*QADDARAR MU CE*
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*3*
Yau kimanin kwana 5 kenan da kwantar da Mahmoud a asibiti saidai har yanzu Yana nan kamar yadda aka kawo shi, kimanin kuma kwana 2 kenan da zuwan Hafeez wanda tun ranar bai dawo ba saidai ya kan kira Hadeeza a waya yaji lafiyar su, sannan ya kan aika Baballe ya kai mata abinci da sauran abubuwan da ba a rasa ba.
A yanda ya fadawa Hadeeza aiki ne ya mishi yawa bai samu damar zuwan ba, amma har ga Allah fargabar Biyawa Hadeeza buqatar su ne ya hana shi zuwa don kuwa shi har yanzu bai gama yanke hukunci ba sannan kuma baiyi shawara da kowa ba.Hadeeza ce zaune cikin dakin asibitin akan sallaya bayan ta idar da sallar isha.
Daga hannayen ta biyu tayi tana kwararo addu'a da a yanzu ita kadai ce abinda ta riqa ta kuma tabbatar itace solution dinta.
"Ya Allah na tuba, Allah na tuba da duk wani laifi da nayi, ya Ubangiji kada ka hukunta ni da Mahmoud, ka sani shine farin ciki na, Allah ka tashi kafadar Mahmoud, Allah nasani kafini son Mahmoud amma na roke ka kada ka karbeshi yanzu, ya Allah bazan iya jure rashin Mahmoud ba, bazan iya ba ya Rabbiiii."
Hadeeza ta qarashe da wani irin kuka mai cin rai, kuka take sosai kamar wadda akayiwa bushara da mutuwa cikin mintuna qalilan, kuka takeyi sosai domin Allah ne kadai tasan zatayi kuka kuma yajita ya bata mafita don haka ta kifa kanta akan sallayar ta cigaba da raira kukan ta.
Kamar a mafarki taji alamar motsi hakan yasa ta dago kanta a tunaninta ko wata nurse din ce ta shigo, jin shiru ne yasa ta mikewa tana waige waige..
kamar ance ta kalli Mahmoud da ke kwance sai ta hangi Hannun shi wanda babu drip a jiki yana motsi shine har ya tabo kan locker jikin gadon da taji motsi.. da sauri ta matsa kusa dashi tana kiran shi "Mahmoud! Mahmoud! Ya Allah! Mahmoud ka bude idonka mamy ce"
Hadeeza duk ta rikice ta sake fashewa da kukan da ita kanta tasan na farin ciki ne, ji takeyi kamar Allah yaji kukanta ne shi yasa ma har Mahmoud din ya motsa. Da gudu ta fita daga dakin, nurse din da ta fara cin karo da ita wadda tasan mostly ita ke zuwa sawa Mahmoud din drip ita ta kira tana fada mata Mahmoud ya motsa. Hakan yasa nurse din tafiya ta kira daya daga cikin Doctors din dake Available suka nufi dakin. Itama Hadeeza bayansu ta bi tana share kwalla.
Ko da suka shiga kuwa kokarin bude idanun shi yake yana kiran "Mamy, Mamy ruwa" a sukwane Hadeeza ta qarasa tana sunkutar robar ruwan da ke gefen gadon zata bashi, nurse din dake tsaye ce ta karba tana fadin "kawo zan bashi".
Ita kuwa Doctor Marwal tuni ta soma aikin duba yanayin jikin Mahmoud din.
Mikar dashi tayi zaune sannan tasa nurse din ta bashi ruwa kadan yasha, ta kuma umarci Hadeeza da a hada mishi ko tea ne yasha sannan a mishi wasu allurai.
Shi dai Mahmoud Bin su kawai yake da ido har suka fita ya zama daga Hadeeza sai dan nata.
Tea ta hada mishi mai dan kauri sannan ta dawo kusa dashi ta zauna tana murmushi tace "Bude bakinka M.J (Sunan da ta kan kirashi dashi kenan ma'ana Mahmoud junior) ka daure kasha tea dinnan kafin azo ayi Allura" yamutse fuska yayi a shagwa6e yace "Bazan sha ba ni bana son Allura"
Girgiza kanta kawai tayi tana murmushi tace " Bakaso mu bar asibitin nan Ka koma skul ka hadu da friends dinka? Ko baka missing su Ashraf da Abulkhairi?"
Hakan ne yasa Mahmoud din karbar tea din domin yaron ba kamar sauran yara bane, shi kam yana son makaranta gashi kuma da manyance. yanzun ma ya karbi cup din tea din ne don bai yarda a bashi ba shi fa a ganin shi shima Big boy ne kamar yanda mamyn shi take fada.Kadan yasha ya mika mata yana yamutse fuska alamar ya koshi tace "Haba mamudan mamy ka dan qara mana"
"To ba daci yake min ba" ya fada a shagwabe kamar zaiyi kuka.
Dariya kawai tayi bata matsa mishi ba don ba shi ba da yake kwance tsawon kwana 5 ba ko ita da ke jinyar ba dadin komai take ji ba tana dai ci ne don dole.
Bude kofar da akayi ne yasa ta juyawa sukayi ido Hudu da Doctor Ma'aruf da wata nurse a bayan shi, karasowa yayi fuskar shi dauke da murmushi yace "what a surprise Mahmoud! I know u are a fighter zaka tashi. oya give me five"
Dariya Mahmoud yayi yana mikawa Doctor Ma'aruf hannu suka kashe sannan ya ce "Doctor kaima zaka min Allura ne? Ni fa banaso tana min zafi🥺" ya marairaice kamar zaiyi kuka.
