Finale

3.3K 334 48
                                    





OXFORD UNIVERSITY, ENGLAND.

20years leap

Cikin makeken conference hall na medics dake cikin university, manyan likitoci, Wanda suke daga mabanbantan kasashe across the world. Wani workshop ne hade da conference aka hada anan akan Head transplant da ake son a gwada.

Dr. Ibrahim Maina yana daya daga cikin mutanen da suka samu privileged din zuwa wannan conference din, kasancewar duk Nigeria babu wani Neurosurgeon da yayi fice yasan aikinshi Kamar shi.

Karfe hudu Dr. Canavaro wanda shi ne leader na wannan head transplant din, yayi akan monkey which was proved to be successful, har monkey yayi surviving for 20hours sede unconscious. Shi ya bada closing remark, da lokacinda Zaa Kara Haduwa ranar Monday.

A gajiye tikis Maina Ya fito daga dakin taron, shekaru sunja kana kallonshi Kasan Ya manyanta, amma jin dadi da kiyayewa yasa hakan bai nuna sosae ba. Cab ya samu ta kaishi har flat din da ya sauka. Hannunshi yasa ya kada door bell din sannan ya tsaya yana jiran a bude. ya kusan mintina uku sannan aka bude kofar, wata kyakyawar mace ce a tsaye wadda shekarunta suka Dan ja amma ba can, Har Yanzun kamanninta yana nan babu wani abu da ya canja, Illa cika da ta kuma, da nutsuwa hade da alamun kwanciyar hankali.

Briefcase dinshi Ta karba, fuskarta dauke da Murmushi tace

"Masoyi, Barka da zuwa. You look tired"

Murmushi yayi yace

"Ganinki ya warware komai gimbiyata. "

Hannunshi yasa ya sakalo na Hikmah wadda fuskarta babu komai banda Murmushi madaukaki. Tare suka shiga, cikin cushion Ya zauna yana fadin

"Gidan Yayi Shiru, Ina Sauran Yaran da Hamida? "

Aje glass cup me cikeda ruwa tayi tace

"Sun fita yin shopping, sannan akwai wata kawarta zata biya"

Kanshi Ya gyada yace

"Muje Yau a tayani nayi wanka, kafin su dawo a bani excuse"

Dariya tayi tace

"Kai Ko? "

Hannunshi ya Mika mata ta kama, suka wuce bedroom dake can gefe, gidan babu laifi yanada girma, katon parlor ne, me kunshe da bedrooms biyar, akwai na Hikman daya, Hamida daya, yaransu mata biyu se dayan na mazansu.

Seda ta tayashi yayi wanka sannan suka fito, sukaci Abinci aka koma daki aka baje soyayya, wadda bata taba tsufa ba, sudai masoyan ne suka kwana biu.

Karfe Tara na dare gaba daya gidan ya karade da sautin Door bell, hannu Hikmah ta goge jikin apron din jikinta ta nufi kofar, tana budewa gaba daya suna tsaye sunyi matukar gajiya, ran Afeeyya a hade saboda ta tsani yawo, ita Bata fiya shiga cikin mutane ba, amma Anty Hamida ta daukesu Tun safe se dare Yanzun zasu dawo.

Mimi suka gaidar Kamar yadda suke kiran Hikma, Tana ta musu ban gajiya suka shigo ciki sannan suka baje cikin kujerun parlon, fitowa Yaya Kamar yadda suke kiran Maina Yayi daga bedroom din Mimi. Gefen Hamida ya zauna, Yaran suka gaisheshi, cikeda kulawa Ya amsa sannan ya dubi Hamida yace

"Ya hanya? "

Kanta ta Dan kwantar Kan kafadarshi tace

"Tiring, ga Afeeyya nata fushi"

Dariya yayi daidai zaman Mimi gefen Afeeyya yace

"Kin gajiyar da ita ai dole"

Take Afeeyya tayi tace

"Mimi abincin kin gama"

Kanta ta gyada, sannan suka mike dukkansu suka isa dining din, Tuwon shinkafa miyar egusi, shredded beef, se white rice hade da stew da salad. Se strawberry monk. Duk sunfi farin ciki da ganin Tuwon musamman Hamida fadi take

HIKMAH Where stories live. Discover now