Chapter 6&7

87 6 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                       *6&7*

Daga shi Har Dr.Ma'aruf bazasu iya cewa ga Adadin lokacin da Hafeez ya dauka yana kuka kanshi a kife ba. Shi kanshi Ma'aruf din taya shi kukan zuci yake. mamaki yake da tunanin idan har hakan ce ta tabbata wannan wacce iriyar mata ce.
Wacce iriyar mata ce mara godiyar Allah da zata samu namiji kamar Hafeez har ta fita neman wani duk da tasan irin tarin zunubin da hakan zai haifar.
Shi kam wasu matan har ma da mazan aure masu neman na waje bazasu ta6a daina bashi mamaki ba.
A ranshi yayi addu'ar Allah ya shiryasu baki daya, sannan ya mayar da kallonshi ga Hafeez.
A hankali ya dan ta6a kafadar Hafeez din yace "Hafeez ya kamata ka bar kukan nan ka tashi haka, abinda ya kamata shine a fara sanin inda matsalar take. Bansan ya kakeji a ranka ba domin ni kaina ina taya ka wannan alhinin, saidai zan baka shawara kuma in tunatar da kai abinda Addini ya koyar damu.
Kada ka kuskura ka yanke hukunci ba tare da bincike ba, sannan kada ka yanke hukunci cikin fushi. Zai iya yiwuwa Ayshan ce, zai kuma iya yiwuwa sa6anin hakan ne. Beside, ita fa cutar nan ba wai dole sai ta hanyar saduwa ake dauka ba. Ko ta sharp objects dinnan ma ana iya dauka. Don haka please ka nutsu kafin ka yanke hukunci. Kuma Alhamdulillahi ma yanzu don mutum yana da cuta kamar wannan yana iya cigaba da rayuwar shi tayi tsawo ma fiye da wanda bashi da ita. Allah dai shine mafi sanin adadin kwanakin kowa a duniya."

Dago kanshi yayi yana kallon Ma'aruf din da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa.
Yaso ace Ma'aruf din yana jin abinda yake ji, tabbas da zai adana kalaman shi ne zuwa lokacin da zai dawo Hayyacin shi. Amma duk da haka bai watsa mishi qasa a ido ba sai yayi alamar da kanshi cewar ya gamsu yace "Haka ne, ni bari in tafi nagode" ya fada yana qoqarin miqewa ya fita.

A daidai lokacin da yake qoqarin fita a daidai lokacin Hadeeza ta turo qofar office din.
Bata san ma yana ciki ba, ba kuma tasan ma yazo asibitin ba. Zuwa tayi don ta ari charger Doctor Ma'aruf sakamakon tata da ta manta a gida, ta kuma za6i ta karbi tashin ne tunda shi tafi sabawa dashi a asibitin.

Kallon Hafeez take da rinannun idanunshi da ko ba'a fada mata ba tasan yasha kuka tace "Lafiya? Me ya faru kake kuka?"
Shiru yayi mata bai amsa ba bai kuma yi yunqurin fita ba.
Sake maida kallon ta tayi ga Dr. Ma'aruf da tun shigowar Hadeeza ya miqe tsaye tace "Me ya faru Doctor? Shima gwajin nashi ba a dace ba?"
Basu amsa mata ba sai ma kallon juna da sukayi.
Hakan yasa ta fashe da kuka a ranta ta qiyasta lokacin mutuwar Mahmoud ne yayi, don haka ta dora Hannuwan ta a ka ta tane cewa "Shikenan mun rasa Mahmoud"

Hafeez ma kukan yaji yana shirin sakko mishi.
Ya sani cewa a yau bashi da kalaman da zai iya rarrashin Hadeezan bare kuma ma yasa ta tayi shiru.

Shirun da sukayi yasa ta qara sautin kukan ta tana cigaba da fadin "Shikenan Mahmoud na rasa ka"

Bata yi zato ba sai kuma taji muryar Hafeez shima cikin kuka yace "Baki rasa Mahmoud ba Hadeeza, Amma na rasa ki. Na rasaki Hadeeza"
ya fada da wata iriyar murya mai rauni ya fice da sauri yana banko qofar da qarfi.

Zata iya cewa dena motsi tayi na wasu mintina. qwaqwalwar ta taji ta cika sosai da bazata iya wani tunani ba.
Ji tayi qafafun ta kamar sun daina daukar ta ma don haka ta nemi kujerar da ke mafi kusa da ita ta zauna.
Sosai Ma'aruf ya lura da yanayin ta, ya kuma san dole zuciyar ta tana raya mata wasu abubuwan ne da zasu cutar da lafiyar ta, don haka yayi saurin katse tunanin nata da cewa
"Hadeez ki kwantar da hankalin ki, ba wani abun damuwa bane, kawai dai Hafeez yana ganin kamar rashin dacewar zaisa kiga ya gaza ne"

Duk da cewa shi ba ma'abocin qarya bane amma yasan a irin wannan lokacin kowa yana buqatar wannan qaryar. Baya ga haka ma shi likita ne bazai so abinda zai cutar da ita ba tunda yasan ba lafiya gareta ba.
"Me ya faru ma kika zo? Ko jikin Mahmoud din ne?"
Ma'aruf din yayi tambayar yana kallon Hadeeza da taqi cewa komai.
Sai da ta goge fuskar ta da gefen mayafin ta sannan tace "Ehh dama charger ka nazo ara idan ba damuwa, tawa tana gida."
Bai ce mata komai ba kawai ya zaro mata charger daga jikin socket ya miqa mata, ita kuma ta amsa tana godiya ta tashi ta fice.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now