2⃣7⃣

2.2K 262 11
                                    


Duk yadda mutum yake daukar Kansa idan yaje SBRS to abin ya wuce nan, idan takamar ka turanci zaka sha mamakin jin American and British accent, idan takamar ka kai guru ne SBRS will turn you to gugguru... Lol... Koda me kazo an fika. Munyi Karatu sosae, Karatu me cikeda kalubale Wanda a times Se Inji tamkar na tattara kayana na gudu gida amma idan na tuna abubuwan dake gabana Se na fasa.

Ranar Friday mun dawo daga lectures din Waves and Vibration, dake jumaa ce babbar Rana, gaba daya Munyi kyau kowaccen mu taci Atamfa. Ammashiekh ta dubi agogon hannunta tace

"Yanzun Zaa Fara huduba, muje massallaci."

Tare duka mukaje mukai sallah, da aka idar mukaje can wajen hostel din maza mukai order Abinci, at least munason mu taba kowanne Abinci na kowanne joint. Seda akai mana packaging muka taho dashi daki mukaci.

Da daddare ni daya na fita, dukkansu suna daki, naje meeting din state, ina dawowa bansan tsautsayi da ya biyo Dani ta C15 ba, na biyo nayi mummunan gani kuwa. Ina dawowa daki na zauna jagwab gadon Ameeyna Ina fadim

"Ku kunsan ta Ina na wuce? "

Firdausi tace

"Ina?"

Nace

"Uhmmmm kiss me sharp sharp! "

Duka suka kwashe da dariya suna fadin

"Su Hikmah Anyi Babban gani, me kika gani? "

Duka na kaiwa kashmy na danyi Tsaki nace

"Allah bansan me mutane ke daukan soyayya ba, wannan ai rubbish ne"

"Sosae ma,"

Mama Sa'ada ta bani amsa, hakan yasa Ammashiekh tace

"Talking about soyayya na tuna me zance. Hikmah Wai ya kuke da Hamma Aiman dinnan, kullum brag dinki bakida saurayi, shi me kukeyi?"

Dan dariya nayi, inason Ammashiekh with that her Sisterly advice nace

"Wallahi babu komai fa."

Amina tayi carat tace

"Kinji ki ko? Malama kowa anan yana da saurayi, meke damunki ne? "

Shiru nayi Ina jin wani iri ,nace

"Only God knows what? Ni Kaina bansan abinda ke faruwa ba, amma one thing for sure is The perfect timing is knew by Allah, if it comes no hesitation no delay. "

Wannan abinda na fada yasa duka sukai Shiru, muka koma hirar latest songs na Maheer zain, dama kashmy ke mana downloading. Ana gama ji muka hada choco pops da madara cikin katon bowl muka sha sannan aka shiga IG na ganin post din Fatigbolady. Muna sonta sosae dukkanmu muke following dinta.

Haka rayuwar mu take kullum daga lectures, Abinci, sallah se hira Se ayi Karatu. Bama zuwa tutorials ni Kaina bansan dalili ba. Ranar muka zauna dukkanmu mukai discussing gaps dinmu Dan an fara test, chemistry practical kuma performance wasn't encouraging. Daga wannan ranar muka dage yau muje tutorial din wannan state din, gobe muje na wancan. A hankali muna picking abubuwa. Da weekends zamuje cafeteria muyi Karatu sannan a koma normal life.

Duk cikinsu kowacce Nada saurayi banda ni kadai, Ammashiekh the love birds kenan, after mintina biyar biyar suke waya itada Munnir, I can swear ban taba ganin soyayya irin tasu ba, they're addicted to each other Kamar me. Amina nata handsome take kiranshi, wannan shi ke tashinmu Sallar asuba, amma akwai side chicks da take dasu. Firdausi kuma wani Khalid ne saurayinta kullum se dare zasu fara waya only God knows when Zaa gama. Mama Sa'ada kawu ne nata though tace he's just a cousin amma kallonta kawai muke. Hajiya kashmy kam Usman ne, Jordan muke kiranshi dashi saboda can yake Karatu. Nikam ni daya ce banda saurayi, idan suna waya sede nayi tsuru Ina kallonsu, a wannan lokacin na Fara jin, I need love, no matter yadda soyayya ta gwaraka Bakada right na cewar bazaka kara ba, I believe love is the spicy of life nasan many will believe me. Soyayya ita ce abarda take wahalar damu and yet kullum ita muke nema, that's love. No one can do without it.

HIKMAH Where stories live. Discover now