Murmushi Doctor Ma'aruf yayi yace "Kai da mukeso ka koma skul ai dole ayi allura, amma bani zanyi maka ba saboda ni friend dinka ne wannan antyn ce zata maka"
Doctor ya fada yana nuna nurse din dake tsaye riqe da tray na injections a hannunta.
Da ido Doctor Ma'aruf yayi mata alama da ta qaraso ta kuwa qarasa din tana kokarin tsikarawa mahmoud Allura.
"Kece bakya sona ko, ko don ni ba friend dinki bane?" Mahmoud yai tambayar yana kafe ta da ido.Ba nurse din ba da Doctor Ma'aruf hatta Hadeeza da ta zuba musu ido tun shigowarsu sai da tayi dariya sannan tace "Mahmoud itama tana son ka, kullum sai tazo ta dubaka fa, tana so ka koma skul da wuri ne shiyasa za tayi maka allura."
Kallon mamyn tashi yakeyi yayi shiru amma shi kam bai gamsu ba, Hakan yasa Doctor Ma'aruf cewa "Big boys ba sa tsoron Allura M.J, juya in rike ka kaji mutumina"
Baiyi musu ba kuwa don haka ya karkata Ma'aruf ya rikeshi akayi allurar.
Ko da aka gama kuwa baiyi kuka ba saidai yayi ta cin magani yana ta6e baki alamun yaji zafi amma gudun kar a rainashi ko ace shi ba Big boy bane yasa ya dake..Babu laifi Dr Ma'aruf ya dan zauna sunyi hira da Mahmoud din inda Hadeeza take mamakin surutu irin na Mahmoud, ace mutum ya farka bayan tsawon kwanaki 5 a kwance amma yana Hira? Lallai ta tabbatar da maganar wata mai aikin ta Mama Lami da tace "Mahmoud ko a gadon mutuwar shi indai da baki a fuskar shi saiyayi surutu"
Ta kuwa tabbatar yau don dukda kana ganinshi kasan yana jin jiki hakan bai hanashi magana ba har da tafawa da Doctor jifa jifa.
Wani irin farin ciki ne da kuma fargaba ya ziyarci Hadeeza wanda ya saukar mata da wasu zafafan hawaye daga idanunta ganin dan nata a zaune har yana Hira.
Tana yunkurin gogewa ne karaf taji muryar Mahmoud "Doctor kaga mamy na kuka"
juyawa Ma'aruf din yayi yana kallon Hadeeza kafin ya maida kallon shi ga Mahmoud "Tears of joy kenan Mahmoud, mamy na kuka ne saboda ka tashi zaka koma skul"
"Mamy wai haka?, ko kina tsoro ne kada na mutu kamar kakana da uncle Mahmoud? Kuma ma ba kince idan mun mutu zamuje mu gansu ba? Ni dama inaso inje ingan su, kuma zan bawa kaka labarin yanda kike kallon pictures dinshi da uncle Mahmoud kina kuka, kuma ma zan fadamusu munayi musu Addu'a kullum kuma ma..."
"A'a Mahmoud bazaka mutu ba, ba yanzu ba don Allah bazaka mutu ka bar mamy ba"
Hadeeza tayi saurin katse mahmoud da wata iriyar murya mai ban tausayi sannan ta fashe da wani matsanancin kuka.Sosai ta bawa Doctor Ma'aruf tausayi shi kanshi sai da yaji wata 'yar kwalla tayi saurin taho mishi yayi saurin goge ta yace "Mahmoud kayi shiru kaji, ba a son yawan magana idan mutum bashi da lafiya, idan ba haka ba zamu barka a nan ba komawa skul, ko kanaso mu barka a nan?"
Da sauri Mahmoud ya girgiza kanshi Doctor yace "yauwa good boy" sannan ya mike yana cewa Hadeeza "zan turo wata nurse din ta taimaka miki a gyara shi yanzu ya samu ya ji dadin jikin shi, Allah ya qara lafiya"
Daga mishi kai kawai tayi bata amsa ba ya fice ita kuma ta matso dab da Mahmoud din.
Rungume shi tayi sosai kamar ance mata wani zai kwace mata shi.
Cikin wata raunanniyar murya tace "Bazaka mutu ba Mahmoud, Ba zaka tafi ka bar Mamy ba, Ba yanzu ba M.J"
Bin ta kawai yake da kallo shikam Mamyn mamaki take bashi da wadannan maganganun.
"Promise me Mahmoud, promise me bazaka mutu yanzu ba, promise Mamy ka jii"
Ba Mahmoud da ke bin ta da kallo ba ita kanta tasan ta dan zare na wasu lokaci, To amma me? Assurance take nema kuma tunda babu wanda zai bata babu laifi don ta tambayi dan nata duk da tasan sanin gaibu sai Allah.
Kamar bazai yi magana ba sai kuma taji ya qara qanqame ta yana cewa "I promise".
Ajiyar zuciya ta saki mai nauyi tana qara qanqame shi tana jin kamar ta maidashi cikin ta ta sake haifo shi...#Masu ce!
ESTÁS LEYENDO
QADDARAR MU CE
FantasíaLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!