*It was amazing and loving reading all your comments, I saw, I read and I'm impressed. Know that I'm happy. Yours Truly Antyn Hikmah*
Wannan furucin nashi Ya girgiza min duniyata da abinda ke cikinta. Bansan yadda zan kwatanta muku yadda sakonshi ya iso gareni ba, one thing shi ne daga ranar komai nawa Ya canza. Nasan da yawa zakuce Hamma bai kyauta ba, zakuce he messed up! Yeah Hakane amma abu daya da yasa ya fada min hakan, saboda ganin Bashida wata mafita data rage mishi banda hakan, yana ganin zai rasa ni matsawar bai fada min ba.
Kallonshi nayi Kamar yadda yake kallona, idanunshi Sunyi tas sede akwai Dana sani a cikinsu, Wanda I'm sure Dan Ya fada min abinda Baffa da Mama sukai ta harkilon rufe min ne, amma aikin gama ya gama.
"Hamma zan fita"
Na fada can Kasan makoshina, idanuna Sunyi jawur Ko ban Kalli madubi ba, nasan da hakan Dan har wani yaji yaji nakeji. Bai Musa min ba ya bude min na fito, ina jinshi yana fadin
"Allah Ya tashe mu lafiya"
Ko amsa ban bashi ba na wuce cikin gida. A hankali na murda kofar parlor, cikin zuciyata addua nake Allah yasa Mama da Baffa basu parlon. Amma ina sallama wadda a hankali ta fita saboda yadda muryar take a shake, babu wani kuzari Haka na shiga na sameshi suna zaune da alamu zamansu kenan.
"Baffa, hannu iwar tauki, Mama miwarti"
Na fada Ina daidaita yanayina, amma banyi nasara ba, Mama ta zuba min idanu, yayinda Baffa yace
"Uwata me ya sameki? Kinga idonki kuwa? "
A hankali na lumshe idon, Karo na farko kwakwalwar Kaina tace Basu suka haifeki ba, idanuna na bude ina karkaro murmushin da iyakar kokarina amma fatar baki kawai ya tsaya nace.
"Abu ya fada min a ido. Mama zan kwanta kowa na gaisheki"
Ina fadar Haka na juya da sauri, saboda Ina tsoron tambayoyi, bana son a tambayeni Dan banida amsar basu, na nufi dakina inajin Baffa na cewa Mama kada ta bini ta barni tukun. Nikam Ina shiga dakina, na tura kofar na jingina da ita ina jin yadda zuciyata ke bugawa Kamar zata fasa kirjina ta fito, ga numfashina da kyar nake iya janyo shi. There and then nasan attack zan samu, hakan yasa nayi saurin saka lock a kofar, drawer naje na ciro inhaler babu jira na dinga shakawa, hawaye ya wanke fuskata tamkar zanyi hauka haka na dinga ji a wannan lokacin, saboda naki na nutsu shiyasa asthma taki sauka Se karuwa abin yake, ganin da gaske idan na cigaba da zama to tabbas lungs dina collapsing zasui saboda da kyar nake fuzgar iska Ko kuma na mutu ban su waye suka haifeni ba, bansan ko ni Shegiya ce ba.
Mikewa nayi ilahirin jikina karkarwa yake na bude kofar na fito parlor, tunkan na karaso naji Salatin Mama daga nan ban kara sanin inda nake ba, Se farkawa nayi naga oxygen a hancina a gadon asibiti.
Hawaye a hankali ya Fara sauka saman kuncina, idanuna na runtse inajin wani abu me tsini yana piercing kirjin, ga Kaina tamkar zai fado haka nakeji. A hankali naji Mama ta kama hannuna tana fadin
"Hikmah kin tashi"
Idanuna na bude, hakan yasa ta tabbatar da zarginta, hannuna ta sake min ta fita, can Sega ta ta dawo da nurse, tana zuwa ta ciremin oxygen din sannan tace
"Zainab tashi ki zauna"
A hankali na tashi na zauna har lokacin kuka nake, Wanda hawaye ne kawai se wani tukukin takaici da bakin ciki marar misaltuwa da nake ji cikin zuciyata.
"Ya jikin? "
Ta tambaya tana hada allura cikin syringe, kaina na gyada mata Dan Ko bakina bana son budewa. Anan tamin allura wadda ta kusa mintina ashirin tanayi, tana gamawa ta dubeni tace