2⃣4⃣

2.1K 270 13
                                    

Washegari Misalin Karfe takwas na safe, Inata sauri na tafi school saboda Munada early food and nutrition essay exams, kuma ita ce last paper da zamuyi. Da kyar nasha tea saboda nasan daf nake da makara. Ina fitowa parlour, I was super shocked ganin Anty Fadila a zaune, baki a hangame na nufeta Har na manta abinda ya faru the other day. Rungumeta nayi Ina fadin

"Wannan buga sammako Haka?"

Murmushi tayi ta dungure min kai tace

"jiya baki fada min jibi saukar ku ba, Nazo taya Mama aiki"

Gosh! Na dafe Kaina ni Kaina ina tunanin na manta da saukar gaba daya, gaba daya Daren jiya a wasiwasi Ya kare min, Haka kurum nake jin puzzles din dake gabana akwai Wanda is not placed right. Ni nasan mu musulmai ne, Fulani dake zama a kasar Hausa masu riko da aladarsu. I thought for many times it can't be coincidence Hamma Mussadiq yace zai aureni sede idan daya daga cikin mu biyun ba Baffa da Mama suka haifemu ba

"Hikma zaki makara fa, wannan deep tunanin is not good"

Wannan ya dawo Dani hayyacina, kaina na gyada ko Mama ban nema ba na fice Kamar zan tashi sama. Ina zuwa Bus zata tafi, hamdala nayi nabi bus din, ko a ciki banga daya daga cikin yan class Dinmu ba, hakan yasa na samu guri na zauna nayi Shiru Inata tunanin rayuwata, idan har zuciyata ta raya min daya daga cikin ni Ko Hamma Mussadiq ba su Baffa suka haifemu ba, to ni ce ba yarsu ba. Saboda duk wani abu na jini Hamma Mussadiq ya dakko amma ni banida wani abu da zai nuna cewar su iyayena. Gabaki daya se naji hankalina yayi matukar tashi, idanuna na runtse wani Bari na zuciyata yana gasgata baa gidanmu nake ba yayinda wani barin ke kalubalantar hakan.

Ranar exams nayi ta ne kawai, bawai Dan nasan me na rubuta ba, idanuna kadai sun isa su nuna ample of Tashin hankalin da nake ciki. Muna fitowa na nufi gate saboda bana son mu hadu da kowa, Allah Allah nake na fita amma my wish wasn't granted, nayi bumping Najaatu. Dagowa nayi da niyyar bada hakuri Se Naga Najaatu ce, dariya tayi tace

"Nemanki nake tayi"

Tsayuwata na gyara, Ina daidaita nutsuwata nace

"Ya exams? "

"Kin manta Tun jiya nayi tawa, ke zan tambaya wannan ai"

Murmushi nayi nace

"Not bad at all"

Nodding kanta tayi tace tana Jan hannuna

"Aure Zanyi Hikma"

Da mamaki na kalleta dukda ba abin mamaki bane tunda Tun muna jss3 take zancen aure, zama mukai kan Wasu gossip chairs nace

"Zakiyi ko zaayi miki? "

Hannunta ta watsar a iska Tana dariya tace

"All the same Kawata. Bayan Neco da sati biu"

Idanuna na bude sosae har seda ta kauda kanta, saboda tana yawan cemin bata kaunar nayi mata full light da idanuna, Tsoro suke bata. Dariya nayi nace

"Sorry Aminiya, Kinsan week daya da nasu Hamma Mus'ab da Hamma mustapha? "

Kallona tayi tace

"Ba zakizo ba kenan? "

Bakina na rufe ina Dan dariya nace

"ko event daya ne zan leko"

Rungumeni tayi tace

"Kinga mijin, bafullatani kyakyawa? "

Dariya nayi nace

"Haka kika iya, gwada maza. Bari kiga na tafi gida, se next month"

Daga Haka mukai sallama, naji dadi Dan at least damuwar da nake ciki ta ragu sosae.

