🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*20*
Kano city, 2012.A kan ce lafiya uwar jiki, kuma itace jigon rayuwa. Amma da yawa daga cikin mutane suna ganin kamar dukiya itace jigon rayuwa, suna ganin tamkar idan da dukiya komai na rayuwa mai sauqi ne.
Saidai a yanzu Hadeeza ta dada tabbatar wa kanta lallai lafiya tafi dukiya.
Ta dada imani da cewa akwai abubuwa da yawa da kudi bazasu iya warkar maka ba, ciki kuwa har da zafin ciwo.
Ta qara imani cewa Allah abin tsoro ne kuma duniya ma haka, ta kuma yarda mutum ba a bakin komai yake ba duk mulkin shi da ikon shi a duk lokacin da Allah ya dora mishi wata lalura.Tana da yaqinin da kudi suna maganin kowanne irin ciwo da ba a ce Abban ta ne kwance cikin asibitin nan ba cikin yanayin da bazata juri ganin shi ba.
Cikin lokacin da bai wuce wata daya ba da kwanciyar da yayi a asibiti bayan birthday shi har aka sallame shi gashi yanzu jikin shi ya qara tsanani.
Ko sati biyu ba a yi ba fa ya sa aka tsaidar ranar auren su "Hadeezan da Taha" da kuma "Jiddah da Haidar" inda aka sa wata 3 don yayi daidai da lokacin da Jiddah zata gama karatun ta na degree tunda Haidar ya dawo gaba daya.
Amma tun bayan faruwar hakan da kwana 2 jikin Abban ya qara tsanani wanda dole aka sake basu gado a asibitin.Wasa wasa ciwon har ya kai matakin da suka soma tunanin fitar dashi waje, saidai sam Abban yace shi bayaso.
A cewar shi idan har yana da rabon warkewa ko a ina ne ma zai warke, idan kuma ciwon ajali ne baya burin ya mutu a wata qasar da ko za a dawo da gawar shi sai an wahala.
Gashi yanzu an kai matakin da likitoci sun ce ciwon sugarn nashi yaci jikin shi sosai musamman qafar tashi da yake kuka da ita ana maganar sai a yanke ta.Sunyi iya qoqarin su suga an samu wata mafitar da Abban zai samu sauqi ba tare da faruwar hakan ba amma likitoci sun tabbatar da a halin da ake ciki hakan shine mafita.
Sunyi qoqarin su fitar da Abban waje amma Taha ya sanar dasu ko a can dinma abinda za a yi kenan, gashi kuma shima Abban ya tubure kan cewar indai sauqin zai samu a yanke qafar don shi kadai yasan me yake ji.Dukkan abubuwan dake faruwa Hadeeza ta gaza yarda cewa ba mafarki take ba.
Ta kasa gane dalilin da yasa lokaci daya duniyar ta juya musu haka.
Ga dai kudin iya kudi, ga kuma gata da soyayya da yake samu daga wajen su da 'yan uwanshi, da mutanen arziqi.
Amma sam hakan bai dauke mishi zafin ciwon da yake fama dashi ba.Ta gaji da zaman cikin dakin asibitin ne, musamman da ya kasance su gwaggo Mero da Maman Taha suna ciki.
Sam bata jituwa da su, suma kuma tana ganin tamkar basa qaunar ta ne don bata ga dalilin da zai sa a duk sanda suka ganta su dinga kiranta da buzuwa ba don dangin mahaifiyar ta sun kasance buzaye.
Ita dai kawai tana basu girman su ne na iyaye, amma tana sane da irin qiyayyar da suke nunawa mahaifiyar ta don haka kar take kallon su.
A yanzun ma ganin sun gaisa ne tasan idan ta cigaba da zama dasu waje daya zasu fadi abinda zai 6ata ranta yasa ta fito harabar asibitin.Ita bata san ma dalilin su na zuwa ranar ba tunda a ranar aka ce za a yiwa Abban aikin, sun kuma san ba ganin shi zasuyi ba amma sunzo sun tare suna faman hira.
A tunanin ta ma ai idan da buqatar suzo din kamata yayi ace addu'a suka zauna suna mishi kan Allah yasa ayi aikin a sa'a.
Amma inaaa? Sai faman yada maganganu sukewa mahaifiyar ta a fakaice tamkar ita ta dora mishi ciwon.
Su ko tausayin Ummin ma basa yi yanda ta rame ta fige lokaci guda tamkar ciwon a jikin ta yake.
Tunda aka kwantar da Abban take dawainiya dashi ko son zuwa gida bata yi.
Duk iya qoqarin da Haidar da Taha zasuyi kan ta tafi gida ta huta su zasu kwana dashi sam bata yarda, a cewar ta ko taje gidan bazata iya baccin ba a halin da yake ciki.Sosai Hadeeza ke tausayin Mahaifin nata dake kwance, da kuma ita kanta ummin da ke jinyar tashi.
Su kansu abin tausayin ne tunda baki dayan su rayuwar su ta koma ta asibitin musamman Hadeeza da ta gama makaranta.
Dama bautar qasa take kuma ba zuwa take yi ma'aikatar da aka kaita ba saidai ta biyasu duk wata.
Ko Maryam da Teema ma dake zuwa makaranta kullum idan suka tashi suna hanyar asibitin sai dare suke komawa idan ummi ta korasu.
Hatta Haidar da Taha ma suna iya qoqarin su, musamman Taha da ya kasance a asibitin yake aiki koda yaushe cikin musu hidima yake.

ESTÁS LEYENDO
QADDARAR MU CE
Ficción GeneralLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!