4⃣0⃣

2.5K 278 26
                                    


*MAIDUGURI*

Hafsa na zaune parlon Mom Tana shan Tea dukda zafin da ake amma ta maidashi routine, a cewarta gwara ta dinga shan hot Tea after kowanne meal ko ta samu tadan rage kibar da takeyi. Kuma a zahiri ba wata kibar Tashin hankali bace, kawai dai kana kallonta Kasan babu alamar wahala Ko Tashin hankali. Salima ce ta shigo hannunta rikeda waya Se bubbude nostrils take saboda yadda parlon yake kamshin abincin da Hafsa ta gama ci, Kamar Ance ta juya side din dining yake Abinci ne cikin warmers an cika table din dashi, cikin sauri Tayi wajen amma kafin ta kai tuntuni Hafsa ta rigata, ture ta ta shiga yi tana fadin

"Meye Haka wai ke Salima? "

Kai Salima ta dafe dawowata kenan daga Lagos, wata iriyar Yunwa takeji Kamar ana kwakular Hanjin cikinta, amma wannan wicked witch din bazata barta tayi tasting ba. Marairaicewa tayi tana fadin

"Haba In-law plate daya kawai wallahi Yunwa nakeji"

"Zancen banza kenan, kije main kitchen Anyi Abinci kici"

Bata rai Salima tayi tace

"Yanzun Inlaw bazaki bani ba, ko Yaya Aminu kika dafawa"

Kai Hafsa ta girgiza ta aje cup din hannunta tace

"Ba nashi bane ba, Kinsan ki hakura kawai"

Tsaki Salima tayi ta Bangaje Hafsa ta bude warmer daya seda yawunta ya kusan zuba cikin gurin. Daman tafi Hafsa kiba gashi sun girma amma wannan childish play din basu daina ba Har lokacin. Hafsa kanta ta girgiza tace

"Allah Ya isa"

Nafisa da Umaima dake parlon suka kwashe da dariya, Mom tace

"Allah Ya isa dai ta rago ce"

Salima na gama diba ta nufi dakin Hafsa Tana fadin

"In-law taho gist dey"

Ai da wurwuri suka fada kurya suna kulle kullensu Kamar yadda suka saba. Suna idar da Sallar Maghrib Hafsa na kan sallayar da tayi sallah tana lazumi, Salima na kan stool din dressing mirror tana instagramming ta hangame Baki tace

"Inlaw zo kiga wani Tea Party, wani yaro ya auri mata biyu Rana daya."

Kafin Hafsa ta karba wayar taji ihun Nasiba yarinyar Ammar tana ihun

"Yaya Maina oyoyo!"

Da sauri Hafsa ta Mike tayi waje yayinda Salima ta sake baki Tana tunani, a ranta ta Ayyana Dama abincin Maina ne Hafsa ke hanata dauka, no wonder! Murmushi tayi tana ayyana soyayyar da Hafsa kewa Maina. Fita Tayi sukai karo dasu suna shigowa. Daga kofar bedroom din ta tsura mishi idanu tana ganin yadda yaron nata ke Kara girma, shekaru suna Hawa kanshi, a ranta ta ayyana inama yana da aure he would have been completely a man. Hannunta taji ya riko fuskarshi a sake yace

"Ammiey ta, surprise right? "

Bayanshi ta buga tace

"Really, banyi tunanin dawowarka ba, no wonder waccan wicked witch din keta aiki Tun safe "

Dariya yayi dan yasan dawa take. Zama yayi gefen Mom tareda kwantar da kafadarshi yace

"Mom yimin massage"

Ture kanshi Tayi tace

"Uwarka Hafsa ita zata maka massage, kaga da kayi aure basai kayi requesting massage ba. Da kanta za tayi maka"

Mikewa yayi yana dariya yace

"Ma, lemme take a shower, Nazo naci tasty dishes dinki"

Kanta ta gyada ya fice, seda ya leka Dada, Ummiey da Anty Yana sannan ya wuce yayi wankan.

HIKMAH Where stories live. Discover now