Chapter 32

57 4 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                             *32*

Sokoto, 2013.

Gaba daya a rayuwar ta bata iya aikin sauri ba, musamman idan mutum yana tsaye a kan ta da sunan ita yake jira.
Duk sai taji ta rikice, sai ta rasa ma me ya kamata tayi.
Shiyasa ko a yanzun ma da take nemawa Zakiyya biro baki daya ta rikice, tsawon kusan mintina biyar kenan tana hargitsa kayan jakar da take ganin za a samu biron a ciki.

"Baki gan shi ba? Bari kawai naje, ko a hanya na siya".

"Yauwa cikin wannan littafin ne"

Hadeeza ta fada tare da zaro littafin dake cikin Babban akwatin ta.

"Yauwa Anty Hadeeza na, sai na dawo. Wish me luck. Idan Mahmoud ya tashi ki shafa min kanshi".

Zakiyyan ta fada bayan ta kar6i biron, cikin hanzari tare da qoqarin barin dakin.

Murmushi Hadeeza tayi tana fadin "Allah ya kiyaye" wanda take kyautata zaton Zakiyyan bata ji ba saboda saurin da take wajen barin dakin.

Bata san meyasa abubuwa da yawa na zakiyyan ke mata yanayi da Teema ba. Gashi dai zakiyyan ta girmi Teema don a qalla zatayi shekara goma sha takwas, sabanin Teema dake da sha biyar.

Saidai wasu halayen nasu na mata kamanceceniya, kamar yau din nan da Zakiyyan ta qwanqwasa mata daki tun sassafe akan ta ara mata biro wai zatayi assignment din malamin da suke da lecture shi qarfe takwas na safe.

A cewar Zakiyyan da ta kasance dalibar aji biyu dake jami'ar Usman dan fodiyo inda take karantar microbiology, ta fadawa Hadeeza malamin na da tsauri kuma ya umarce su da su kai mishi assignment din office dinshi kafin qarfe takwas na safen.
Saidai kasancewar zakiyyan zakiyya ce, har shida da rabi na safe sannan ta tuna cewa bata da biro, gashi kuma shagon dake kusa dasu basu bude ba, kuma tana ganin kafin ta isa makaranta taje ta nemi biron tayi lokaci zai qure mata.

Shiyasa tazo wajen Hadeezan, saidai Hadeeza ta san kimanin watanni biyun da tayi a garin sokoton bata yi amfani da biro ba, tunawa da cewar cikin littattafan ta bata rasa biro yasa ta dubawa don taimakawa zakiyyan da ta lura fuskar ta cike take da tsoron malamin nasu take.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan tafiyar zakiyyan, tare da maida kallon ta ga Mahmoud dinta dake kwance yana bacci tamkar ba shi ne ya hana ta bacci cikin dare da kukan shi ba.

Har ta riga ta saba ma cikin kwanakin nan da rigimar Mahmoud din cikin dare, ta riga ta saba da yanda yake hanata bacci shi kuma ya ci nashi baccin daga kiran asuba har zuwa wayewar gari.
Saidai hanata baccin da Mahmoud din ke yi bai hana soyayyar shi ratsa zuciyar ta kowanne dare da rana ba.
A kullum takan tsinci kanta da godewa Allah da ya hana ta nasarar salwantar da rayuwar yaron da a yanzu take jin zata iya bada ta ta rayuwar don ku6utar da tashi rayuwar.

Idan har akwai wani abun farin ciki da zata dorar daga ranar da ta bar gida bai wuce bude idanun ta taga Mahmoud ba. Bai wuce lokutan da zata ga yana wasa da guntayen hannayen shi ba ko kuma lokutan da zata ga yana murmushi ko da cikin baccin shi ne.

Tana jin yaron a ranta fiye da kima, tana matuqar qaunar shi da tausayin shi.
Ita da kan ta bata san wacce iriyar soyayya take yiwa Mahmoud din ba, saidai ta tabbatar tana mishi soyayyar mutum biyu ne.
Ma'ana soyayya ta tsakanin uwa da da, da kuma soyayyar da take mishi a madadin Mahmoud Babba da ta rasa.

Ita kam bazata ce zuwa garin sokoto yayi mata dadi ba, saidai bazata dorar da wasu matsaloli masu yawa da ta samu bayan zuwan ta garin ba.

Tun daga tasha Allah ya hada ta da wani dattijo wanda shi ya taimaka mata wajen samun gidan da take a yanzu, a cewar shi dama aikin shi samawa dalibai gida shi kuma ya dan samu alkhairi daga masu gidan da ma su kan su daliban.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now