1⃣5⃣

2.2K 254 10
                                    



Bude kofar bedroom din da akai yasa nayi saurin maida board din na aje, Kamar marar gaskiya Haka na juyo, Mama ce ta shigo fuskarta blank babu wani expression da zan iya karanta, tsira min idanu tayi tana kallona Har ta karaso sannan tace

"Menene? "

Da sauri na girgiza mata Kai na ba tareda na iya furta Kalma Ko daya ba, nayi waje. Shiru tayi na lokaci kafin ta maida trolleyn ta rufe don bashi take nufi ba, kuma tunaninta bai taba kawo mata zanga wannan board ba. Ina zuwa dakina na zauna gefen gado tareda zabga tagumi, gaba daya kaina a cunkushe yake I dunno what to think of, sede tambaya daya ce su waye Hafsa da Aminu? Mama da Baffa ba iyayena bane?

Cikin sauri zuciyata ta kwabe ni akan abinda nake tunani, saboda tunanin hakan seda naji kunya ta lullubeni, babu wani gap da aka Bari da zai nuna cewar su ba iyayena bane, Babu wani abu, bayan hakan jikin board Zainab is written amma Meye Lulu? Jin Kaina na barazanar tarwatsewa Se na sulale na kwanta a gurin gaba daya hankalina ya tafi akan abinda na karanta.

Haka muka cigaba da Hada lefen Anty Fadila, kullum Se mun fita wani lokacin Har dashi kanshi angon. Ana saura kwanaki uku a fara biki na shirya zan tafi islamiyya, na gama saka uniform dina na fito, Anty Fadila tana zaune an kawo gowns dinta da Sauran kayan fitar biki daga gurin dinki, once na ganta Tana ta magana cikeda jin dadi don tunda aka Fara shirin bikin ta dinke bakinta especially idan Mama na gurin ,gaba daya surukuta take da ita.

"Na zata se an gama biki zaki koma makaranta"

Bude baki nayi nace

"Kada Mama ta jiki tace ni nace ki fada. AI daga yau Se bayan biki"

Dan Murmushi tayi tace

"Allah Ya kiyaye "

"Amin Amin "

Na amsa mata tareda nufar kitchen na yiwa Mama sallama. Ina fitowa kofar gate Naga zaki shida abokinshi suna hira, tunda na fito abokin wani mummuna dashi ya kafe ni da ido, munin shi bai Kara fitowa seda ya hada zama da Mus'ab epitome of handsomeness, Raina a hade na iso inda suke na dan rankwaba na gaishesu, abokin har da hardewar baki gurin fadin

"Lafiya.... Lafiya... Lau... Yanmata "

Ko kallon Arziki zaki baimin ba, na wuce Abuna ina jin yana dannawa abokinshi zagi Wai

"Kai amma banza ne wallahi, wannan gurguwar ita Kake yiwa wannan kallon Kamar kaga wata mace..... "

Sauri na kara saboda bansan abinda zai fada next ba, saboda bana son zuciyata ta tsaneshi amma Naga alamar zata kaimu ga Haka, don har na Fara jin wani irin yanayi inhar na ganshi, bana son ganin shi idan kuma muka hadu to gabana Se ya fadi, se naji gaba daya raina ya baci.

Nayi gaba sosae Kamar daga sama naji ance

"Beautiful Zainab"

Ba kowa yasan sunana ba Zainab balle a kirani harda beauty, hakan yasa na kara sauri ina kokarin shan kwana Naga mutum a gabana, seda na tsorata Har na ja da baya se Naga yana Murmushi yace

"Matsoraciya kawai, makaranta zaki je? "

Da sauri na gyada Kaina Ko leben bakina ban bude ba saboda tsoron kar wani ya ganmu tare da Abdallah, ganin yadda nake ta waigewaige yasa yayi dariya yace

"Jeki yi tafiyarki, Allah Ya bada saa"

"Amin"

Na amsa sannan na gebare shi na wuce. Har na shiga class gabana bai daina faduwa ba, duk Tsoro nakeji. Ina zama Malam ya shigo mukai tilawa sannan ya Fara karbar hadda, ni ce ta ukun karshe Don haka ina bada Haddar na ciro invitation card nasu Hamma Mussadiq na bashi, seda ya karanta sannan yace

HIKMAH Where stories live. Discover now