🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*33*
Sokoto,
Yanda duniya ke gudu, yanda dan adam ke tashi kowacce safiya ya wuni dare ya qara yi gari ya waye kadai ya ishi mai hankali fahimtar yanda kowacce rana ke zuwa da qarar kwanan mu.
Mu kan ce duniyar na gudu, amma dayawa daga cikin mu ba ma fahimtar yanda duniyar ke gudu da abubuwa da yawa a rayuwar mu wadanda bazasu dawo ba.
Kamar yau ne fa, kamar yau ta bar gidan su, ta bar kowa da koman ta, ta bar mutanen da tafi so fiye da komai a rayuwar ta, kamar yau ta shigo garin sokoto har ta hadu da ita, ta hadu da yarinyar da ta rage mata kadaicin mutanen da ta baro a baya.
Kamar yau suka hadu take fada mata ita daliba ce dake aji biyu a matakin degreen ta.Bazatayi qarya ba idan tace a lokacin da suka hadu da Zakiyya ta hango mata gama makaranta nan kusa, sai gashi Allah cikin ikon shi kwanci tashi shekaru biyun da take ganin kamar ita ko Mahmoud bazasuyi su a raye ba sun iso, wai har Zakiyyan ta kammala jarabawar ta ta qarshe.
"Anty Hadeeza mana, baki ce nayi kyau ba".
Zakiyyan ta fada tana turo baki, wanda tsawon shekaru biyun da Hadeeza tayi da sanin ta duk sanda tayi hakan sai ta tuna mata da Teema.
Murmishi Hadeezan tayi tare da fadin "kinyi kyau mana Antyn Mahmoud, ai yau ke zaki haska kowa ma cikin yan ajin naku".
Hakan yasa Zakiyyan fadada murmushin ta don ita tana so a yabe ta, a kambama ta, musamman irin wannan ranar da ta shafe watanni ko tace shekaru tana jiran ta.
Ranar da ta kasance ranar da zasuyi taron 'yan ajin su don taya juna murnar gama makaranta.
"Momi, momi, uwa".
Sukaji muryar Mahmoud da tashin shi kenan daga bacci.
Al'adar shi ce duk sanda ya tashi daga bacci abinda yake fara nema shine ruwa, shiyasa ma Hadeeza take ajiye ruwan a kusa, kamar yanzu ma da miqa hannu kawai tayi ta dauko tare da bashi ledar pure watern da ya fasa da kanshi yana zuqa tare da zama a jikin ta.
"Mahmoud baka ganni bane? Bazaka ce Anty kinyi kyau ba?"
Yanda Zakiyyan ta qarashe maganar tana shagwa6e fuska yasa Hadeeza dariya, dariyar da tunda ta sauka garin sokoto Zakiyya kadai ke da baiwar sakata yin ta.
"Mahmoud kaji Antyn ka, kace Ati kinyi kyau".
Hadeezan ta fada tare da qoqarin kwaikwayon yanda Mahmoud din ke kiran Zakiyyan da "Ati" a madadin Anty.
"Ati, gwalagaala lala....."
Ya fara gwarancin da su duka basu san me yace ba amma suka sa dariya, dariyar da shi kanshi Mahmoud din tasa shi dariya.
Qarar wayar Zakiyyan da ake kira ne ya katse su daga nishadin su, inda zakiyyan ta amsa tare da fadin "Okay, gani nan fitowa".
Kallon ta Hadeeza tayi, hakan yasa ta amsawa da "Bari naje, K.B ne zai kaini dama, wai ya qaraso".
Irin kallon da Hadeeza tayi mata yasa Zakiyyan qarawa da "Come on, Anty Hadeeza, kinsan dai bazan ci kwalliyar nan naje na hau napep ba, dinner graduation dina fa zanje, please kar kice komai".
"Bana buqatar na sake nanata miki, ki kula dai. Kuma ki tabbatar kin koma gida a kan lokaci. Ki kira ni idan kin isa gidan, kuma ki hada ni da Baban Murja (Mai gadi) na tabbatar kin isa".
Yanda Hadeezan tayi magana zaka rantse ba ita ke dariya da Zakiyya mintina ko sakanni kadan ba. A cikin muryar ta zaka fahimci babu wasa a tattare da ita.
![](https://img.wattpad.com/cover/146407140-288-k405691.jpg)
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
General FictionLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!