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, wata Rana zuma, wata Rana madaci. Anyi bikin saukar quranin mu. Anyi shagali sosae. Yan Uwa sun mini kara Kamar Wanda ake biki. Sati biyu daga wannan lokacin muka fara NECO, tareda Aneeysa akai mana registration muke zuwa tare. Bahaushe yace albarkacin kaza, kadangare kan sha ruwan kasko. Kullum Hamma Mus'ab kaimu yake ya dakko mu. Babu fashi kowanne aiki ko yakeyi se ya barshi yazo Ya dauke mu. Babu ruwana da sabgar su, abinda ya dameni shi ne a gabana. Kullum se nayi tunanin su waye suka haifeni, su waye iyayena. Dukda babu alamar nuna akwai yiwuwar su din basu suka haifeni ba amma Haka kurum nake jin akwai breakage along the way. Ban taba budar baki na tambayi wani ko na fadawa wani ba Har Anty Fadila saboda kunya nakeji nauyin hakan nakeji, Ina ganin banyi musu adalci ba.

Ranar alhamis, muna zaune ni da Aneeysa wadda muka fara shiri da ita kwana biyu saboda yadda kullum muke tare, kuma taga bana shiga sabgarta se ta yadda makaman yakinta ta rungumeni. Muna zaune muna solving wani quadratic equation, Mama na serving Baffa Se su Hamma suna danne dannea wayoyinsu. Muna gamawa Aneeysa ta janyo wani bowl Wanda muka zuba popcorn da caramel topping, Munyi akan inhar muka samu answer da steps din daidai zamu ci, idan ba Haka ba kuwa to sede muyi kyautar shi. Hannu ta bani muka tafa sannan muka fara munching dinshi, kowa yana lumshe ido Dan dadi. Idanuna na mayar kan network news din da Baffa yake zaune yana kalla.

Wani mutumi ne a tsaye akan podium, flash yanata haska fuskarshi ga dandazon Yan Jarida sun kawaye shi. Gaba daya na tattara hankalina na mayar kan wani rantsatsan speech dake fita daga bakin mutuminnan, Ya manyanta a kalla zai tasarwa 50 years, idan bai kai ba to kadan ya rage babu, shima saboda yadda na kura masa idanu yasa na fahimci hakan, amma lokaci daya bazaka fadi hakan ba. Dogo ne yanada tsayi, fari tas dashi, kana kallonshi kaga dan gayu Wanda by all means yakeson batar da shekarunsa. Yana sanye da Wani lafiyyayan grey suit, idanunshi cikin farin garegaren medical glasses. Daga yadda yake magana zaka dinga jiyo yadda yake fitarda sautin kowanne word, American accent Yayi aiki Dan Ya fito radau, kana jin maganarshi Kasan America ta Gina Dan Nigeria.

Juyowa nayi na Kalli Baffa dake kurbar tea nace

"Baffa waye wannan? "

I was super curious nasan waye wannan, waye shi. Sau daya na kalleshi amma naji wani abu me girma a tare dashi, ban taba jin wannan yanayin ba, not even on Mama or Baffa. Love at first sight, ba so na soyayya ba irin Wanda nayiwa Abdallah ba, No is just a different feeling da nake dashi da ban taba jin irinshi ba akan kowa, so Wanda yake natural, within a minute Ya gama circulating dukkan sassan jikina.

Baffa ya dubeni yaga yadda na tsura ma mutumin ido yace min

"Last week aka mishi appointment na CBN governor. Mutumin yanada kirki anata yabon shi, da alama Zaiyi aiki. "

kaina na gyada mace

"Baffa Ina son na ganshi"

Duka aka kwashe min da dariya, suna ganin wauta ce kawai, amma bazasu gane me nakeji akan Mutumin ba.

"Ai Uwata, meeting such people is very hard, da kina tweeter Se kiyi following account dinshi."

Da sauri Kamar ina jira naje na dakko wayata aka bude min tweeter account mukai searching  *ABMaina* Ranar Har sha daya ina bincike a profile dinshi. Yawancin trips din da yayi ne ,guraren da yayi Karatu, se official aikin da suke akan gyara CBN da other banks.

Washegari muka fara hada Lefe, kullum se Munje kasuwa, ranar muka dawo a mugun gajiye ana a week to bikin na cewa Mama Bazan kara raka ta ba, ni gajiya nake, kullum na dawo da kyar nake iya tashi Washegari, saboda azaba.

_Jakadiyar kainuwa_

HIKMAH Where stories live. Discover now