Chapter 8

65 9 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

By Merow Masu (Sen.Mersoo)

Salam, ya kamata na dinga ganin votes da comments.. I guess dat's d only way to support me..
                            *8*
            
A gurguje ya gama shiryawar shi kasancewar ya so ya makara gashi kuma ranar monday ce wanda period dinshi ce ta farko don haka yake ta sauri zuwa makarantar.
Ko da ya isa har an gama assembly don haka yana zuwa staff room yayi signing kai tsaye ajin da yake koyarwar ya nufa.

Tabbas da Hafeez bai zo zaria ba da bai dorar da cewa ana karatun wahala a Nigeria ba.
Duk da cewa bayan zuwan shi zarian da aka bashi makarantar a matsayin wajen aikin shi, kawun shi Alhaji Hamza ya so yayi qoqarin a canja mishi ma'aikata zuwa wani babban company.
Amma sai Hafeez ya nuna shi yana son koyarwar musamman ma tunda ta dan lokaci ce kuma zai qara samun experience.
Ko da ya fara zuwa secondary ce ta 'yan mata inda suka bashi manyan ajujuwa daga SS1-SS2.
6angaren English suka bashi, hakan kuma ba qaramin dadi ya mishi ba tunda ya iya ya kuma san bazai gagare shi ba.

Abinda Hafeez ya lura dashi tun zuwan shi makarantar shine yanda sam babu wani kyakykyawan muhalli, ko kuma ingatattun abun zama bare kuma abubuwan jin dadi irin su liluka da sauran kayan more karatu.
Sannan ya lura da malaman makarantar kowa abinda yaga dama yake yi tunda a cewar su qarqashin gwamnati suke aiki ba na wani ba.
Su kuwa daliban dama ya fahimci akwai rawar kai a tare dasu musamman yanda tun ranar shi ta farko yaga suna ta wani yauqi duk dan su burgeshi.
Dariya ma shi abun ya bashi don haka ya soma gwada su da tambayoyin abinda ya shafi karatun su.
Yayi mamaki yanda yara 'yan matakin senior ya zama ko cikakkiyar amsa da turanci sun gaza bashi bare kuma azo 6angaren lissafi da suke fanko a wannan fannin.
Ya so ace zai iya kawo gyara a makarantar ko babu komai don a samu canji a 'yan baya masu tasowa amma abun yafi qarfin shi, don haka yayi Alqawarin zai yi iya abinda zai iya ya barwa Allah sauran.

Yau ma kamar kullum ko da ya shiga ajin sai surutun su suke, inda suka kasu kashi kashi suna raha da tafawa.
Tsayawa yayi a gaban Allo ya harde hannayen shi da qirjin shi yana bin su da kallo.
A hankali suka soma ta6o juna har kowacce ta nutsu ta gyara zaman ta suna kallon shi.
Ba qaramin kyau yayi musu ba duk da yau din ba manyan kaya yasa ba kamar yanda ya saba yawanci.
sanye yake da baqin wando da jar t-shirt sai kuma wata baqar rigar sanyi da ya dora mai hula a kan rigar tashi kasancewar lokacin damuna ne kuma anyi ruwa da asuba, amma bai sa hular jikin rigar sanyin ba sai ya bar kanshi a haka wanda ya bayyana kyawun sumar da ke kanshi.
Takalmin shi kuwa zasu iya cewa irin wadannan masu zubi da na turawan ne da suke sawa kamar canvas.
Duk da cewa sun saba ganin Hafeez din cikin shiga iri iri ta 'yan gayu wanda har ta kai ga sun sa mishi suna a bayan idonshi wai "Malam gaye", amma hakan bai hana su ganin kyawun shi ba a ranar ma.

Sai da ya tabbatar duk sun nutsu sannan ya gaishe su suma suka gaishe shi aka fara darasi.
Duk da kasancewar Hafeez mutum mai sakin fuska, lura da yanayin yaran da kuma wasan su yasa ya kan ci magani don haka sai ya zama suna shakkar shi, kuma ya kan saki fuska a yi raha na wani dan lokaci idan yaso.
Ko da period dinshi ta qare fita yayi bayan ya basu assignment inda suka dora gulmar irin gayu da kyau irin nashi. A haka dai har wani malamin na gaba ya shiga.

Ko da ya fita sauri yake ta yi don ya samar wa kanshi abinda zai ci tunda bai karya ba ya fita gashi kuma shi bai saba zama da yunwa ba.
Fitowa yayi bakin gate din da niyyar ya tafi wajen wani mai shayi dake kusa da makarantar amma sai idonshi ya sauka akan wata yarinya daga cikin masu tallar dake zama a bakin gate din makarantar tana zubawa wani gurasa bandashe a leda.
Abinka da mai jin yunwa gashi kuma mayen gurasa don haka yaji zuciyar shi na umartar shi da ya qarasa wajen.
Duk da cewa ya saba ganin ta a wajen da fantekar ta, bai ta6a lura da abinda take siyarwa ba bare ma ya tsaya ya siya.

Qarasawa yayi ya sameta a zaune ta duqar da kai cikin atamfar ta mai ratsin blue, ta kuma sanya hijabin ta yadin moris blue wanda ya sha guga shima, sannan qafarta dake ta sheqin mai dauke da bathroom silipas mai kyau.
Duk da cewa yarinyar baqa ce hakan bazai hana ka fahimtar mai tsafta bace, don haka sai yaji hankalin shi ya kwanta da cin gurasar.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now