Chapter 30

49 3 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                             *30*

Kano city, 2013.

Ta sha jin mutane na cewa baka isa ka guje ma qaddara ba, ko kuma ma ka canja ta, Saidai bata ta6a gamsuwa da hakan ba, a ganin ta wasu lokuttan dan Adam yana da ikon kaucewa qaddarar shi, ya tsallake ta ko kuma ma ya canja ta.
Saidai a cikin watannin nan, a ranakun nan, a yanzun nan da take riqe da tata qaddarar a hannun ta ta yarda ta amince, ta kuma tabbatar da tsawon lokacin nan yaudarar kanta take tunda ta kasa tsallake ta ta qaddarar.

"Kuka yake yi, ki bashi abinci mana".

Jajayen idanun ta ta daga tana kallon Tahan dake zaune a gefen gadon asibitin da take, yana maida kallon shi ga jaririn da har yanzu ta kasa dora idanun ta a kan shi duk da tana riqe dashi a hannun ta.

Lokuta da dama a shekarun baya tasha mafarkin rana irin wannan, ranar da zata haihu taga Taha da jaririn ta a dakin asibiti kamar haka, saidai mafarkin nata yazo da gaskiyar abinda bata ta6a hasashe ba ko kuma ma tayi fata a ran ta.

Tsawon watannin nan da tayi da cikin a jikin ta wannan ranar take gudu, ranar da za a ce gashi ta haifo dan da kuskuren ta ya sa ta same shi, ranar da za a ce ta haifo dan Mujaheed, mutumin da bata jin ko a mafarkan ta zata sake ganin shi.

Shiyasa tun daga ranar da tasan da cikin tayi qoqarin raba kanta dashi, shiyasa ko a ranar da ta san da hakan kai tsaye da ta fita gidan su zainab qawarta ta dosa.

Bazata ce ga adadin lokacin da ta dauka wajen yiwa zainab magiya akan ta taimaka mata a san yanda za a yi a zubar da cikin, ba wai don zainab din likita bace, ko kuma don ta ta6a zubar da ciki ba, ta dai zo wajen ta ne saboda ita kadai ce qawar ta, qawar da ta san zasu kashe su binne tare ta taimaka mata.
Saidai da fari zainab ta nuna mata illar hakan, ta kuma turje akan tunda mai faruwa ta faru kawai suyi haquri su jira abinda hali zaiyi, mai yiwuwa Allah zai dube su cikin ya 6are dan kan shi ko kuma ma ta haife shi ba rai su huta.

Amma saidai Hadeeza ta nace, kuka da magiyar da ta dinga yiwa zainab yasa zainab din ta dauke ta zuwa gidan wata 'yar unguwar su wadda bazawara ce dake zaman kan ta, ta yi fice wajen sanin irin wadannan harkokin don haka suka je don ta basu shawara ko ma ta kai su inda za a zubar da cikin.

Kasancewar suna dasawa da zainab sosai yasa bata 6ata lokaci ba bayan sun mata bayani ta daga waya ta kira likitan da tasan yana aikin, inda yace suje asibitin shi su same shi.

Ko da suka je likitan ya gwada Hadeeza, ya kuma ga cewar jinin ta ya hau, sannan bata gama murmurewa ba don haka ya fada musu cewar akwai gagarumar matsala idan sukace zasu zubar da cikin a lokacin, saidai ko su bari sai ta qara samun sauqi.

Magiya da kukan dai Hadeeza ta cigaba da mishi, a cewar ta babu damuwa ko da zata rasa ranta ne ma ayi, daqyar zainab da Zuzu qawar zainab din suka fitar da Hadeeza daga asibitin.

Ganin yanda hankalin Hadeeza ya tashi ne yasa Zuzun basu shawarar suje ta rakasu inda za a kar6o na Hausa, ta kuma tabbatar da yardar Allah indai kasha bazaka sake kwana da cikin ba, saidai akwai azaba mai yawa shiyasa ma bata kawo musu shawarar hakan ba tun farko.

Yanda zainab taga Hadeeza ta dage yasa ba don son ranta ba aka je aka kar6o maganin nan, inda aka hadawa Hadeeza tasha ta tafi gida, da fatan cewa cikin zai zube kafin wayewar gari kamar yanda mutumin ya fada musu.

Da nutsuwar ta ta koma gida, musamman da ya kasance zuzu qawar zainab ta qarfafa mata gwiwar cewa abu ne da aka saba, zuzun ta sanar da ita cewa ta kai mutane sunfi a irga kuma an dace don haka ta kwantar da hankalin ta kamar cikin ya zube ma, shiyasa ko da taje gidan ta wuce dakin ta tayi sallah tare da roqon Allah da ya bata nasarar zubar da cikin, sannan ta koma gadon ta ta kwanta.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now