4⃣9⃣

2.7K 310 29
                                    

Bayan Watanni Hudu

Tunda na farka Sallar asuba nake jin wani irin Kwadayi, kuma na cheese abin mamaki ni ba fan din cheese bace Mussaman cheddar cheese, bana sonshi. Amma Yanzun tunashi idan nayi se naji wani salivation a bakina. tare mukai alwala Ya wuce massallaci, ni kuma nayi rakaatanul fajr sannan na tafi kitchen. Freezer na bude na ciro wata bowl da froze chicken breast yake, Allah Yasa shekaranjiya muje shopping na siyo Harda cheese din. Fito dasu nayi daga fridge na aje dan su sake jikinsu. Ball of yellow pepper, da green da red na yayyanka Manya Manya. Sannan na dakko baking tray, nayi greesing dinshi, na jera chicken breast din akai, peppers dinnan na zuba akai, nayi seasoning sannan na yaryada Mai nasa a oven. Flour, Mai, gishiri na kwaba da ruwa, kamar kwabin meat pie na barshi ya saki jikinshi. Daki na koma nayi sallah. Inata mamakin kaina, duk yadda nake da ci bantaba jin inason abu wuta wuta ba irin Haka ba. Mamaki sosae nake. Ina idarwa ko adduar Arziki banyi ba na koma kitchen. Ina zuwa na Barbada flour kan working surface na dakko pin ina fadada ta in a round shape, wani round cutter na dakko na yanka ya fitar da shape din sosae. Seda nayi goma sannan na dakko nonstick frying pan na daura akan cooker, low heat, nayi greesing da mai sannan na dakko round shaped flour ina sawa, idan Yayi na juya. Har na gama. Na aje ya huce na Fara hadawa Armor abincinshi, ya koma aiki, yana nan a National hospital nan yake. Yanzun consultancy dinshi yake a cikin asibitin.

Idan ya fita tun safe se yamma yake dawowa. Har tausayinshi nakeji, gaba daya bani shawa'ar clinicals, its requires more than sacrifice and effort, shiyasa ban taba under looking dinsu ba, sunbar uzurinsu da dukkan komai sun taho Dan aikin jamaa, amma laifi daya gaba daya se ayi stereotyping dinsu, many of them are good, kuma zarar kana aiki da mutane ko Bakada fada dole Seka koya. Ba'a kallon su patients da patient relatives abinda sukeyi, al'amuran da suke bai dace ba amma na iya health workers ne Yayi zafi most especially Nurses. Kuma Inada tabbacin mafi yawan mutane mutuncin da Nurses sukai musu yafi rashin kirkin da sukai musu. Allah yasa mu dace.

Kunun gyada na hada masa da farfesun kifi Wanda tun jiya nayi yau warming kadai nayi. A gefe nayi setting na dawo kan nawa abincin. Sliced mozerella cheese, na saka cikin wannan pita bread din dana gasa, pita bread a kasa, sliced mozerella cheese guda biyu se na rufa wani pita bread a sama. Na jera akan baking tray bayan nayi greesing. Wannan Chicken Breast din na dakko, Yayi laushi sosae, fork nayi using na farfasa shi, na zuba tsakiyar pita breads dinnan, na grating cheddar cheese na watsa akai na rufa Wasu bread din masu cheese akai na maida oven. Zama nayi na hada plain black tea, Inasha.

Daki na koma, ga mamakina Har ya fito a wanka, taya shi nayi ya shirya ina ce masa

"Amma Armor ka shigo Baka nemeni ba"

Shafan Kai yayi yace

"Naga Yau Kwadayi ya tashi, tun asuba ana kitchen kinga gwara na barki kafin Anjima Kice na dameki"

Bakina na turo Ina fadin

"Dama Haka mukai dakai? Are we not team? "

Hannuna yaja muka fita zuwa kitchen yace

"Ai munfi team, mu squad ne, so kinga ni dake babu me jin kanmu"

Hannuna na dunkule shima ya dunkule muka buga sannan nayi ihu tareda rungumeshi, nasan mijina baifi mijin kowa ba amma a gurina, Ina ganin babu kamarshi, babu Macen da zata zo tayi min bragging akan mijinta. Na yadda akwai matsaloli sosae cikin aure kuma ko Yaya kuke son Kanku dole ne Ku fuskanci hakan amma ranar da aka kawoni gidannan, yace min aure consist of 3 building blocks, Trust, communication and perseverance. Hakane su Muka rike shiyasa muke ganin daidai. A Yanzun Ina ganin munfi Wasu Wanda sukai shekaru goma in curtship Sannan sukai aure, to munfi su son juna da tattalin junanmu, shi nawa ne nima tashi ce. Kullum ina Kara shiwa Hajiya Talatu adduar shiriya at least tayi kokarin wajen kara kusanto ni nida abin kaunata.

HIKMAH Where stories live. Discover now