2⃣5⃣

2.1K 279 19
                                    

*People of Maman Mamaa novel, take this page*

A gaba dayan rayuwarmu mukan dauka the only heart break da muke samu shi ne akan soyayya. A cikin rayuwa ta na fahimci, ba haka bane. Akwai abinda yafi wannan bacin rai.

Cikin nasara muka kammalla NECO na zama graduate Kamar yadda nake mafarki kullum. Sede wani hanzari ba gudu ba. Ashe ko JAMB ban ci ba, balle naje ABU dana kwallafa rai a kai, Babu Wanda ya sanar dani, don tuni sun sake result din amma Baa fada min ba. Se ranar da muka gama school sannan Baffa ya fada min. Nasha kuka Kamar raina zai fita. Ina ganin tamkar an nesanta ni ne da wani abu da zai faru dani a rayuwata.

A Haka a wannan halin aka Fara bikin su Hamma. Dukda bawai ina wani jin dadi bane sosae a lokacin amma na ji dadin bikin, ko bikinsu Anty Fadila albarka. Tamkar wannan ne karo na farko da Mama zata aurar da Ya'ya, mutane sosae. Ranar asabar aka daura musu aure su hudu. Tunda aka daura auren dake da yamma ne kowa ya Fara shirin dinner, amma abinka da mata bamu muka gama shiri ba se bayan Sallar ishai. Lokacin Aneeysa ta shigo Dan kira na, Tayi kyau na karshe. Wani material Baki da adon golden akai mata gown dashi. Tayi kyau na karshe abinka da farar mace, gani nayi tayi turus tana wurga min harara, dauke kaina nayi Ina kokarin daura igiyar Takalmi na, Wanda yake flat sandals ne silver. Dan dukkan takalmana flat ne saboda yanayin halittar kafar, ganin nayi mata banza yasa ta matso ta zauna gefena tace

"Haba Hikmah, saboda abinda Hamma Mus'ab yayi miki jiya, shi ne baza kije dinner ba? "

Kaina na dago lokacinda na gama fixing Takalmin kafata, kafadar ta na dafa, fuskata dauke da Murmushi nace

"Kinyi kyau, Hamma Mus'ab yayi saa! "

Turen hannuna tayi tace

"Wai me yasa kike Haka ne Hikmah? Yanzun wa kikeso yaje miki"

"Ni nace Bazan Je ba? I didnt"

"To gashi Kinsa, wani kayan daban"

Lumshe idona nayi nace

"Aneey, Kinsan Najaatu yau dinner dinta, banyi attending kowanne event ba. Babu dadi kinga"

Batace min komai ba ta fice, ranta a mugun bace. Kaina na rausayar kawai na Mike na fito. Nazo parlor Naga an zagaye ta ana tambayarta abinda yasa take kuka. Ni dariya ma ta bani da mamaki, can dakin Mama na taddo ta nace

"Mama zan tafi"

Kafin ta bani amsa Sega Maman Aiman ta shigo, Tana ganina tace

"Me yasa bazakije dinner Aneeysa ba, gata can se kuka take. Na zata jiya kin hakura akan abinda Mus'ab yayi miki, kuma dama sako da sako ai ya gaji Haka. "

Dan Murmushi nayi nace mata

"Allah Mummy wannan ya wuce, best friend Dita akewa biki Zanje, lekawa zanyi na koma na Aneeysa din"

Kanta ta gyada tace

"OK, bata fahimta bane, yi maza kije na Kira Aiman Ya kaiki, se ya jira ki gama sannan ku koma can din. "

Kaina na gyada, na fahimci takun Mummy dole de takeson salkafa min danta. Tunda suka zo daga London, dukkan wani motsina a idonta, Dan Ko fadan da mukai da hamma Mus'ab, bayan ta fattatake shi seda tayi min fada, me yasa na kula abokinshi, bayan ga manyan Yara masu sona, me zanyi da wannan kazaman abokan Mus'ab. Ni dai Bance komai ba Dan na fahimci danta take yiwa campaign ba kowa ba.

Tare muka fita da Aiman, shi Bashida surutu, if I guess right babanshi ya biyo, Dan Mummy tana iya magana ita daya saboda azabar surutu. Unlike Aiman tunda muka gaisa bai Kara cemin komai ba, seda mukai tafiya sosae sannan yace min

"Naji Ance you didn't make your JAMB"

Kaina na gyada mishi Bance komai ba, shima Se yayi Shiru kafin tamkar an tsikare shi yace

HIKMAH Where stories live. Discover now