*💖RUWAIDAH💖*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne...*👌🏻
~*Free Book Insha Allahu Babu Canjin Ra'ayi*~
'''MALLAKIN'''
👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*Wattpad@RahamaUmmufareesa
*DEDICATED TOO*
MAMAN RA'EES💝Son so domin Allah😍'''🙏🏻🙏🏻🙏🏻ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH GODIYA TA TABBATA GA ALLAH SWT SARKI UBANGIJIN TALIKAI, ALLAH NAGODE MAKA DA KABANI IKON KAMMALA LITTAFIN KAMAL NE DA BANIDA GATA CIKIN ƘOSHIN LAFIYA, DA KUMA KWANCIYAR HANKALI HAR NA DAWO CIKIN SABON BOOK ƊINA ME SUNA RUWAIDAH WANDA SALON DABAN YAKE DA SAURAN BOOK ƊINA, YA ALLAH KASA YANDA NA FARA LAFIYA NA KAMMALASHI LAFIYA,YA ALLAH KA ƘARAMA ANNABI DARAJA AMEEE'''
*~Jinjina da ban girma ga masoyana na asali masu sayan book ɗina, da masu karantawa baku sayaba, duk cikin sone....dubin gaisuwa da fatan Alkhairi zuwa gareku a duk inda kuke a faɗin duniya, shiyasa nazo maku dawani salo na daban👌🏻wannan book ɗin Sadakarwa ne ga masu sanyan book ɗina harma da wanda basu sayaba, ina yinku irin babu adadin nan,👌🏻 nasan ko da yaushe kuna tare dani,kamar yadda nake tare daku😍 kuji daɗin ku ni Real Ladingo ina tare daku zanci gaba da sambado da mazgo maku zafafan book idan Allah ya bani ikon yin hakan, abu ɗaya nake buƙata shine comments ɗinku da sharhi shine zai nuna min kuna yin book ɗin RUWAIDAH👌🏻 nikuma zan wanke maku zukatanku cikin wannan tafiya ta musammamn kudai ku sambado comments👌🏻asha karatu Lafiya Son so Fisabilillah🤝🏻😘😘😘~*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Chapter 1*
Babbar buss ce take sharara gudu tsakiyar dajin, jahar Taraba jama'a sai hirasu suke cikin nishaɗi, wasa da dariya sai labaran dariya suke, wasu kuwa Tv ɗin dake manne da motar suke kallo suna dariya, saboda film ɗin akwai bada nishaɗi.
Wata ƴar matashi ce kyakyawa mai kyan fasali, baƙa na hangota rungume da ƙaton teddy a ƙirjinta, tana sanye da wani haɗadɗan less milk ɗinkin doguwar riga sai hijab shima milk ne dogo har ƙasa, wacce bazata wuce 18 year ba, can tsakiyar kujerun zaune, ta haɗa kai da guiwa rungume da teddy dinta.
Tinda buss ɗin ta ɗauko su daga garin kano har zuwa yanzu da suke dab da shiga Taraba Jalingo, yarinyar babu wanda ta kula a cikin motar, asali ma bata kalli kowaba.
Matar da take kusanta tayi mata maganar duniya saboda kukan da take, bata tankata ba, dole ta rabu da ita.
Ɗan gambo ne ya fasa wata irin dariya yana tafa hannunsa yana cewa.
"Yauwa nawan cimin ubansu karo da maza ba riba." Hakan ne yasa Ruwaidah ta ɗago da kanta, ta zubama Tv dake manne a jikin motar dara-daran kyawawan idanunta masu kamar tanajin bacci, taga yanda ake gabza faɗan, fuska ta ɗan yamutsa fuska tana matsar ƙwalla, lumshe lumsassun idanunta tayi ta haɗe kai da guiwa, ta ƙara manne teddy ɗinta A ƙirjinta.
Masha Allah nace Allah yayi baiwar kyau anan, kana kallon yanayi fatar jikinta kasan gidan hutu ta fito, saboda yanda fatar ta take sheƙi, dan less ɗin jikinta ma kadai zaka kalla kasan ba ƙaramin gida ta fito ba.Karfe 7 pm dai² suka iso cikin babbar tashar da take cikin garin Taraba, anata ƙiran sallar magarib. Saukowa jama'ar motar suka fara ɗaya bayan ɗaya. Se da taga kowa yakusa sauka ta sanyan tattausan hannunta ta ɗauki bottle na Faro, water ta miƙe tsaye, ta ƙara rungume teddy ɗinta cikin ƙirjinta, sai lokacin na ƙare mata kallo, baƙa ce kyakyawa doguwar fuskarta tana ɗauke da dogon hanci mai matuƙar tsini, sai manyan idanunta lumsassu farare tas wanda ƙwayar idanun nata sun bada launin kalar irin na turawa, gasu kamar tanajin bacci, gashin idanunta gazar² haka girar ta mai yalwar gashi, bakinta ɗan ƙarami wanda ya bada launi ja kaɗan haƙoranta siri² farare tas masu ɗauke da wushirya a tsakiya mai ƴar faɗi, se dai bata dimples, iya kyau Ruwaidah tanada kyan fuska da na dirin jiki dan dirarace sosai.
