4⃣1⃣

2.2K 278 32
                                    


Thank you so much Yaah kaagu... Oum Naeeym, she just called and told me ina shigowa kano na mata waya, grilled chicken and milk shake na jirana, saboda na aurawa Maina HIKMAH. Oh Allah I felt loved, Nagode sosae. I can't wait to see Friday..... Kwadayi tinx

A wannan lokacin ji nayi kamar na kashe Kaina saboda wani irin bakin ciki da ya turnuke min zuciyata, da ace an barni na kadaice wallahi ko ban kashe Kaina ba se nayi attempting suicide. Gaba daya rayuwar baya Hamma Mus'ab yayi ta ne akan cutar dani amma wannan abin da yayi min shi ya wanke dukkan laifufukansa.

Baffa dasu Hamma Sunyi iya bakin kokarinsu ganin sun bani baki, jinsu kawai nakeyi Dan jikina na fada min bayin kan Abdallah bane, no way Abdallah yana hayyacinsa zai ce bazai aureni ba, wannan Maganar hankalina bazai dauka ba. Naso ace da Abdallah yace ya Fasa Baffa baimin auren dole ba Naso ace kyaleni yayi na samu wani amma tunanin yadda zanyi coping da zama da Wanda bana so shike kara sani kuka.

Kowa ya tafi ya rage daga ni se Nanah se Aneeysa wadda mijinta ya dawo da ita se kuma Najaatu. Tun tuni na cire kayan ina zaune kan sallaya na idar da Sallar ishai, kaina cikin cinyoyina ni ba kuka nake ba amma gwara ace kukan nake. Gashi a lokacin nasan tuni BP na ya hau sboda dukkan Wasu signs sun bayyana. Wayata dake hannun Nanah ce ta Fara ringing,

_Nothing is gonna change my love for you, you ought to know by now how much I love you, one thing ......._

Ko bata miko min ba nasan Abdallah ne kadai yakeda wannan ringtone a cikin contact dina. Katse kiran Nanah tayi hakan yasa na dago da sauri, dukkansu kallona suke nace cikin dasashiyar murya

"Nanah, Ya kika katse?"

"Me zai ce miki kuma, bakuda alakar da ta rage"

Kaina na girgiza hawaye na sauka a hankali nace

"We have Nanah, baimin bayani ba, bansan dalilinshi ba. Nima kukan nan da nakeyi ba so nakeyi ba, na gaji dashi....."

Ban karasa ba naji Ya sake kira, cikin sauri na karba nayi swiping tareda amsawa

" _Farin cikina_ Ban cika alkawarin da na dauka miki ba, I failed you, I didn't fulfilled promises din da nayi miki. Da nasan Haka zamu kare da ban kulaki ba, da banyi breaking miki zuciyarki ba, duk yadda bansan ganin kukanki amma Ni ne sanadin kukan..... "

Tuni na fashe da wani irin kuka, zuciyata gaba daya ta narke, bai hanani ba seda nayi me isata sannan nace

"Just tell, from the start dama abinda Kake nufi Dani? Dama duk alkawarrikan daka dauka ba Har zuciya suke ba? Abdallah why will you do this, why will you?..... "

Ban karasa ba wani kukan ya Kara kubce min, nayi kuka sosae shima bai hanani ba, seda nayi me isata kafin yace min

"Kiyi hakuri Hikmah, nasan a gurinki I'm a monster, nasan na cancanci dukkan Wasu sunaye da zaki kirani dashi, amma abu daya nake so dake Dan Allah ki saurareni"

"Bayan mun gama waya, nace miki na dawo daga massallaci. Straight hotel din da muka sauka da Abbu nan mukaje, tuntuni shi ya shirya nima dakina na shiga na shirya. Abinda zan tuna Abbu yace min muje kada mu makara, daga nan na yanke jiki na fadi, Nidai consciousness dina bai dawo ba seda akai Sallar Maghrib daf da ishai. A gigice na mike ganin duhu Ya shiga, na kalla mutanen gurin, Abbu, Ummiey, kannen Abbu biyu da kannen Ummiey, Idanunta Sunyi jawur alamar Tasha kuka, hannunta na kama ina kuka nace, Ummiey An daura auren? Na aura hikman? Gaba daya Shiru sukai suna kallona se Abbu ne ya cemin, Abdallah cewa kayi Baka sonta ka fasa aurenta, cewa kayi daka aureta gwara ka mutu, I wanted to force you aurenta amma yadda kayi baimin dadi ba, Abdallah haka na kira mahaifinta nace a aura mata wani, a take kuwa Yayi mata miji, ka dauka haka Allah Ya tsara maka. Hikmah kuka kawai nake Dan nasan I was possessed, bayin kaina bane...... "

Gaba daya seda tsikar jikina ta tashi saboda yadda yake kuka, Nima Haka na shiga yin nawa bazance asiri bane kai tsaye amma abin da mugun mamaki, all of a sudden.

