*QADDARAR MU CE*
🌹 By Merow Masu (Sen.Mersoo)
***Da sunan Allah mai Rahma mai jin qai***
Bai kasance labarin da na fara qirqira ba, Bai kuma kasance labarin da na fara rubutawa ba, saidai shi din labarin "QADDARAR MU CE" ya kasance labari na farko da zan fara posting online. Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfane ni da ku baki daya.
Me yiwuwa a samu kuskure, ko a wajen typing ko kuma shi kanshi labarin, Amma na tabbatar zanyi iya qoqari na na isar da saqon.
*1*
Zaune take a kujerar dake gefen gadon mara lafiyan dan nata wanda yake kwance tamkar gawa.
Ta zuba uban tagumi, ga kuma aikin buga qafafun ta da take cikin tsananin tashin hankali da tunanin abinda ya faru da kuma wanda yake shirin faruwa.kwana 3 kenan yau da kawo dan nata tilo mahadin rayuwarta asibitin wanda shi kadai ya rage mata da zata kira ko tayi tunkaho da sunan nata a yanzu.
ta sani cewa tunda ta haifi Mahmoud bashi da lafiya, ta sani cewa tunda ta haifeshi basu taba cikakken sati 4 basu ziyarci asibiti ba tsawon shekaru 6 a halin yanzu, ta sani cewa tun a shekarun da suka gabata an tabbatar mata da ciwon Mahmoud na da nasaba da matsalar kodar da yake fama da ita wato "kidney failure", ta kuma sani ciwon nashi ya kai matakin "Chronic kidney injury" a yanzu. Amma abu daya da ke qara firgita ta shine tsawon shekaru shidan nan Mahmoud bai taba shiga halin da yake ciki a yanzu ba, Infact bai ma taba sumar da ta gaza Hour bai farfado ba bare ace har tsawon kwanaki 3.Rashin farfadowar mahmoud bashi ne kadai abinda yafi damunta a yanzu ba, bayanin da Doctor Ma'aruf yayi mata mintina ko ince Awannin da suka wuce kafin dawowar ta dakin shine ya qara tsunduma ta cikin halin da take ciki.
Dr Ma'aruf wanda ya kasance likitan da ke ganin Mahmoud tsawon wani lokaci kawo yanzu, shi ya aika mata da saqo ta hanyar wata nurse akan ta same shi a office tun wayewar gari sanin cewa yana ta kiranta a waya ba a dauka.
Hakan yasa bayan tayi sallar asuba ta tafi gida domin dauko wasu kayayyakin har ma da wayar ta da ta bari a gidan tun ranar da ta kai Mahmoud din asibiti.
Ta kuma samu damar yin wanka da wasu abubuwan da ba a rasa ba don kuwa tun ranar da suka zo asibitin ba ta samu nutsuwar hakan ba.Ko da ta koma asibitin kayan ta kawai ta ajiye a dakin ta nufi office din likitan don jin dalilin kiran nashi.
Idan Hadeeza tace zuciyar ta bata buga ba bayan ganin adadin missed calls dinshi a wayarta tayi karya, domin ta tabbata da Alheri ne babu abinda zai Hana Dr Ma'aruf din zuwa har inda take don ya sanar mata.
Zaton nata ne kuwa ya tabbata bayan ta gurfana a ofishin nashi sanda ya fara mata bayani."Malama Hadeeza, kamar yanda na gaya miki tun kwanakin nan da suka wuce cewa ba za a iya daukar kodar (kidney) ki ko ta wani ba ba tare da anyi wasu gwaje gwaje ba kika nutsu kuma kika yi hakuri har aka yin, a yanzun ma nutsuwar ki nake buqata domin sanar dake halin da ake ciki bayan anyi gwajin".
Wannan kalaman sune bayanan farko da Ya fito daga bakin Dr Ma'aruf bayan kimanin mintina 3 da suka yi ba tare da suncewa juna komai ba sa6anin gaisuwar da ta shiga tsakanin su.Hadeeza dake zaune a kujerar dake fuskantar ta Dr Ma'aruf din ne ta sake gyara zaman ta sannan ta kafe shi da manyan idanunta tace "kamar yaya kenan Doctor? Akwai wani abu kuma da ba a yi min bayanai ba ne kuma a baya? maganar gaskiya ni kam na gaji da tsurfar ku a asibitin nan, yaro na yana kwance yau kimanin kwanaki 3 kun kasa mishi abinda ya dace kuna maganar wani gwaje gwaje, yanzu kuma anyin kana kokarin kawo wani abun kuma? meyasa tun da can ba a fada min akwai wani abu da yayi saura ba?."
Har ga Allah zuciyar ta kawai ta bata wani gwajin ne ko kuma wata matsala ta kudi ce ta sake tasowa don haka dole abun ya bata mata rai.Girgiza mata kai Doctor yayi sannan yace "Shiyasa nace ki nutsu na miki bayani Hadeeza, u need to calm down plz"
"Ka fada min da sauri Doctor, kafin zuciya ta ta daina Harbawa."
Hadeezan ta fada tana kokarin goge kwallar dake yunkurin zubowa daga kyawawan idanunta da a yanzu damuwa da kuka suka dusashe su.
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!