4⃣6⃣

2.4K 280 22
                                    


Tunda naga sun gama komai zasu tafi na kankame Mama Ina kuka, gaba daya ji nake tamkar an daura min wani Babban nauyi a kaina, tunda naji kowa yana cemin HIKMAH kiyi hakuri, to nasan tabbas aure ba karamin Abu bane. Haka ina kallo gaba daya suka tafi ko Nafisar Baa barmin ba. Da gudu na koma daki na fada gado na saki wani irin kuka, Ni bansan me yasa nake kukan ba amma na kasa lallashin kaina. A hankali naji numfashina pattern dinsa ya Fara canjawa, hakan yasa na mike na zaune, cikin raina na Fara bawa kaina hakuri, tareda tunawa kaina, Ni kadai ce fa, babu wani Dazai kawo min dauki gwara na daina kukan. A hankali shima ya dauke dif, se Ajiyar zuciya da nake ta yi.

Nafi awa daya a zaune, kafin na mike na yaye lafayar da aka Nada min, na tafi gaban dressing mirror, fuskata na kalla, Haba se kawai na kwashe da dariya, kwaliyyar da Nafisa ta yimin, gaba daya ta jagule, Dama da kyar na yadda akai min saboda nasan chances inyi kuka, 95% ne to gashi kuwa. Kara kallon kaina nayi a take ranar da aka kai Anty Fadila ta fado min, yadda tayi kuka make up dinta ya bata mata fuska, nayi ta dariya. Kawai se nayi Murmushi na wuce zuwa kofar da nafi tunanin ta bayi ce. Face wash nasa na wanke fuskata tsaf, nayi alwala saboda daf ake da ishai. Sannan na fito na dan shafa powder, na maida lafayar da naxo da ita. Kafin na zauna kiran Sallar yasa na daidaita kaina nayi sallah Harda shafa'i amma banyi wutiri ba. Ban jima da idarwa ba naji shigowar shi, da farko na tsorata Dan Banji motsi ba se turo kofa kawai naji, a firgice na juya, na ganshi a tsaye yaci wani soft yadi fari tas, Babbar riga. Yayi kyau sosae. Idanuna suka cicikko da kwalla, a hankali suka Fara zuba saman kuncina, shigowa yayi sosae yana girgiza min kai yace

"Sorry Baby, ni ne na barki ke kadai ko? "

Kaina na gyada ina Hararashi, ban ankare ba naji ya rungumeni gaba daya, tareda miko min hannunshi daidai saitin bakina yace

"Oya, Tofo a rama"

I couldn't resist, seda nayi dariya sannan na kwanbala mishi yawu a tafin hannun, sakina yayi ya kalla hannun sannan ya kalleni yace

"Tab, Baby a hannuna? Kin taro match!"

Inata dariya Naga ya yiyo kaina da hannun alamun zai goga min, kofar na bude fice a guje ina fadin

"Zan fadawa Mami fa "

Kawai gani na nayi tsakiyar Parlor, ga maza a zazzaune, Kai naji kunya kkĺĺk]lol*gJr Jr NHL da sosae, it escaped my mind ranar farko Ango da Abokanshi yake zuwa. Kamar ruwa ya cinye ni hakan na tsaya, na kasa motsi, su kuma se tsokanata suke Wai Haka nake son Abokinsu dama. Ina nan tsaye se gashi ya fito yana dariya da dukkan alamu hannunshi ya wanko, Dan naga ruwa a gaban malumalin dinshi. Tunda ya shigo suke mishi tsiya, Babu Wanda ya kula seda yazo gefena, ya Dan riko hannuna yace

"Zauna, Karki kulasu"

Zama nayi gefenshi sannan sukai mana addua sosae, da abinda ke fadar min gaba wato muyi hakuri. Daga nan suka gabatar da kansu sannan suka tafi.

Aure abune dake canja maka rayuwarka entirely. Idan kana cewa kai bazakiyi kaza ba, ba kya son kaza to bata kama Ki ba. Maza sunada wani Hali na wannan abin nawa ne, I've every right over it, se kiga Wasu abubuwan da gayya akeyinsu. Nafi tunanin shiyasa ake cewa muyi hakuri.

