Chapter 9

77 4 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

By Merow Masu (Sen.Mersoo)

Salamu alaikum ma'abota karanta littafin "Qaddarar mu ce" nasani nayi Alqawarin updating a kan lokaci ba tare da kun qosa ba. Saidai dan Adam ba a rasa shi da uzuri na yau da kullum.
Don haka ina mai baku haqurin cewa bazan samu damar yin updates akai akai kwanakin nan ba.. Amma inshaa Allahu da zarar na gama za'a koma yanda na saba yin updates kwana biyu zuwa 3.

A shaqata da wannan yanzu😅              
                             

                               *9*

Tun daga wannan ranar da Hafeez ya siya gurasar Aysha, sai ya zama kullum yaje makaranta sai ya biya wajen nata, ko da bazai ci ba dai yakan je ko dan yaci dariyar wautar ta.
Ya lura itama Ayshan ta saki jiki dashi don har ta kan bashi labarai akan abinda ya shafi Innar ta da Baban ta da ma gidan nasu baki daya.

A cikin labaran Ayshan ta fada mishi su mazauna unguwar Hanwa ne da ke nan cikin zarian, ta sanar dashi cewa Innar ta 'yar kano ce a can unguwar jakara, a cewar ta innar ta ta ma gadon iya gurasa tayi tunda itace sana'ar da akeyi a gidan su.
Daga labaran nata ya fahimci Innar Aysha ba ita kadai ce mata a wajen baban su ba, Ayshan kuma ta sanar dashi cewa Gidan da suke a yanzu innar ta ce ke biya tunda ta bar gidan da sauran kishiyoyin suke.
Duk da bata fito fili ta fada mishi ba amma ya lura sam mahaifin su Ayshan bai damu da lamuran su, ya sakar wa matanshi ragamar wahalar gidan shi, shine ma dalilin dayasa ya gaza barin yaran su cigaba da karatu saidai iyayen su su dora musu talla don a samu abinda za a rufawa kai asiri

Abinda yake bawa Hafeez din tausayi shine yanda ya lura Ayshan na matuqar son karatu.
Abinda kuma yake bashi mamaki yanda  yarinyar bata ta6a tambayar sunan shi ba duk da wannan sanin da yayi mata.

Ya lura tana da tsiwa, don tasha yin rashin mutunci idan taga mutum zai cuce ta, amma shi kam bata ta6a yi mishi ba saidai a wasa.
Ya kuma fahimci Ayshan yarinya ce mai tsafta, kwalliya da kuma son ado, saidai bata da kayan aikin gayun.

Sau tari idan yaje siyan gurasa hirar ta akan makarantar da tayi firamare ne ko kuma akan mustyn ta.
Shi kam har mamaki take bashi idan tana hirar saurayin nata, ya kan tsaya ya tsura mata ido a ranshi yana mamakin irin saurayin da zaije ya 6ata lokacin shi wajen yarinyar da bata wuce a ce tana aji ba.
Amma abinda yafi bashi mamaki shine yanda take matuqar son Mustyn nata, har ma Alqawari tayi wa Hafeez kan zata hada shi da mustyn su gaisa.

Wata ranar Alhamis Hafeez da wata abokiyar aikinshi Blessing wadda itama corper ce a makarantar suka je wajen Ayshan siyan gurasa.
A zaune suka same ta sanye da wata baqar doguwar rigar Abaya ta gumama taci uban rolling da wani yellown mayafi mai arha.
Karkada qafar ta kawai take tana tunanin da ita kadai tasan abinda take tunawa.

Ganin su Hafeez ne yasa ta sakin fuska tun kafin su qaraso sanin cewa zata yi ciniki.
Da fara'a Hafeez yayi mata sallama ta amsa mishi ita ma da fara'a tana tambayar shi ta nawa za a sa mishi.
Sai da ya juya ya kalli Blessing dake tsaye wadda sam bata jin Hausa bare taji me suke cewa, ya tambaye ta ko zata ci da harshen turanci.
Amsa mishi tayi da ta qoshi ita doya take son ci.
Girgiza kanshi yayi yana dariya don shi mamakin cin doya irin na Blessing yake.
Sai da ya gama dariyar tashi sannan ya maida kallonshi ga Aysha.

Da mamakin shi bakin ta a sake yake tana bin su da kallo.
Har Hafeez yayi magana yacewa Ayshan ta zuba mishi ta 150 a leda hankalin ta baya kai.
Hakan yasa shi tafa hannayen shi sannan Ayshan ta maida kallonta gare shi.

"Tunanin me kike indon inna?" Hafeez ya fada cikin sigar tsokana.
Da mamaki take kallon shi tace "Dama ka iya turanci haka?"
Wata dariya Ayshan ta bashi, a ranshi yace yanzu duk wannan sakin bakin na jin turanci ne?.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now