🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*39*
Kano city, 2022.
Ya riga ya saba da tashin hankali, duba da irin abubuwan da suka dinga faruwa da rayuwar su.
Hasalima ya kamata ace ya riga da ya zame mishi jiki.
Ya saba da fama da marasa lafiya, hasalima idan baije wajen aiki ba ya gana dasu har baya jin dadi.
Ya kuma saba da kar6ar haihuwa, hasalima bazai iya lissafa yaran da ya bada gudunmawa wajen zuwan su duniya ba.Saidai bai san meyasa ba, baki daya a yanzu da matar shi ke fama da naquda, ya kasa samun nutsuwa a ilahirin jikin shi, shiyasa ma yake ta sintiri cikin asibitin da ya kasance mallakin shi.
"Taha mana! Ka samu nutsuwa ka samu waje ka zauna. Haba da Allah, sai kace ba likita ba?".
Juyowa yayi ya kalli Maman Jiddan dake zaune kan kujerar zaman jiran dake cikin corridorn asibitin.
Shi kam da ta san yanda yake ji da batayi mishi tayin zaman ba.Ji yake baki daya duniyar ta mishi zafi, Ji yake tamkar yaje ya kar6i ciwon dake jikin Dee ya maidashi nashi jikin.
Ji yake tamkar itan ma wani abu zai same ta, Ji yake tamkar itan ma mutuwa zata yi ta bar su.Shiyasa ko dazu ya kasa amsa tambayar Mahmoud, shiyasa yake ganin tamkar tambayar da Mahmoud din yayi mishi zata kasance gaskiya.
"Abba, meyasa muka kawo Mummy nan? Ko dai itama tafiya zatayi ta bar mu kamar Anty Maryam?"
Tambayar Mahmoud din tazo mishi a bazata.
Qarfin hali ne kawai yasa ya iya amsa Mahmoud din.
"A'a Mahmoud, Mummy zata haifa muku qanwa ko qani ne. ko kuwa baka so little ta samu masu ce mata "yaya" kamar yanda take kiran ka ne?"
Girgiza kai Mahmoud din yayi, tare da fadin.
"Ina so, amma bana so idan ta haifa mana
Babyn kuma ta tafi ta barmu"Hakan yasa Tahan sauke numfashi mai nauyi.
Shi din ma tsoron nashi kenan, saidai baya so ya bayyana nashi tsoron a wannan yanayin.
Hakan ne ma yasa shi kiran Mama a waya don ta turo wanda zai zo ya tafi da su Mahmoud din gida.Little dama tun a mota tayi bacci kafin su qaraso asibitin, shiyasa tun shigowar su ya bawa wata nurse ita ta je ta kwantar da ita.
Zuwan Mama da Maman Jiddan ne yasa Maman tafiya da su Mahmoud, duk da cewa taso ta zauna amma sam Maman Jiddah tace ta tafi ita zata zauna har zuwa lokacin da Allah zai sauki Hadeezan.
Maman Taha da kanta tace kar a sanar da Ummi har sai Hadeezan ta sauka lafiya.
A cewar ta Ummin zata iya daga hankalin ta har hakan ya tasar da ciwon hawan jinin ta, musamman a yanzu da ya kasance tun bayan rasuwar Maryam abu kadan ke haifar mata da tashin ciwon."Ka kwantar da hankalin ka Taha, Inshaa Allahu zata sauka lafiya. Ka zauna ka cigaba da mata Addu'a".
Maman Jiddah ta qara fada, wannan karan cike da kulawa.
Ba wai don yana son zaman ba, ba don yana ganin hankalin shi zai kwanta din ba, ya dai zauna ne kawai don yasan Maman Jiddahn bazata qyale shi ba.
Tunda ya zauna wani tsoro yake dada lullu6e shi.
Ba kuma iya tsoron halin da Hadeezan take ciki ba.
Tsoro ne na rayuwa da yanda dan Adam bai kasance a bakin komai ba tsakanin rayuwa da mutuwa.
Tsoro ne na yanda lokaci guda, cikin mintina qalilan ciwo na rashin lafiya ko naquda zai zo wa dan Adam da qarar kwana ba tare da ya shirya ba.Shi kam ko da suka tashi da safe har ya fita ya dawo da yamma tare da Albishir din haihuwar Teema, bai kawo cewar naqudar ta tana kusa ba.
Hakan ne ma yasa shi saka ta ta shirya don ya kai ta inda yake ganin zata so ganin wanda yake wajen.
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!