🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*23*
Kano city, 2012.
Kwance take a kan gado tana karanta wani littafi mai suna "Strange love" taji qarar wayarta dake kusa da ita.
Hannu tasa ta dauka tana mai duba sunan wanda ya kira din.
"Mujaheed Deen" ta gani a kan screen dinta don haka ta dauka da murmushi a fuskar ta tana fadin "Mutanen lagos".
Murmushi yayi daga daya bangaren wanda har sautin shi sai da ya fito yace "Eh da alama ciwon kan yayi sauqi tunda har kina zolaya ta.
Ya kike? Ya gida? Ya jikin?".Hadeeza dake kwance sake gyara kwanciyar ta tayi tace "Ah naji sauqi fa, dama stress ne kasan naje clearance na NYSC. Amma yanzu kam Alhamdulillah ya daina.
Ya kke? Ya lagos din? Tana maka dadi dai ko?"."Kaii ina fa wani dadi, dadi ai sai ku Ajebo kuna gida hankalin ku kwance. Mu kuwa da muka tafi hustling ina maganar dadi. Amma Alhamdulillah, it's not that bad".
Murmushi Hadeeza tayi tace "ka dai ji dashi. Yaushe zaka dawo ne?".
"Ehwooo, somebody misses me?"
Mujaheed din yayi tambayar cike da zolaya.Harara Hadeeza ta watsa mishi duk da tasan a waya ne ba ganin ta yake ba tace "Allah shi kyauta, surutun zanyi missing?"
"Dadin Abun dai surutun ba ni kadai nake yi ba da ke muke yi"
Mujaheed din ya amsa yana dariya.Girgiza kai kawai tayi tace "Deeni ko ba mai taya ka surutu zakayi da bango ko bishiya"
Wata dariya yayi daga dayan bangaren yace "Eh lallai Dije kin raina ni. Lalacewar tawa ta kai haka?"
Itan ma dariyar tayi tace "Ai ta ma wuce""Ai shikenan, dama i just called to check up on u, sai anjima zan sake kira. kuma daga yanzu murya ta tsada zata dinga miki har sai kin roqe ni nayi magana naqi".
Dariya Hadeeza tayi sanin cewa bazai ta6a iya hakan ba, don haka tace "we shall see"
"Eh din! Bye bye"
Mujaheed din ya fada yana kashe wayar.
Ita din ma ajiye wayar tayi tana murmushin da bata san takamaimai na menene ba, saidai zata iya cewa na farin ciki ne da take ciki kwanakin nan.Kimanin sati uku kenan da Haduwar Hadeeza da Mujaheed a park bayan rasuwar Abba, kimanin kuma sati hudu kenan da rasuwar Abban.
Zaman Hadeeza da Mujaheed a park wannan ranar ya basu damar fahimtar junan su sosai da kuma sanin damuwar junan su, ya kuma zama silar kasancewar su Abokai masu kusanci kamar yanda suke kiran junan su.Daga labarin da Hadeeza ta samu wajen Mujaheed a wannan ranar, ta fahimci cewa ya rasa iyayen shi biyu shekaru goma da suka wuce wanda a lokacin da sauran quruciyar shi kuma ko makaranta bai gama ba tunda duka duka shekarun shi basu wuce 28 ba a yanzu.
Ta kuma fahimci cewar mutuwar iyayen shi ta sa ya rasa duk gatan da yake dashi a wancan lokacin musamman tunda dangin uban shi sunyi handama da baba kere da dumbin dukiyar da aka bar mishi wanda hakan ya jefa shi cikin wahalar da ta sa shi dole ya iya neman kudin da ya cigaba da karatun shi, a qarshe ma kuma ya bar garin nasu maiduguri ya dawo kano inda yake cigaba da gudanar da kasuwancin shi tsakanin kano, lagos, cotonou da ma qasashen waje kamar yanda ya sanar da ita.A cewar shi Mahaifiyar shi irin sadakar yallan nan ne, mahaifin shi kuma haifaffen garin maiduguri ne kuma dangin shuwa arab, hakan yasa Hadeeza tabbatar da yanda akai ya kasance fari kuma kyakykyawa ko ma balarabe kamar yanda Teema ta ce a ranar da yaje musu gaisuwa.
A 6angaren sana'a kuma ko da Hadeeza ta tambaye shi ya fada mata yana harkar sai da motoci ne sababbi da wadanda akayi amfani dasu da kuma harkar kayan motocin kamar su engine motar, battery da sauran su.
Hakan ya sa Hadeeza gamsuwa da yanda take ganin shi da motoci kala kala wanda yace mata ko ya siyi mota da minti daya ne wani ya gani yana so zai siyar mishi tunda sana'ar shi ne.
ESTÁS LEYENDO
QADDARAR MU CE
FantasíaLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!