawo, ta zauna gefen kafafun Hafsa tana fadin
"Exhausted"
Dan Murmushi Hafsa tayi tace
"Sannu Momma ta, Naga Kin hada min kaya cikin trolley, Ina zani? "
Gyara zama Mom tayi tace
"Nigeria zaki koma..... "
"Saboda me, nace na gaji da nan ne? "
Kai Miss A'isha ta girgiza tace
"No, cikinki na wahalar dake, Ina tsoron ya fita kina nan is better ya fita gaban ubanshi, so time din flight dinki 1am in the night, nayi communicating da Aminu akan yana jiranki"
Hafsa bata kara cewa komai ba, Dama kara take itama mijinta take so, Tana ganin idan da suna tare bazata dinga wannan Jinyar ba. Kunji Hafcy da magana!
Karfe daya na dare jirginsu Ya Mike zuwa Nigeria, tunda aka Fara Hafsa ke bacci Wanda ta manta last da tayi irinshi, ita dai karfin jikinta kawai take ji. Basu tsaya wani Trans in ba seda ya saukesu Babban Birnin Tarayya, Tana dira kafafunta ta hango Rabin ranta, her better person, her soul mate, da kyar ta iya clearing kanta ta isa inda yake jira, tana zuwa ya Rungume ta itama kankame shi tayi dukkansu suna jin sanyi a ransu tareda jin tamkar shekara sukai basu hadu ba.
Dayake weekend ce hakan yasa ranar babu inda Aminu yaje banda hidimar Hafsa, da ace akwai possibility wani yayiwa wani numfashi tabbas Aminu Zaiyi mata, Kamar ciwon da take yasan ta dawo gurin mijinta ya kwanta, a Haka sukai sati daya cikeda farin ciki da kwanciyar hankali sede Tana cika sati daya, masifaffen zazzabi Ya dawo mata, Babu shiri Yayi asibiti da ita anan ta Fara bleeding Wanda ya kara daga musu hankali.
Shatuuu ♥️