2⃣1⃣

2.1K 236 13
                                    

"Na hakura! "

Kalmomi biyu ne amma sun girgiza duniya ta gaba daya, ban taba jin kalamai masu daci a rayuwata ba se wannan, sun dake ni, sun kunce min duk wani abu da nake Takama dashi. Da sauri na samu guri na zauna ina jikina ya Fara rawa nace

"Abdallah! Ka hakura? Dani? Da soyayya ta? Ka manta promises dinka? Dama yaudarata zakai"

Hawaye shar ya Fara gangaro min, se yayi Shiru na seconds kafin yace

"Ko daya Hikmah, ina sonki amma Dama nasan ni dake ba aure Zamui ba, banda abinki Hikma Ina zan kaiki ai Kinyi min girma, ai Saar aurena itace wadda take primary a ynzun amma bake ba. Nagode sosae for your time and love, banso ace ta Haka zamu rabu ba, amma Baffanki yazo da bidi'a! Allah Ya baki wani"

Bai jira abinda zance ba ya kashe wayar, duk duniya a rabuwa da Abdallah regret dina guda daya ne, da ban cinye masa mutunci ba, da ban nuna masa Wacece real Hikzeey ba, da ban zagi uwarshi da ubanshi ba. Ajiye wayar nayi akan gado na nufi toilet na dauro alwala da yake banyi Sallar ishai ba. Ina fitowa na saka lock a dakin, na Nemo inhaler na aje a gefen praying carpet dina. Sallah na tayar Inata kokarin ganin conversation dinmu da Abdallah bai dawo ba, seda na kai sujjada ta karshe wadda daga ita na idar, a lokacin naji Ya kamata na fadawa Allah damuwa ta, nasan shi kadai zai amsa min, shi kadai yasan halin da nake ciki. Ina furta

"Ya Allah! "

Se naji wani irin rauni Ya ziyarci zuciyata ai se kuka, na dinga kuka inajin wani nauyi a kirjina. Nafi mintina ashirin a Haka seda naji Kamar zan shide sannan na dago nayi tahiya nayi sallama. Hannayena nasa na rufe fuskata dashi Inata kuka. There and then na fahimci dating a charming guy shi ne abu mafi hadari da mace zatayi, saboda suna ganin suna da kyau duk inda suka shiga mata ke binsu basu ke binsu ba. Abdallah taught me a great lesson a rayuwata.

In takaice muku ranar akan dandanyar tiles na kwanta duk sanyin da ake, idanuna suka kekashe banda kuka marar sauti babu abinda nake, abin ya kada ni, it was unexpected, I never expect such daga gareshi.

Wajen Karfe goma na dare, Mama Tazo tana ta buga min saboda ban ci Abinci ba, amma ko kokarin budewa banyi ba, se kuka daya Kara kwace min. Ni daya nasan abinda yake faruwa cikin zuciyata, ni kadai nasan wutar da ake rura min, se naji tamkar son Abdallah aka kara min.

Karfe uku na dare bayan nayi sallah bacci me nauyi Yayi gaba Dani, bacci marar dadi da duk yawanci mafarkan Abdallah ne, wai yazo yace min wasa yake min, he never meant his words. Koda asuba kasa tashi nayi se wajen shida na safe nayi sallah nayi wanka sannan na duba mudubi, seda na tsorata saboda ganin yadda idanuna sukai jawur, fuskata ta Dan tashi, gefen idanuna saboda zubar hawaye duk wrinkles Sunyi forming a gurin. Kaina na dafe saboda bansan Wanne bayani zanyiwa Mama ta yarda ba. Sai na tuna weekend ne Zanje islamiyya, haka nayi sauri na saka uniform dina, koda na fito as usual kowa baccinsa yake Shara, haka nayi tafiyata ban nemi Abinci ba.

