Chapter 34

46 2 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                               *34*

Sokoto,

Ko a baya bata son mutum mai naci, bare kuma a yanzu da ta tsani maza, ta tsani duk abinda zai hada ta dasu. Take kuma kiyaye duk wata mu'amala da zata hada ta dasu.
Saidai ta lura mutumin nan nacin shi na daban ne, ta rasa dalilin shi na bibiyar rayuwar su haka.

Sati biyu kenan da Haduwar su ta farko a asibiti lokacin da ta kai Mahmoud allura, tun a ranar ma bata bashi fuska ba, ba kuma ta bari wata magana mai tsayi ta shiga tsakanin su ba.

Bata sani ba tsautsayi ne ko qaddara ta sake hada su yau a asibiti, abu daya dai ta sani ko ma menene bata farin ciki da ganin shi.
Sa6anin Mahmoud da kallo daya ya gane shi ya kuma nuna farin cikin shi da ganin mutumin, babu kunya har da miqa mishi hannu kamar wani babba suka gaisa.
Saidai ta dauki hakan me yiwuwa saboda ranar farko da suka hadu ya bawa Mahmoud alewa lokacin da ya gudu wajen shi yana tsoron allura.

Saidai ta lura mutumin ya zaqe da yawa, ta yanda ya nemi ya kai su gida bayan fitowar su daga cikin asibitin.
Hauka da yarinta irin na Mahmoud taga ya nace mishi, tun kafin ma ta nuna rashin amincewar ta ya budewa Mahmoud qofar gaba ya shiga.

Ta wani 6angaren bata ga laifin Mahmoud din ba, don zata iya cewa bai fi sau daya ko biyu ya ta6a shiga mota ba tun da suka zo garin sokoto.
Sau daya da Dr.Ma'aruf ne da wataran ya rage musu hanya, sau daya kuma tun kafin zakiyya ta gama makaranta wataran da suka fita a motar saurayin ta.
Don haka ganin mota mai kyawu irin ta bawan Allahn ta rudi Mahmoud, shiyasa ma da ya bude mishi yayi gaggawar shiga.

Tayi mamaki yanda ko tsawar ta bata sa Mahmoud fitowa ba, hasalima shi mutumin shi yake ziga shi kan kar ya fito yayi zaman shi.

"Kinga, idan baki shirya tafiya ba ki bani adress din ni sai na sauke shi a gidan, idan yaso sai ki biyo mu daga baya".

Ya fada bayan wani lokaci.

Wani irin kallo ta watsa mishi, don ita tunda take ma bata ta6a ganin dan rainin wayo kamar wannan ba.
Haduwar farko? Zai zira mata yaro a mota kuma yace zai tafi dashi ya bar ta?

"Wai kai wane irin mutum ne? Daga ganin mace da yaro baka sani ba ko ni matar wani ce zaka nemi shishshige mana dole?
Kaga malam, ka sauke min d'a na tunda dama can ba kai ka kawo mu ba".

Ta fada a fusace.

Murmushi yayi, murmushin da ya sake 6ata ran ta.

"Ban gani an zana a goshin ki ba cewar ke matar aure ce. Don haka idan nayi kuskuren gane hakan kiyi haquri, ki ajiye fushin a gefe muje na sauke ku, naga akwai hadari sosai a garin ne. Kuma ko ba don ke ba bazan so ruwa ya ta6a aboki na ba".

Da ta san cewa tun ranar farko da ya ganta yake sha'awar cusa kan shi garesu, da ta san cewa tun a ranar farko ya san cewa bata da aure, da ta san cewa yayi iya qoqarin shi wajen sanin abubuwa da dama a kan ta fiye da ciwon Mahmoud din.
Da bata yi zargin shi da cusa kan shi garesu ba ba tare da sanin tana da aure ko babu ba.

Sun dau tsawon lokaci tana tsaye, ta kuma qi motsawa ko da nan da can.
Yayyafin da aka fara akan su yasa shi hanzarin shiga mota, tare da tada motar.
Yayi mata horn yafi sau biyar kafin ta gama kokawa da zuciyar ta ta yarda ta shiga motar ta shi.

Tunda suka dau hanya ta fada mishi unguwar da zasu je bata qara magana ba, shima kuma hirar su kawai suke da Mahmoud tamkar wanda suka dade da sanin juna.
Labarai kala kala na makaranta da asibiti Mahmoud din ke bashi, shima kuma tamkar wani yaro sai yake biyewa Mahmoud din suke ta dariya.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now