3⃣8⃣

2.3K 265 17
                                    

Da sauri na saka hannuna na dafe kuncina dan dukkan tunanina ni aka mara, se kuma Banji zafi ba hakan yasa na waigo kan Mupheeyda wadda tuni hawaye sun bata saman kyakyawar fuskar da ake takama da ita, Abdallah ne a gabanta, idanunshi Sunyi jawur saboda bacin rai, ban taba ganinshi a Haka ba tunda nake.

"Get out! "

Ya fada da karfi yana nuna mata hanyar waje, muryarta na bala'in rawa tace

"Yaya Abdallah, ni ka mara? "

Hannunshi ya Kara dagawa zai sauke mata wani, nayi saurin rike hannun tareda girgiza mishi Kaina, itakam tama sadakar zata sha Mari Har ta runtse idonta.

"Get out nace"

Ya kara maimaitawa, bude idonta tayi tareda min wani mugun kallo sannan ta gyada kanta tayi gaba, Binta yayi a baya har suka fita, se lokacin na sauke Ajiyar zuciya tareda dafe Kaina Wanda ya Fara min ciwo, wayata na dauka batareda nace komai ba nayi hanyar fita Dan Ko na zauna I'll understand nothing. Nazo tsakiyar hall din shima yana shigowa, turus na tsaya Har ya karaso inda nake, murya can kasa kasa yace

"Farin Cikina, are you hurt? "

Dan Murmushi nayi na girgiza kaina nace

"I'm ok as you can see"

Ajiyar zuciya me nauyi wadda har seda na kalleshi ya sauke sannan yace

"please, Ki koma ki zauna, ko kwantar da Kanki ne kiyi, but at least Ina ganinki a class din zanji dadi"

Yadda ya marairaice yasa nayi Murmushi na juya na koma seat dina, kowa a class din banda mamaki babu abinda suke baki a sake, kowanne tambaya ce bakinsu. Komawa nayi na zauna tareda sunkuyar da kaina shi kuma ya cigaba da lectures dinshi, gaba daya fuskar Mupheeyda ce kemin kai kawo a idona, saboda takamar ta Tana da wannan shouting beauty dake fading matsawar zaka dinga kallonshi for long. Sunkuyowa Nanah tayi tana magana a hankali

"Ke fadamin yaushe kuka dinke keda abokin fadan naki? "

Gyaran murya mukaji daidai saitin mu, a hankali na dago naji yana ce mata

"Nanah we need a rest fa, kada ki dameta da yawa"

Hararashi nayi shikuma ya dage min gira ya cigaba da abinda yake, Nanah kasa magana tayi Se binmu da kallo take. Can class din yayi nisa Sega level coordinator dinmu ya shigo, da dukkan alamu sun saba sosae da Abdallah yadda suke gaisawa sannan ya jashi waje sukai magana Se gashi ya dawo, inda nake yazo Ya tsaya yace

"Baffa yazo yana office din VC, go and meet him and please kada Ki damu... I love you"

Murmushi nayi na gyada Kaina na fita inajin ihun Yan class din amma baice dasu komai ba. Karo na farko da na taba tunkarar inda office dinshi yake, securities all over, seda na nuna appointment paper ta sannan na wuce. Basa main office din se wani Dan parlor like guri Wanda cushions suka kayata gurin, suna zaune su biyu gabansu Anyi musu serving juice se dariya suke najin dadi. Da sallama na shiga, lokaci guda Duka suka dago suna kallona, Kaina a kasa na tsuggunna na gaishesu, cikin faraa suka amsa, Baban Abdallah ya kalleni cikin sakin fuska Wanda anan na gano inda ziryan din kamannin Abdallah suke.

"'Yata ya Karatu? "

kaina na sake sunkuyarwa nace

"Alhamdulillah "

Kanshi Ya gyada yace

"To Allah Ya bada saa, ina fatan Babana baya hanaki Karatu Ko? "

Dan Murmushi nayi tareda girgiza Kai amma Bance komai ba, mikewa yayi bayan yasa na zauna dukda dardar da nakeyi ni a dole office din suruki! Sake gaisawa mukai da Baffa, gyara zamanshi Yayi yace

HIKMAH Where stories live. Discover now