1⃣8⃣

2.2K 256 11
                                    







A hankali cikin nutsuwa ya zare surgical gloves din hannunshi, file din da aka aje mishi akan table din dake da gaban gadon patient din ya bude Yana karanta previous review da akaiwa patient din, yana kammalawa ya gyara zaman glasses din idanunshi tareda duban nurse din dake gefenshi yace

"Sister Kamar babu progress akan patient dinnan, akwai damuwa ne? "

Dr. Maina Ya tambaya yana maida dukkan hankalinshi akan bayanin da sister din take mishi, kanshi Ya girgiza cikeda takaicin halin da rayuwar aure take a wannan zamanin, yadda maza gaba daya suke neglecting duties dinsu a matsayin shuwagabbani abinda kawai suka sani bada order da possession a dole sune jagorori, Ajiyar zuciya me nauyi ya saki tareda yin rubuce rubuce a file din sannan ya zare glasses din idanunshi yace

"Sister Ina ganin ya kamata mu hada su da social welfare na asibiti Ko? "

Kanta ta gyada tace

"Already sun shigo zasui intervening, so Bakada matsala da wannan"

Murmushi yayi a nutse yace

"Thank you sister, Inada wani aikin kuma? "

Kai ta girgiza tace

"Se wannan matar me Myocardial infarction"

Kanshi Ya shafa alamar gajiya yace

"Muje"

Tana gaba yana biye da ita a bayanshi Har sukaje Kan patient din wadda take zaune abin tausayi amma kana kallonsu kaga suna Afuwar rayuwa, daga Haka ya dubata ya kara rubuta sababbin drugs sannan ya fice zuwa motarshi, yana shiga ya tayar da motar se massallaci. Seda ya idar da sallah sannan ya koma gidan da yake zaune cikin jerin gidajen dake staff quarters na asibitin Malam Aminu Kano dake cikin kundila. Bayan Ya gama course dinshi a Germany na Heart surgeon akai posting dinshi nan AKTH, Haka kurum Kano bata daya daga cikin garin da yake son zama saboda cukowar jamaa, mutum ne me akida ta baya son hayaniya Ko cunkuso shiyasa yaso ayi posting dinshi Jigawa, Yobe Ko Gombe to hakan bai samu ba, dole ayi using available resources.

Wanka ya Fara yi kasancewar ana matsanancin zafi a garin na Kano, seda ya watsa ruwa sannan ya shirya cikin Armless top Ash, da milk din short, gefen katuwar katifar dake tsakar bedroom din nashi Ya zauna, komai a cukwikuye yake, Hatta bed sheet din don baiyi stretching gadon ba bayan Ya tashi a barci, Haka ya dawo ya samu tunda waye zai gyara masa, shi yanada tsafta ta jiki, ko kallonshi kayi sau daya se ka fahimci hakan amma Kamar Sauran maza haka yake, dakin is always untidy and unkempt, Mussaman tunda yayi MBBS a Nigeria ya koma tamkar Bako a kasar, yau yana can gobe yana can kuma duk kasar da yaje idan ba Karatu bane to yanada personal me mishi gyaran gida, to amma a kanon nan har yayi wata guda bai samu ba saboda rashin takaimaiman me samo mishi mutum na gari.

Abincin da ya shigo dashi cikin Leda ya bude, farar shikafa ce da miya, gefe cikin wata transparent roba salad ne Wanda aka hada da macaroni, mayonnaise, sardine, parsley, Irish se ganyen cabbage. Cikin plate ya zuba abincin sannan ya bude wata foil paper gefenshi Nama ne na karamar dabba an gasa shi harda romo. Cikin nutsuwa ya zauna yana ci seda yayi Kat sannan ya nade komai ya kora da pineapple juice na Chi exotic.

Lumshe idonshi Yayi a ranshi yana jin ya kamata ya samu yayi aure, to amma tambayar anan Wacece zai aura? Bayan zuciyarshi mutum daya take so take kuma muradi banda Lulu , a iya rayuwarshi Kai shi gane yake sonta dashi aka hada dukkan Wasu strips na purkinje fibres dinshi, dalilin da ya tsiri Karatu me tsawon lokaci kenan saboda ya dauke mishi hankalinshi, Dan Ko kusa medicine is never what he wanted, but Yasan Karatu ne Wanda Baka isa ka kai karshenshi ba, the field is so wide da sede ka lasa ka hakura, amma badai kaga karshenshi ba.

HIKMAH Where stories live. Discover now