🌸QADDARAR MU CE🌸🌹By Merow Masu (Sen.mersoo)
Assalamu Alaikum! Dafatan kunyi sallah lafiya. Ya haquri da zaman jiran updates😅
A cigaba da haquri dai da abinda ya samu, Allah ya bamu ikon amfana dashi.
Nagode!*16*
Alhaji musa (Baffa) yareema Bichi mutum ne dan asalin jihar kano cikin qaramar hukumar Bichi, mazaunin unguwar 'yar kasuwa. Yayi aure tunda quruciyar shi inda ya auri Khadijatul kubra wadda ta kasance itama haifaffiyar garin bichin.
Ba za a ce kai tsaye Baffa yareema ya taso cikin wadata ba, saidai ya taso cikin rufin asiri gwargwadon yanda bai rasa ci ba ko sha.
Mahaifinshi manomi ne wanda ya mutu ya bar mishi kimanin gonaki 5 cikin garin bichi dama qauyukan garin.
Ko da bayan mutuwar Mahaifin shi musa yayi amfani da wannan Albarkatun gonar wajen gina kanshi da rayuwar iyalinshi.Rayuwar Baffa yareema da khadijatu wadda aka fi sani da Dije rayuwa ce mai cike da rufin asiri da kwanciyar hankali. Cikin hukuncin ubangiji kuma Allah ya Albarkace su da 'yaya 5 a zaman su.
Mudassiru wanda ya kasance Babban d'a ga zuri'ar, Mustapha da ya kasance mabiyin shi, sai Maryama (Mero), Aliyu (Bature), sai kuma Hafsatu wadda ta kasance auta ga zuri'ar Alhaji Baffan.A iya cewa da duk wani shekaru da zuri'ar Alhaji Baffa ke qarawa a duniya, da yanayin yawan arziqin dukiyar dake qaruwa gare su.
Cikin ikon Allah kafin yaran shi su gama tasawa ya kasance daya daga cikin attajirai na cikin garin Bichin.Kasancewar shi Mutumin da baiyi ilimin Boko ba sai na islama, hakan bai hana shi bawa yaran shi damar yin karatun bokon ba har da 'yaya matan.
Saidai ya aurar da Mero ga daya daga cikin yaran da ke kula mishi da kasuwancin shi ne bayan ta kammala karatun ta na firamaren ta wanda a lokacin bata gaza shekaru 14 ba, inda yace idan tana da burin cigaba da makaranta ta iya qarasawa a gidan mijin ta.Tazarar dake tsakanin Mudassiru da Mustapha shekaru 3 ne kacal, hakan yasa suka taso tare suke makaranta tare musamman da ya kasance Mustaphan yafi yayan nashi qwazo da son karatun bokon.
Bayan kammala karatun diplomar su a FCE ne lokacin Mudassiru nada shekaru 23, inda Mustapha ke da 20, Mahaifinsu Baffa yareema ya basu damar suyi aure tunda Allah ya hore musu abinda ake buqata.Murna sosai a wajen Mudassiru ba a magana, musamman da ya kasance akwai yarinyar maqociyar su Rabi'atu da a lokacin yake qauna, don haka baiyi nauyin baki ba ya bayyana qudurin shi ga mahaifin nasu wanda yayi farin ciki sosai da hakan, shi kuwa Mustapha sam a lokacin auren baya gaban shi, burin shi bai wuce ya tafi jami'ar Bayero dake birnin kano ba don cigaba da karatun shi.
Duk da qoqarin da Dije (Innar su) tayi na ganin Mustapha ya bi sahun yayan shi yayi auren, amma sam hakan ya gagara ya nuna rashin amincewar shi da hakan.
Sanin kafiya irin ta Mustaphan yasa Alhaji Baffa ya ce a qyale shi ya nemi makarantar ya tafi, duk lokacin da yake son auren sai yayi.
6angaren Mudassiru kuwa tunda akayi auren, Alhaji Baffa ya damqa mishi wani bangare na kasuwancin shi yake kula dasu, tunda dama can shi yafi nuna qwazon shi wajen kasuwancin, bai kuma nuna yana son wani aikin gwamnati ba ko kuma cigaba da makaranta.Kwanci tashi Mustapha ya kai matakin karatun degree shi na 3, inda yake karantar fannin Electrical Engineering wanda a lokacin ne qaddarar shi ta hada shi da buzuwar yarinya Aminatu, wadda ta kasance tana kawo tallar magani irin na gargajiya.
Ba wai iya kyawu irin na Aminatu ne ya dauki hankalin mustaphan ba, kunyar ta da kamun kanta duk da qarancin shekarun ta yasa cikin lokaci qalilan ta shiga ran Mustaphan.Ya samu labarin ita din buzuwa ce, kuma asalin su mutanen garin Nijar ne saidai suna zaune anan cikin birnin kano unguwar tal'udu cikin gidan wani Attajirin mutum da mahaifin ta ke musu gadi.
Saidai sa6anin sauran yara 'yan talla, Aminatu na da nutsuwa da kuma dan guntun ilimin addinin ta, wanda ta sanar dashi tana samu ne daga wajen malamin yaran gidan mutumin da suke zaune.
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!