Masha Allah nace, ganin yanda takeda dirarran jiki me kyau, doguwace amman ba can ba saboda tana da ɗan kauri kaɗan batada rama, sanna bata da ƙiba wato tsaka tsakiya ce ita, amman akwai mazauna, ga hips kamar zasuyi magana, uwa uba boobs ɗinta, Allah ya mata baiwar dukiyar fulani, irin manyan nan kuma tsayayyu masu tsinin nipples ga taushi, ita ɗin ta daban ce cikin mata, Allah yay mata kyawun diri da sura mai matuƙar kyau da ɗaukar hankalin duk wani namiji mai cikakkiyar lafiya, duk da ita ɗin ba babba bace shekarunta 18. Amman akwai hankali da sanin yakamata.
A hankali ta fara takawa cike da nutsuwa kanta a ƙasa, ta sauko babu wanda ta kalla ta fara tafiya a nutsu, hannunta babu kome daga ita sai teddy ɗinta, se gorar ruwan da ta saya tindaga kano.
Duk da a katon hijab take hakan bazai hana ka gane irin baiwar kyawunta ba da kyan surata, duba da yanda take takawa a nutsu, kanta a ƙasa, amman jikinta ko ina motsi yake tamkar tarwaɗa, asace take ƙarema tashar ta Jalingo kallo.
Tana fitowa ta shiga waige-waige ta rasa ina ma zata nufa, tayi sallah, tana tsallaka titi tafiya kawai take sam bata san inda zata nufa ba, ga bata son magarib ta wuce.
Tafiya tayi me nisa sosai, ta fara jin ƙishirwa, gefen hijabinta ta saka tana goge ƙwallar idanunta, bishiya ta hango ta uwar mangwaro, gashi ta gaji, raɓawa tayi gefen titin jikin uwar itaciyar mangwaro, ta zauna ta buɗe bottle water ɗin ta kafa bakinta tasha sosai, ta cire ta tsugunna, ta daura alwalla, ta zura hannunta kanta, ta sinto ɗankwalin kanta wanda ta ɗaure uban tulun gashinta, ta shimfida nan ƙasa bishiyar ta tayar da sallah. Tana gamawa tayi Addu'a ta shafa, jikin bishiyar ta zauna cike tsananin tsoro saboda ita mutumce mai tsoron gaske.
Haɗa kai da guiwa tayi ta fashe da kuka, tana rungume da teddy.
Ɗan gambo kuwa tinda yaga yarinyar nan cikin mota ya lura batada nutsuwa, barin ganinta bata tare koda jakane, ya gane guduwa tayi.
Shiyasa ya saka mata idanu, lokacin da suka fito daga motar, bai tafi ba, ganin kowa na famar yin sallah yasa ya saka mata idanu, kayansa yaba wani mai keke napep yakai masa gidansu, sbd sanane ne sosai a tashar duk sati yake zuwa kano, shiyasa yayi sabo da jama'a a tashar sosai, saidai duk abinda yake yana taka tsantsan idan ba kun haɗe a gidan gwamma magajiya ba....
Yana bibiyarta yaga inda zata, har lokacin da yaga tayi sallah ta zauna gindin bishiyar, kenan hakan ya nuna masa babu takamamman gurin zuwanta.
Wayarsa ya ciro daga aljihun wandonsa yay dialing ɗin wata number, tanata ringing ba'a ɗaga ba. Tsaki yaja yace"Kaji banzar matarnan ki ɗauki ƙira arziki ne ya samu, ko na kaita gidanmu yasin."
Saida ya mata missed calls 5 kafin take ɗagawa. Cikin masifa yace"Gwamma bakida rabon arzikine kome? Ina ƙira baki ɗauka to wallahi ɗanya sharaf ce na samo irin tagaban motar nan dagani zata kawo wuta, yarinyar babbar yarinya ce da duk halamu kuma tana neman temako..." Shiru yay ko me aka ce masa daga can ya amsa da.
"Ok amman zaki biyani kaso me tsoka fa, dan nasan anan zaki tara haja wallahi." ya faɗi yana tsinke ƙiran. Ya nufi gun Ruwaidah wacce take famar kuka harda shasheƙa.
Kusa da ita ya tsaya yace"Ƴan mata ykk kina buƙatar temako ne?" Da sauri ta ɗago kyakyawar fuskarta da ta cika da ruwan hawaye sharaf. Miƙewa tayi a ɗan tsorace! Ta fara tafiya gudu-gudu sauri².
Binta ɗan gambo yayi yana cewa"Please ki tsaya bazan cutar dakeba, wlh wajanan cike yake da haɗari, zuwa anjima kome zai iya faru dake, tsaya na temaka miki , amshi mamana kuyi waya idan baki yarda dani ba." ya faɗi yana dialing ɗin number Magajiya gwamma. Ruwaidah jin ya ambaci mamarsa yasa ta tsaya, a ɗan tsorace.!
Gabanta ya iso yana magana yace"Mama ki mata magana mu temaka mata mota ɗaya muka shigo tin daga kano, to naga kamar batasan kowa ba, kinsan kuma halin garin nan idan dare yayi." ya faɗi yana bata wayar. Amsa tayi tasa a kunnenta. Ɗaga can matar tace"Yarinya karki tsaya atiti ki biyo yarona zan temaka miki, wlh wajan da kike bashida kyau, kizo nan zakiji daɗi kinji."
Ruwaidah ta jinjina kai tana hawaye ta bashi wayar, tana jinjina kai, ta masa kwatance da hannunta, ta faɗa masa, ta yarda zata bishi ya faɗama maman.
Ɗan gambo ya kara wayar a kunnensa yace"ikon Allah! Gwamma jikina yayi sanyi bata magana fa." bai jira daga can anyi magana ba ya tsinke ƙiran yace.
"Muje to."
Gaba ya shiga tana binsa a baya suka isa bakin titi, dakyar ya samu me napep suka shiga.
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.