"Ki yafe min, ki sani ina sonki Bazan taba Mantawa dake ba. Ashe we're not meant to be, dama wani baya aurar matar wani. Inasonki Ina kaunar ki Hikmah, Naso aurenki na rayu dake amma Allah bai nufa ba, ke matar wani ce. "

Munjima muna hira dukda inner self dina na fadamin babu kyau hakan amma naji hankalina ya kwanta sosae, at least naji sanyi saboda nasan ba yin kanshi bane, na yadda dashi Haka nan naji hankalina ya kwanta. Seda na daina kuka Har ina Murmushi sannan Yayi min adduoi tareda fatan alkhairi, Naso sosae na Tambayeshi Mupheeyda amma nasan ba hurumina bane.

Ina aje wayar naji wata irin nutsuwa da dangana Ya shiga zuciyata ban taba tunanin hankalina zai kwanta ba Kamar haka. Mikewa nayi daidai shigowar Hamma Mus'ab, Da murnarshi yace

"Hikmah, Alhamdulillah! "

Dan Murmushi nayi ya miko min Leda hannunshi yace

"Zauna kici"

Komawa nayi na zauna dukda banida appetite amma Haka na bude ledar, shawarma ce da yoghurt, kallonshi nayi Ina Murmushi na tuna Marin da nasha akan wannan abin. Kaina na girgiza Ina tuna rayuwa, Surely no condition is permanent in life! Seda naci sannan nace

"Hamma waye aka aura min? "

Zamanshi ya gyara yace

"Bansanshi ba amma nasan yanada nasaba me kyau, sunanshi Ibrahim, Likita ne. Asalinsu Yan maiduguri ne. Shine kawai abinda na sani game dashi. Kinyi saa shi ne abinda kawai zance miki, Inshaaa Allah bazakiyi regretting ba. "

Lumshe idona nayi bance komai ba, se can yace

"Jiya Bakiyi bacci ba, kije Ki kwanta ko. "

Kaina na gyada na mike nace

"Hamma thank you for everything"

Kanshi Ya gyada yana min Murmushi na wuce dakin da aka bani, Nanah tuni tayi bacci Nima alwala nayi na kwanta gefenta, tunanin kullum ne a raina ko waye mijin? Ko ya kamarshi take, a Haka bacci yayi gaba Dani. Mafarkin Abdallah Munyi reuniting shi ne komai.

Washegari shi ne birthday Dina, nayi bacci bayan Sallar asuba bani na tashi ba se goma shima saboda Nanah zata tafi ne, Har mamakin yadda na dangana nake babu attack balle BP rise. Seda muka kaita har Tasha sannan na dawo nayi wanka, doguwar riga Aneeysa ta bani na saka, muna parlour dukkanmu muna hira, ga cake Hamma ya siyomin, yana aje ko yankawa banyi ba se wayata dake hannuna Inata replying messages na jaje da fatan alkhairi hade da birthday wishes.

Twitter na shiga ina dudduba abubuwa kawai naga tweet din IBmaina, ciki sauri na bude hoto ne amma yana loading bakai ga budewa ba, a caption yasa *Today marks 21 years, since you were kidnapped, we love you so much and we missed you, I..... "

Ban gama karantawa ba picture Ya bude, gabana yanata faduwa na bude picture, bansan lokacinda na zabura na mike ba, Inata kallon hoton, ni ce wallahi babu tantama ni ce, so CBN governor is my father, lumshe idona nayi, dukkansu basu kula dani ba seda na fito rikeda veil, sannan Hamma yace

"Hikmah ina zakije? "

Gyara yanayina nayi nace

"Yanzun zan dawo, gurin Mama zanje"

Ban jira abinda zasuce ba nayi gaba, Inata wulla kafa Kamar zan hantsila, kwanya ta ta cushe. Ina zuwa Naga Baffa yana nan I'm sure suna tare, hakan yasa na lallaba na shiga dakinta, trolley nan da Naga kayan nan da hand tag tana nan saman wardrobe, Hawa kan gado nayi na sakko da ita, kayan ne kawai a ciki snapping nayi daya bayan daya sannan na rufe na mayar na fita babu Wanda yasan da shigowata. Gidan Najaatu na wuce na shiga dakinta na Fara mawa IBmaina DM da pictures din a kasa nace

_I might be the missing baby!"

_Jakadiyar kainuwa_

HIKMAH Where stories live. Discover now