Chapter 31

41 4 3
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                             *31*

Kano city, 2013.

Duniya abun tsoro, Allah abun tsoro, kuma mutuwa ma abun tsoro.
Yanda dan Adam ya ke kwana ya tashi da sanin cewa zai mutu watarana, hakan baya hana mu mamaki ko jimamin mutuwar wasu.
Tun muna jin ta a gari, muna jin ta a maqota, har watarana yazo kan makusantan mu wadanda muke qauna da dukkan ran mu.

Yanda duk tunanin mai tunani zai yi tunani, cikin duniyar mu baki daya babu wanda zai iya siffanta irin yanayin da Hadeeza ke ciki game da mutuwar Mahmoud.

A tunanin ta ta gama sanin wani zafin mutuwa bayan rasuwar Abba, saidai tayi tunanin ne cikin rashin sani, domin bata ta6a hangowa ko a mafarkin ta cewa zata sake rasa wani nata a kusa ba, ballantana kuma dan uwanta shaqiqin ta mafi soyuwa a zuciyar ta.

Mutuwar Mahmoud ta daki Al'umma da dama, musamman zuri'ar su, da maqota da ma abokanan shi, kasancewar shi mutum na mutane mai cike da barkwanci da qaunar kowa.

Hadeeza kam ba iya dukan ta mutuwar tayi ba, baki daya ta ta rayuwar ta ta6a.
Ta yanda take ganin Mahmoud din ya tafi da duk wani dadin duniya da take ganin zata samu a gaba.

Kwanaki biyar kenan da mutuwar Mahmoud din, saidai cikin kwanaki biyar din nan kowacce rana tana zuwar mata da wani sabon ciwon ne a madadin taji wani sauqi a zuciyar ta.

Duk yanda taso ta fadawa kanta cewa Mutuwar Mahmoud qaddarar su ce, hakan ya gagara shiga qwaqwalwar ta ta amince dashi.
Gani take yi tamkar itace silar mutuwar Mahmoud din, tamkar ita taje ta kade Mahmoud din.

A ganinta da bata hadu da Mujaheed ba, da bata bashi dama ba, da bata saida mutuncin ta ba, da yanzu Mahmoud yana raye cikin walwala da fara'ar da ya saba.

Ta sani cewa ta aikata laifuka da dama a rayuwar ta, saidai mutuwar Mahmoud na daga cikin laifukan da bazata iya yafewa kanta ba.

"Mahmoud ya rasu, Mahmoud bazai dawo ba".

Shine abinda ko da yaushe take furtawa kan ta. Amma a duk lokacin da ta fadawa kan nata haka don samun nutsuwar ta, wani sabon kuka da baqin ciki ne yake dada lullu6e ta.

Ta yarda a duniya Mahmoud na daga cikin masu qaunar ta fiye da yanda take son kan ta, ta yarda Mahmoud zai iya komai don samun farin cikin ta.
Tun suna yara yake nuna hakan, tun suna qanana yake fifita ta fiye ma da Maryam da ta kasance tagwayen shi.
Saidai bata san soyayyar da yake mata ita zata zama ajalin shi ba, bata san cewa maganganun da yake fada mata kan sai ya nemo Mujaheed gaskiya bane.
Gashi yanzu bai nemo Mujaheed ba Mutuwa ta nemo shi, ta kuma aika shi inda ba a ta6a dawowa.

Shigowar Teema da sallamar ta cikin daki ita ta katse Hadeeza daga tunanin ta, har ma ta maida kallon ta ga Teeman dake riqe da plate din abinci.

"Ga abincin ki, naga tun safe baki fito kinci wani abu ba".

Teeman ta fada tana dire plate din abincin a gefen gado.

Kallo Hadeeza ta bi ta dashi kawai, zuciyar ta na tuna mata da Mahmoud da a kullum cikin hidimta mata yake.

"Deedee kin ci abinci?
Me zaki ci?
Me kike so?
Me zan taho miki dashi?
Ko na dafa miki da kaina?"

Ire iren wadannan tambayoyin na Mahmoud na dawo mata kunnuwan ta.

Shi kadai ne, shi kadai ne bai ta6a nuna qyamar ta ko cikin dake jikin ta ba. Sai kuma Teeman.
Shiyasa ko a ranar da zai mutu a hanyar su ta dawowa daga asibiti sai da ta tambaye shi.

"Mahmoud wai kana manta cikin nan dake jiki na ba na halak bane? Me yasa kake damuwa da lafiyar shi?"

Murmushi kawai yayi yana tuqi, kafin daga baya ya amsa mata da "ko wanne iri ne ma ai a jikin ki yake rayuwa. Idan har lafiyar shi zata ta6a taki dole mu kiyaye hakan.
Kuma don Allah Deedee ki daina fadar cikin nan ba na halak bane, idan yaron nan yazo duniya yaji hakan daga bakin ki bazai ta6a mantawa ba".

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now