1⃣7⃣

2.1K 269 8
                                    

*Have you read Maimoon? A'isha Humaira? Have you been waiting for another tantalizing and fascinating novel from MamanMaimoon .....Mashaaa Allah don't panic Diyam has been posted, don't miss out dearies*

Tsabar gajiyar dana Tarawa kaina koda asuba kasa tashi nayi sallah, inda Allah Ya taimaka ina period da idan na tashi I won't forgive myself, saboda duk duniya babu abinda na dauka da muhimmanci Kamar sallah, I hate it idan nayi delaying sallah Ko Yaya ne, shiyasa nake mamakin yadda musulmi zai tashi kuma yanada tsarki amma yaki tashi Yayi sallah, rabuwar tayi yawa saboda munsan cewar sallah ita ce shugabar ayyuka.

Har Karfe goma sha daya ina kwance cikin Duvet cover me laushin gaske Kamar fur din mage, dama sanyi ake it's winter bacci dadi. Cikin bacci naji muryar Mama tana fadin

"AI har Yanzun bacci take? "

Cikin fullanci, Aneeysa cousin dinmu ta mayar mata itama cikin fullancin

"Tun dazun takeyi ko Sallar asuba ba tayi ba"

Kusan Uwa tafi kowa sanin halin danta, tasan bana wasa da sallah hakan yasa ta shigo ciki sosae tana bubbuga min gefen gado, a hankali na yi juyi sannan na fito da kaina daga Duvet din ina mitsika idanuna nace

"Mama Yalli jam? "

"Jam kalau Hikma, akace bakiyi sallah ba? "

Kaina na gyada nace

"Period nake fa"

Kanta ta gyada sannan tace

"To tashi kiyi wanka, ki gyara jikinki an hada breakfast din gidan Hammanki"

Kaina na gyada nace

"Inshaaa Allah zan fito"

Tana fita na Mike Ina zabgawa Aneeysa harara nace

"Shi ne kika ce Banyi sallah ba"

Harara ta wurgo min itama tace

"Kinyi? Bakiyi ba ai ba karya na fada ba"

Bama shiri da ita kwatakwata, a haukan ta Hamma Mus'ab take so ganin takun sakar da muke dashi tayi tunanin may be zai ce yana sona shiyasa Bama ga maciji da ita. Wani mugun kallo Nayi mata nace

"Dadin abin ni bana skipping Sallah, idan kinga banyi ba period nake"

Ai se ta mike tana huci saboda tasan gaskiya na fada, Nana itama cousin dinmu ce ta mike tareda riko hannunta tana fadin

"Aneeysa Meye Haka wai, Hikma Yaddiko ba wanka tace kiyi ba?....."

"Maimaita abinda kika fada,....."

Da sauri Hikma ta katse ta da fadin

"Baki bukatar hakan Dan Kinji me nace, ni bana skipping sallah sede period"

Wani wancakalarwa tayiwa Nana Har seda ta fada gadon da na tashi a Kaina tayo Kaina Tana zage zage, yadda ta taho I thought dukana zatayi shiyasa na tsaya still inason ganin gudun ruwanta. Ganin ta tsaya Nesa Dani yasa nayi Murmushi kawai na wuce toilet, Ina tura kofar naji tace

"Da baasan asalin balbela ba se tace daga Misra take"

Wani bugu naji a kirjina amma Se ban fito ba Wanda nima bansan dalilin hakan ba. Aminu Hafsa ya dinga ringing cikin kunnuwana, a Haka na fito na samu babu kowa a dakin, a tsanake na shirya cikin wata coffee abaya Anyi adonta da stones masu tsananin haske, milk veil na yafa sannan na fito, Inata gaida mutane Har na dauki abincin dake cikin basket na nufi waje Se nayi wani tunanin hakan yasa na karasa parking lot na bawa driver nace ya Kai ni kuma na juya gida, ina shigowa nayi karo da Zaki da Aneeysa, ta wani bata fuska tana ta shagwaba Kamar zata narke, cikin sauri na rufe fuakata da veil din don Naga basu lura Dani ba, kafin ya tsinka ni cikin mutane. Dakin Mama na iske ta itada sisters dinta suna ta shirin tafiya gidajensu, Amarya ta tashi zaman me zaayi?

HIKMAH Where stories live. Discover now