Da naje islamiyya babu kowa, haka na zauna na zabga tagumi inajin yadda zuciyata take zafi amma hawaye ko diso yaki zubowa. Na jima kafin students suka Fara zuwa akai Shara sannan muka shiga aji. Kowa ya ganni Se ya tambayeni ko lafiya? Hatta Najaatu kasa fada mata nayi, na fada mata nace me? Haka nayi Shiru Abuna, ina bada hadda naje can karshen class na zauna har kowa suka bada tasu. Adduoin cikin hisnul Muslim mukai sannan aka tashi. Tunda muka taho Najaatu ke cemin

"Yau Abdallah bazai zo bane? "Kaina na girgiza mata kawai saboda bakina yayi min nauyi, kuma Haka kurum bana son yawan magana idan ba dole ce ba. Da na koma gida Mama Tana dakinta Dan Haka can na sameta muka gaisa, ta kura min ido tamkar me son gano wani abin, Nidai mikewa nayi kawai na fita zuwa dakina.

Tundaga wannan ranar shikenan muka kulla da zaman daki, Kai ka rantse kace nan aka haifeni, na daina yawan surutu da nake a baya, Abinci baifi sau daya nake ci a Rana ba, duk nabi na rame na lalace. Mama se ta tambayeni Kamar sau biyar a rana meke damu na, amsa daya ce babu komai Se wani lokacin nace kaina yana min ciwo, kuma ba karya nake ba, kullum dashi nake wuni nake kwana, hakan ya Fara tsoratar da Mama , Baffa kam yasan dawar Garin, ya dai zuba min ido ne dukda wasan buya nake mishi saboda bana son mu hadu yace na tura mishi Abdallah, Haka yasa kawai na yankewa kaina shawarar daina zaman parlour, shima baya nema na. Hamma Mussadiq dif shi da matarsa tamkar Anyi ruwa an dauke, ni tashin hankalin da nake ciki bai barni na fahimci Anty Fadila fushi take Dani ba.

A Haka a daddafe nayi sati biu da faruwar abin. Idan kuka kalleni se Kunyi min kuka, saboda Ina cikin mutanen dake saka damuwa a ransu, Ina cikin mutane dake zafafa Abu, basu taking things easy kwatakwata.

Da daddare Kamar kullum ina dakina, Mama ta tafi dakin Baffa yana kwance yana kallon network news dake har Karfe Tara tayi. Zama tayi gefenshi cikeda damuwa tace

"Nikam Kamar Baka san halin da Hikmah take ciki ba a gidannan, ka tattara mu ka watsar. "

Gyara zamanshi Yayi yace

"To me zance muku? Kunyar Idanunta nake Maman Musbahu. Saboda abu take so, banda shi Bazan iya bata ba, inda Inada karfin Ikon aura mata Abdallah wallahi se na aura mata shi, amma Yaron gabaki daya bayada niyyar alkhairi Dan da yana sonta to zai turon Mahaifinshi muyi magana, amma yaki, kuma nayi niyyar idan Mahaifinshi yazo ko shekara hudu ne zan jira amma yaki, Kinsan har office din Babanshi naje, da ya kirashi se cewa Yayi baya sonta..... Ya zanyi? Bansan yazan lallashi Hikma ba"

Ajiyar zuciya me nauyi Mama ta aje, cikin damuwa tace

"To Yanzun ya zanyi kenan? Yazan mata, babu abinda na tsana Kamar ganinta a damuwa."

Tashi Baffa yayi yace

"Muje na ganta. "

Banyi tunanin kowa zai shigo min daki ba shiyasa banyi jamming ba. Ina zaune saman praying mat din Dana idar da sallah, na fada kaina da gwiwa ta ina kuka, Nima na gaji da halin da nake ciki, inason na koma Normal self dina amma zuciyata taki bani Hadin Kai, kwatakwata na kasa cire wanna Kalmomi biyu da Abdallah ya fada min, na kasa tsayawa na rarrashi kaina.

Ji nayi an turo kofa, da sauri na dago tareda mikewa tsaye ina share hawayen idanuna da Hannayena, it's too late dan sun rigada sun gani, Gabaki dayansu fuskokinsu babu walwala, babu wani annashuwa se Tashin hankali Mussaman ganina ina kuka.

Mama ta riko hannuna ta zaunar dani Kan sallayar Dana tashi akai, idanuna a warwaje saboda Ko Naki ko Naso yau dole zan fadi matsalata. Ga mamakina babu Wanda ya tambayeni se nasihohi da Baffa ya dinga min akan yadda da kaddara. Hakan nan se naji zuciyata tayi sanyi , na Rungume Mama na kankameta Inata kuka, amma Tundaga wannan ranar

HIKMAH Where stories live. Discover now