8⃣

2.6K 257 12
                                    

2009, December

"Hikmah! Hikmah!! Hikmah!!! Wai bazaki tashi ba? "

Juyawa nayi Dan ba karamin dadi baccin yake min ba amma tunda wannan nataciyyar Anty Fadila Tazo nasan tabbas baccina Ya kare, Juyawa nayi tare da bude idanuna Wanda na tabbatar Sunyi jawur tsabar baccin dake cikinsu,

"Anty Fadila Menene kuma? "

Cikin sanyin murya tace

"Tashi kiyo brush kizo kiji "

Babu musu na mike zaune, Kaina babu ko dankwali Se wata tujajjiyar kalba kusan guda goma, ta hade ko tsagar Baa gani, babu abinda na tsana duniyar nan irin kitso bana so bana kaunarshi ,Tun Mama tana tilasta min akan se Anyi kitson amma na kekashe bana so, ita Dama batada hayaniya hakan yasa duk abinda nake so kusan shi nake a gidan, matsalata guda daya ce a gidan Hamma Mus'ab, zaki kenan Haka nake kiranshi Dan kuwa kullum Indai ni dashi ne to babu jituwa tsakaninmu.

"Tashi mana Hikmah, sauri nake fa "

Bata fuska nayi tareda mikewa na nufi bayin dake cikin bedroom din nawa, brush nayi na wanke fuskata tsaf sannan na fito ina Jan kafata ta hagu, idan Ina zaune ka kalleni bazaka taba cewa I'm handicapped ba, amma ina mikewa zakaga kafata ta hagu dingisawa nake Ina limping dinta ne hakan.

Kallon kayan jikina nayi wata baggy shirt ce ta polio campaign da Hamma Mussadiq ya kawo min, se skinny a ciki, hula na zaro na kifa akan sannan nace

"Anty Fadila ina zamuje? "

Kalloma tayi ta ja hannuna muka fito Har parlour, kasancewar ranar asabar ce yasa babu Wanda Ya tashi a gidan kowa bacci yake, a tunanina nan parlon zamu tsaya amma Haka ta ta jana har wajen gate, Bance mata komai ba seda muka isa kofar wani gida Wanda gidaje hudu suka rabamu dasu, Dayake ba barina ake na fito ba Shifaaa babu Wanda na sani.

"Anty Fadila ina kika kawo ni? Mama ta hanani fita fa"

Takarda ta miko min tace

"kwankwasa gate dinnan, Ki bayar Kice a bawa Abdallah"

Idanu na zaro mata saboda ni mutum ce me Tsoro nace

"Kai Anty... A'a gaskiya "

Hararata tayi tace

"Dallah kije ina jiranki "

Kaina na gyada idanuna a warwaje na nufi katon ash gate din, hannuna nasa nayi knocking babu dadewa aka bude karamar kofar ta shiga, wani buzu ne yasha rawani ya kalleni tareda fadin

"ke yarinya ya akai? "

Murmushi nayi don ina son accent din buzaye, dariya yake bani. Letter na Fito da ita nace

"Gashi a bawa Abdallah"

Babu musu Ya karba ni kuwa nayo baya Ina dingisawa Abuna se Murmushi nake. Ina isa inda Anty Fadila ke rakube ta taso tana fadin

"kin bashi? An karba? "

Kaina na gyada Bance komai ba har muka isa gida, yadda muka fita a sace Haka muka koma a sace, wanka nayi na gyara dakin yadda zan iya na bar Sauran, uniform din islamiyya na saka sannan na fito, har lokacin babu Wanda ya fito balle nayi tunanin zan samu abin breakfast, maimakon naje na tashi Mama A'a kawai na bude fridge din dining anan nayi kyakyawan gani, yoghurt ne me sanyi chilled se guntuwar shawarma wadda ko rabi Baa taba ba, wani murmushin farin ciki ya subuce min ganin favorites dina, a take na zauna nayi munching shwarmar tas na bar wrapper akan table, yoghurt na jefa a jaka na fice se makaranta.

Mahaifana dukkansu su biyun bafulataine ne usul kuwa, fulanin jos ne na Barikin ladi, Baffa Malam Muhammad lecturer ne a BUK a physiology department, Mama complete house wife ce wadda bana tunanin ta gama secondary, kuma bata taba damuwa ta karasa ba balle tayi tunanin cigabawa, Hakanan take rayuwarta damu.

