🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*25*
Kano city, 2012.
"Kai! Allah dai ya sakawa Gwaggo Merow da Alheri. Wannan magarya ba dai zaqi ba".
Maryam dake hakimce kan kujerar gaban mota ta fada cike da santin magaryar da take sha."Gaskiya dole ma da bikina ayi magarya day kowa yasha ya qoshi".
Wannan karan tana magana tana kallon Hadeeza dake tuqi wadda gaba daya hankalin ta na kan tuqin ta da alama ma bata ji surutan da Maryam din keyi ba.Hakan yasa Maryam dake zaune gefen Hadeezan ta sa Hannun ta tana ta6a ta tare da fadin "Deedee, lafiya? Tunanin me kike?"
Sai a lokacin Hadeeza ta dawo hayyacin ta tare da tambayar "Magana kike yi?"
Ba dan sanin Hadeeza da tunane tunanen ta ba tabbas da Maryam zata ce rainin hankali ne.
Ya za a yi ace mutum yana tuqi kuma yana dogon tunanin da ba ya jin abinda na kusa dashi ma yake fada bare kuma yaji abinda na titi zasu ce?."Tun dazu nake miki magana naji shiru, tunanin me kike haka?"
Girgiza kai Hadeeza tayi ta amsa da "Nothing much, kawai ina tuna Abba ne"
"Abba kuma? Me kika tuna?"
Maryam tayi tambayar tare da karkata zamanta tana kallon Hadeezan da hankalin ta ke kan tuqin ta."Ina tunanin irin dadin da zaiji da ace yana raye idan aka ce mishi yau munje Bichi da kanmu ba tare dashi ba ko kuma yace mu je.
Dama yasha fada min cewa mu koyi zuwa da kanmu don watarana baya nan bare yace muje ko ya kaimu. Gashi kuwa har lokacin yazo"
Hadeeza ta fada jikinta a sanyaye zuciyar ta cike da kewar mahaifin ta don har yanzu tana jin shi a ranta tana kuma kewar shi.Ta lura dukkan abubuwan da take gudanarwa suna tafiya ne da abubuwan da Abba yake fada mata a lokacin da yana raye, kamar dai yanzu da aka ce Inna Dije bata da lafiya.
Kuma tunda ciwon ya kama ta a bichi ne gidan Gwaggo Merow dole suka je suka dubata ita da Maryam tunda Ummi bata gama takaba ba Teema kuma bata jin dadi sannan kuma shima Yaya Haidar yaje meeting lagos.Bata ta6a tunanin a rayuwar ta zata zo garin nasu su biyu ba ba tare da Abban su ba kamar yanda suka saba.
Sau dayawa ma idan zasu je da sallah ko wani taro ita bata farin ciki da zuwan har ma ta dinga qunquni.
Shiyasa Abba yake yawan mata fada akan ta saba da zumunci don watarana baya nan bare yasa su.
Ya kan kuma ce itace Babba ko babu shi dole ta sa su a gaba suje idan buqatar hakan ta tashi.
Gashi kuwa tun ba a je ko ina ba lokacin ya fara zuwa, gashi har suna zuwa duba Inna dije ba tare da iyayen su ba."Allah sarki Abba. Allah yaji qanshi da Rahma. Nasan da yana nan da shi zai kawo mu da kanshi".
Maryam ta fada jikin ta a sanyaye tare da kewar Mahaifin nata."Amiin ya Rabbi. Me kike cewa ne dazun da ban ji ki ba?"
Hadeeza tayi qoqarin canja hirar tasu don tasan idan suka cigaba zata iya fara kuka."Auu! Ai ya wuce ki. Magana nake akan dadin magarya".
Girgiza kai Hadeeza tayi tana ta6e baki tace "gara ma da banji ba, meye wani abun dadi a wannan abar? Ni kar ma ki zubar min da qwallayen ta a mota".
"Uhm! Dadin abun dai ba ni kadai nake sha ba. Har yaya Taha zan ragewa don nasan zai ji dadi sosai kuma........."
Qarar wayar Maryam ce dake cikin jaka ta katse ta daga maganar ta tare da dauko wayar don ganin wanda yake kiran.
Saidai ganin sunan "Mubarak Abdulfatah" yasa ta jan tsaki tare da katse wayar wadda aka cigaba da kira tana katsewa."Waye ne yake kiran ki kina rejecting?"
Hadeeza dake lura da yanayin Maryam din ta fada."Waye kuwa in ba wannan banzan ba?"
Maryam ta fada ranta a 6ace.
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!