3⃣6⃣

2.4K 276 23
                                    


*Russia*

"Like seriously yarinyar Kake jira Har tsawon wannan shekarun Maina, are you serious or you kidding me?"

Dr. Dalhat Ya tambayi Maina yana Kara sakin dariya Hade da tafa hannu, Maina dake zaune kawai kallonshi yake bai iya cewa komai ba, saboda shima yana ganin foolishness dinsa, ta Yaya zai zauna jiran abinda bai da masaniyar wanzuwar shi a duniya, it's been 20years kenan tunda ya Wayi gari Ammiey tace masa an sace Lulu, yana ta kuka ya yini baici Abinci ba, da sukaje Maiduguri Dada tace mishi ai zata dawo, duk inda take zata dawo, kodan wannan alkawarin auren da akai. Wannan auren zai dawo da ita gida shidai Ya dage kawai da addua. So Dada ita ta saka mishi wannan hope din, ita ta Kara dasa mishi wannan soyayyar tareda rike alkawari amma kwana biyunnan bukatunshi suna neman fin karfinshi, shekarunsa sunkai yadda yake bukatar opposite gender Dan Ya cika mutum kuma namiji, so har ya Fara tunanin Anya bazaiyi aure ba idan yaso duk lokacinda Allah yasa ta dawo gida Dan shi jikinshi na bashi she's coming, she'll come for him. To amma tambayar ita ce yaushe? Se yaushe zata dawo? Ta Yaya kuma? Bai sani ba, Allah shi ya barwa kanshi sani.

"Abokina Ya zanyi? Nifa saboda yadda na sata a rai ko kallon Wasu matan banayi balle har naji Meye taste dina"

Wani kallo Dr. Dalhat yayi mishi sannan yace

"Seriously this is Delusional, ban taba tunanin zanji makamankciyar rayuwa irin taka ba Maina, how can you? "

Se kuma yayi Tsaki sannan yace

"See, wata ya rage kawai mu gama komai, ka manta da yarinyar kawai kayi aurenka, ina wannan yarinyar dake stalking dinka? Ka aureta mana amma babu yadda zaayi ka zauna jiran gawon shanu, what if idan Tazo ka ganta gurguwa ko a nakashe? Zaka sota still"

Se a sannan Maina Yayi dariya tareda buga kafadar Dalhat yace

"Mutumina kana sha'aninka, wayace maka zan sota ne? Ai zuciyata da sonta ta ginu kaga I'll accept her da duk yadda na ganta, as far as zata kauda Idanunta daga flaws dina bana tunanin akwai abinda zai gagara"

Kai Dalhat Ya Jinjina  tareda kurbar coffee din da tuntuni ya dade da yin sanyi, Dan tuntuni akai serving dinsu amma saboda they're heated up in a serious conversation shiyasa basu ma sha ba, seda ya shanye tas sannan ya aje tea mug din akan saucer yace

"Kafi karfina Maina, kasa yarinyar da yawa a zuciyarka. Allah ubangiji ya zaba muku mafificin alkhairi. Amma kayi Trusting rayuwa da yawa"

Kai Maina Ya girgiza yace

"Nagode sosae Abokina Kaima you have contributed so far. Amma Kasan ba rayuwa nayi trusting ba, Allah nayi trusting, nasan addua ta bazata taba tashi a banza ba. Kaidai mu hanzarta muje class"

Mikewa kawai sukai suka nufi inda zasuyi lecture din.

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, by each passing day zuciyata tana kara karbar Abdallah, tana kara nuna min shi din shi ne abinda ya cancanta Dani. Gaba daya Abdallah ya siye min zuciyata banida wani tunani idan ba nashi ba, kome zanyi se na Fara fada mishi ya bani shawara kafin nayi. A hankali har wata guda Ya tafi anan naje weekends Kano, munjima muna hira da Mama sannan nayi wanka naci Abinci nayi sallah na dasa waya.

"Farin Cikina baki ganin ya dace su Papa suzo ayi formal magana, Nifa gwaurancin nan ya isheni haka"

Dan Murmushi nayi nace

"Kai Tun Yanzun ka bari idan na gama level 3 se ayi Maganar kafin azo bikin kuma na gama school gaba daya"

Wata dariya ya saki yace

"Haba? Da gaske kike? Tabdijam! I can't wait gaskiya, Dan ni so nake nanda 4months ace kina gidana"

Idanuna na zaro tareda marairaice fuska nace

HIKMAH Where stories live. Discover now