Gidanmu gidan zaman lafiya ne, rayuwar mu gwanin shaawa Haka take, Babban yayanmu Hamma Musbahu, da ace mace ne shi tabbas zai iya haifata, Tun Ina primary yayi aure yana Jos da family dinshi yana da Yara biyu, Matarshi Asiya se yaranshi Nusaiba da Nabila. Me binshi Hamma Mussadiq ne shine mutumina muna shiri sosae da sosae kuma duk cikin yan gidanmu nafi sonshi, baiyi aure ba yana Jigawa yana aiki da Primary health care Agency. Me binshi Hamma Mustapha shikam shi ne most reserve a gidanmu baya magana, dukda mu Yan gidanmu basuda magana ni kadai ce na fita zakka to amma Hamma Mustapha his on case is different, Lokuta da dama xakai tunanin ko yanada matsalar hankali ne amma a hakan yafi kowa yan mata, I wonder yadda yake tsarasu. Hamma Mus'ab zaki the lion in the jungle, duk gidanmu babu Wanda Bama shiri nake masifar Tsoro kamarshi, gamon mu Lokuta da dama baya dadi, dadina daya shi ne Mama Ko Baffa idan suna guri tabbas na tsira amma Indai ni da shi ne ko nayi laifi ko banyi ba se ya dake ni. Ni nake binshi, Mama tace Har ta fitar da ran kara haihuwa Se ta samu cikina, kusan shekara shida Hamma Mus'ab ya bani.

Dukkan Yan gidanmu farare ne tas Kamar ka tabasu jini Ya fito kana kallonsu kaga bafulataine ko Baa fada maka ba, kamanninsu dukkansu na Baffa ne ko Mama Wanda suma farare suke amma bandani, Baka ce ni, kuma mutane na kara ganin bakina kasancewar Wanda suke tare dani farare.

Sunana Zainab amma ana kirana Hikmah nayi primary dina a Kano model dake muna zaune a Matan fada cikin Birnin Kano. Yanzun Haka ina Js2 a Musa Iliyasu dake Rijiyar zaki. Wannan kenan!

Karfe sha daya na dawo daga islamiyya a gajiye, ga Yunwa dake addabata. Fuskata kwatakwata babu annuri Dan cikiciki nayi sallama, Mama dake zaune a parlour ta dago Tana bina da kallo Har na karaso na zauna

"Mama Ina Kwana?"

Da fullanci ta amsa min sannan tace

"Me kikaci da zaki tafi islamiyya"

Baki na zumburo nace

"Yoghurt na gani a fridge, Yanzun Yunwa nake ji"

Ta dade Tana kallona kafin tace

"Kinsan yoghurt din na waye kika dauka? Ba nace Karki kara daukar Abu idan baki tambaye ni ba"

Raina a bace nacr

"To Mama Yunwa nakeji fa! "

Bata kara cemin komai ba, nasan taji haushi ne Dama Haka takemin, Inda take naje na rungumeta ina rada mata a Kunne ita kuma tana ture ni seda ta Fara dariya sannan tace

"Sake ni kije abincin a dakinki"

Da sauri na saketa Ina murna na wuce dakina sede Ina taka corridor da zai kaika dakunan baccinmu naji kamshin daya sa naji muguwar faduwar gaba, Hamma Mus'ab the lion in the jungle kenan! Sunkuyar da kaina nayi zan rabeshi na wuce naji Ya cafki hannuna, idanu na bude jikina na rawa nace

"Hamma...."

Kallon daya buga min yasa na hadiye Maganar a makoshina,

"Ke kika dauka min yoghurt da shawarma a fridge"

Matsalata daya bana karya ko kasheni zaayi, hakan yana Kara bata ran Hamma Mus'ab Don shi yana son yaga ana tsoronshi, Kaina na gyada alamar ni ce, Mari ne ya biyo baya, Tun karfi na na bude baki na fara ihu Ina kuka, ganin hakan yasa ya ciro belt din jikinshi ya dinga tafka min a jikina, abin nema Ya samu Aikuwa se kuka da ihu, hakan yasa Mama da Hamma Mussadiq fitowa a hanzarce, yana ganinsu ya sakeni, da sauri Nayi bayan Hamma Mussadiq Ina kuka Dan dukan Ya shigeni sosae, Hamma Mussadiq dakina Ya jani yayinda Mama ta Kalli Mus'ab tace

"Mus'ab Nagode, Allah Ya saka da alkhairi"

Daga Haka ta juya ta nufi dakina inda Hamma ke rarrashina, da kyar naci Abinci duk yadda nake daukin abincin.

Jakadiyar kainuwa

HIKMAH Where stories live. Discover now