🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*35*
Kano city, 2020.
Ta dade da sanin rasa su tamkar rasa wani bangare ne na rayuwar ta.
Ta dade da sanin su din wani sashe ne na rayuwa da farin cikin ta.
Ta dade da fidda rai da samun wannan farin cikin, ta kuma dade da fadawa kanta cewar ta riga da ta rasa su din har abada.Saidai a yanzu da take ganin su kusa da ita, a yanzu ta kasa gasgata cewar rayuwa ta qara bata damar sake ganin su.
Ta kasa gasgata cewar itace zaune cikin su cike da walawala da farin ciki haka.
Ta kasa gasgata cewar dukkannin su sunyi kewar ta haka."Deedee mana, muma fa duk muna so mu dauki babyn nan. Kin qanqame ta kin hana kowa".
Teema ta fada a shagwa6e, wanda hakan yasa Hadeeza kallon jaririyar dake hannun ta, tare da maida kallon ta ga Teema.
Ta yarda abubuwa da dama basa canjawa, ciki kuwa har da ta6arar Teema.
Shekaru bakwai kenan, shekaru bakwai da barin ta da wannan shagwa6ar, saidai ta lura a jinin Teeman ne, bazata daina ba duk da cewar ta qara girma.
"To kema ai kin dauke ta Teema, ko kuwa mai da ta cikii zakiyi ki sake haifo ta?"
"Ummi mana... ni fa bata dade a hannu na ba kamar Deedee".
Hararar da Ummi ta aikawa Teeman ya sa Hadeeza dariya.
Tayi kewar su sosai, tayi kewar wannan dramar tasu.
Saidai tasan da a baya ne babu abinda zai hana Ummi saka ta ta bawa Teema Babyn, amma a yanzu ta kasa sabawa da yanda Ummi ke lalla6ata cikin awannin nan.
Yanda take qoqarin kiyaye duk wani abu da zai 6ata ran Hadeezan, yanda tun zuwan su asibitin take riqe da Mahmoud da a baya ta tsane shi tun baizo duniya ba.Saidai abinda bata sani ba Ummi na kiyaye duk wani abu da tasan zaiyi silar sake komawar ta inda ta fito ne.
Ita kadai tasan halin da ta shiga bayan barin Hadeezan cikin rayuwar ta, don haka bazata bari ta qara wani kuskuren da zai sa ta bar ta ba."Yauwa Angon qarni, kaga Deedee ta hana ni riqe Babyn nan tun dazu".
Harara Taha da shigowar shi kenan ya aikawa Teema.
"Lallai yarinyar nan kin raina ni dayawa, nine angon qarnin?".
Sai a lokacin Hadeeza ta daga idanun ta ta lura da Tahan, sam bata ji shigowar shi ba.
Zata ce rabon da ta ganshi tun lokacin da suka iso asibitin da aka sanar dashi zai saka hannu cewar za a yiwa Maryam CS.Shi ya aiko nurse akan ta bude musu office dinshi su zauna su jira tunda sunqi tafiya gida.
Ko da aka ciro Babyn ma ba shi ya kawo musu ba, wata nurse ce ta kawo musu yarinyar, ta kuma sanar dasu Maryam din bata farfado ba tukunna.Sai da Hadeeza ta kalli Tahan ta maida kallon ta da yarinyar ta tabbatar da suna kama.
Duk da cewa kuwa Ummi tace hancin dai na Maryam ne.Abu daya dai ta sani shine me yiwuwa tana jin son jaririyar a ranta sosai ne saboda kasancewar ta jinin Taha da Maryam, don kuwa zata rantse ko a lokacin da ta haifi Mahmoud bata ji soyayyar shi farat daya ta ratsa zuciyar ta kamar haka ba.
A kallon farko taji qaunar yarinyar ta shiga ran ta, shiyasa tunda aka damqa mata ita ta kasa bawa kowa ita ta qanqame ta.
"Bashi ita ya dauke ta, me yiwuwa shima ko riqe ta baiyi ba"
Muryar Ummi ta katse ta daga tunanin ta.
Zama yayi daga gefe kan doguwar kujerar da Hadeezan ke zaune, sannan ta miqa mishi ita.
![](https://img.wattpad.com/cover/146407140-288-k405691.jpg)
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
General FictionLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!