Yana dawowa daga rakiyar Abokanshi, ina nan zaune inda ya barni, nayi zurfi sosae cikin tunani, Inata ayyana yadda zaayi wannan zaman, abinda na sani akanshi kalilan ne Haka zalika shima. Zama yayi gefena yace

"Tunani da yawa is Bad, anan gurin ke kadai kike da iko da ita. So zamanmu Inshaaa Allah zan zame miki adali tunda ni ne shugaba, zanyi miki dukkan abinda ya dace gwargwadon iyawata, zan sauke nauyin da Allah Ya daura min, idan da Hali I'll go extra miles. Zamannan bazai tafi daidai ba seda Hadin Kanki, Abu daya zan rokeki, Dan Allah Hikmah kada Ki boye min zuciyarki, open up to me, hakan Zansan yadda nakeyi, amma idan kika rufeni, I might think wannan abin is right bayan kuma ke cutarki ne. Kinsan aure a ganina abu uku ne, building blocks dinsa, Trust, Communication and perseverance. Idan muka rike wannan ina ganin se munfi Wanda suka shekara dari suna soyayya. "

Bance komai ba amma naji shi, komai ya shiga Kaina, kuma alkawari na dauka Inshaaa Allah komai zai tafi daidai. Hannunshi ya bani na kama se daki, mukai sallah, mukaci Nama. Gani ga Nama babu sassauci, text ne ya shigo wayata, dake wayar na gefenshi, shi ya miko min, Nanah ce

_Zuwa Ynzun nasan an kawo kaza, kamar yadda kika roka, na sako miki yajin garlic, jikin bedside drawer, akwai pain killers hade da box of tissue, se pepper soup a kitchen. Thank me later!_

Kawai se na saki dariya na mike tsaye, bina yayi da kallo har na dakko yajin, bai cemin komai ba seda na Fara dangwalawa sannan yace

"Tuna miki akai"

Murmushi nayi na bashi text din ya karanta. Kanshi Ya shafa yace

"Muna godiya, tunda Kinada pain killers tashi na baki gajiya"

Ture Naman nayi nace

"Na koshi"

Dariya yayi yace

"Ci abinki Babyta"

Daga Haka ya shige toilet, gaba daya se naji tsoronshi nake amma ya zanyi duk daga baya ne wannan. Tare muka kwanta bayan Munyi demacating gadon saboda Tsoro. Yana ta dariya yace

"Kiyi kwanciyarki, ni aiki zanyi na 30mins"

Cikin jin dadi na haye gadon kafin mintina shida bacci me nauyin gaske ya daukeni saboda gajiyar dana kwasa. Bansan lokacinda yazo Ya kwanta ba, amma ya jima yana kallona imagining nayi ruining plan dinsa, saboda yadda ya sawa ranshi duk ranar da yayi aure, ranar zaa yita ta Kare, hakanne kadai zaisa yaji completely ni din tashi ce. Amma yadda nake baccinan bazai iya tashi na ba, balle ya rigada yace bazai min komai ba, idan Yayi ya saba alkawarin.

Kwanciya yayi ya rungumeni, nima bansani ba na rungume shi Nima. A Haka mukai bacci so peaceful and so lovely. Bayan Munyi Sallar asuba, Har seda gari ya fara haske Ya bani wayata yace

"Kira duk Wanda ya kamata, kiyi musu bangajiya"

Yana Gama fada ya fita, su Mama na Fara kira, mun danyi hira ta Kara min nasiha sosae sannan mukai sallama ina sharar kwalla. Sannan na kira Mami,

"Hikmata kin tashi lafiya"

"Lafiya lau Mamita, ya gajiya? "

Nan ta tambayeni Maina nace Yanzun yaje parlor, nan ta farfada min abubuwan Wanda duk tuni ne sannan mukai sallama. Wasawasa na kira mutane da yawa, wajen mintina talatin da fitar shi, hakan yasa na mike nabi bayanshi, se na tarar yana waya a parlor, kitchen na wuce, Inata kallon yadda ya hadu kamar a mafarki, na taba wannan na Danna wancan, na bude can na rufe Haka nayi tayi. Se can na daura Tea, ina tunanin me zan dafa na breakfast, naji gyaran muryarshi. Kashe Gas din yayi yace

"Zo muje bacci bai isheki ba. "

Banyi musu ba Dan nasan Inada taurin Kai amma banida musu ko kadan, ranar da Mami ta Kara jaddadda min Aljannata tana karkashin kafarshi, da yazo nace zai daga min. A take ya daga ta yace

"Baby na daga miki, shiga kawai zakiyi as far as kin bani Hadin Kai. Banida damuwa. "

Har daki mukaje, gadon yana nan yadda muka barshi, seda nayi stretching sheets din, na gyara sannan na kwanta, shima kwanciya yayi, nayi tunanin bacci Zamui amma se naga an fara wani abu daban. God nayi kuka, nayi cizo, nayi yakushi, majina amma ina Maina bai saurara ba seda ya maidani tashi, seda ya tabbatar na zama mallakinshi sannan ya dinga rarrashina, I was pissed off amma a Haka bacci ya daukeni.

Short? Manage it plz!

_Jakadiyar kainuwa_

HIKMAH Where stories live. Discover now