🔟

2.4K 258 7
                                    

Wasa wasa seda mukai kaman sati kullum Se munkai wannan letter da bansan ta mecece ba, Haka zalika bansan dalilin kaiwar ba. Ranar ta kama Alhamis babu islamiyya ina gida Mama ta sani a gaba seda ta tsefe min cukurkudadden Kaina, seda ta gama muka tafi toilet da kanta ta wanke min Inata bata rai da raki amma Haka ta wanke shi tas, tasa towel ta daure min sannan ta hada ruwa cikin bucket me dumi tace

"Maza kiyi wanka Kinji?"

Kaina na gyada mata, Itakuma ta fice daga toilet Din Baki daya, gaba daya se naji dadi da wata iska Tana shiga Kan. Sosae nayi wankan sannan na fito, a zaune na sameta Tana waya

"Eh to idan Babansu ya dawo se ya fada mata"

Banji abinda aka fada mata ba se naji tace

"A'a Fadila bazata bamu matsala ba, amma Naso tuntuni ace tasan da Maganar ba kawai ace se Yanzun ba "

Can ta kuma fadin

"Allah dai ya bamu nasara kawai, Bari na sallami Hikmah. Se Munyi magana a gaida Yara. "

Aje wayar tayi ta dubeni, ina tsaye na kafeta da ido, Kalloma tayi tace

"Tsayuwar me kikeyi ne, zo ki zauna"

Gefenta na zauna na shafa Mai sannan na dawo kasa na zauna Ta gyara min Kan sannan ta dakko min kaya, wani lace ne fari da blue na saka sannan na nufi dakin da Anty Fadila take, ina zuwa Naga Tasha kwaliyya, ta saka lace sak irin na jikina, zama nayi ina fadin

"Anty Fadila Kinyi kyau"

Murmushi tayi tace

"Nagode Hikma, Hamma Mussadiq zan raka unguwa"

Nima Murmushi nayi mata nace

"Iyeee Kinyi kyau kuwa, se Kun dawo"

Kanta ta gyada Tana Kara bada turare a jikinta Wanda Har ya Fara damuna, itakam yar gayu ce, gata kamanninsu daya dasu Hamma Mussadiq din shiyasa idan kazo gidanmu ni dince dai Odd a ciki, da babanta da Baffa Uwa daya uba daya suke immediate brothers ne.

Tare muka fito se Naga taja hannuna mun koma sannan ta ciro wata paper Kamar kullum tace

"Ki kaiwa Abdallah"

Babu musu na amsa, muka fito Har main parlor inda Hamma Mussadiq ke tsaye fuskarshi a dinke babu ko digon  annuri, hakan kuwa ba halinshi bane, mutum ne very jovial and nice. Nima se na shiga taitayina, na samu cushion na zauna ina wasa da jelar gashina da ta fito, Kamar daga sama naji yace

"Tashi ki dakko hijab kizo muje kema"

Dagowa nayi nace

"Ni? "

Na fada Ina nuna kaina, harara ya wurgo min yace

"A'a ni"

Kallon Anty Fadila nayi naga Tana kyafta min ido Don itama tunda muka Kalli fuskarshi ta shiga hankalinta don naturally ita dashi basu fiye shiri ba, su basu fada kuma ba wani dasawa suke ba. Daki na nufa na dakko mayafin kayan amma kafin na karasa mukai karo da Mama Tana fitowa daga daki hannunta da wata Leda, Kallona tayi tace

"Ina zakije na ganki da hijab? "

"Hamma Mussadiq ne yace na dakko zamu fita"

Ba tace min komai ba ta nufo parlour nan Nima na biyo ta, Tana zuwa tace dashi

"Tsayuwar me kuke Har Yanzun baku tafi ba?"

Ranshi a bace yace

"Hikmah muke jira"

Hararar shi tayi sannan tace

"Musaddiq ka fita a idanuna kaji ko? Bana son taurin Kai. Tohm"

Baice komi ba yayi gaba abinshi, itama Anty Fadila da sauri ta take masa baya, seda mukaji fitarsu a Mota sannan Mama tace dani

HIKMAH Where stories live. Discover now