Chapter 37

48 6 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                                *37*

Canada, 2021.

Kamar kowanne dangi dake wajen, su din ma zuciyoyin su cike suke da farin cikin ganin 'yar uwarsu cikin jerin daliban da suke sanye da rigunan kammala makaranta (graduation gown).
A cikin idanun su da fara'ar su zaka fahimci tsantsar farin cikin da suke taya ta, saidai a qarqashin zuciyoyin su kewa ce ta mutane masu muhimmanci daga rayuwar su.
Mutanen da rashin su ya kasance musu Babban ciwon da suka kasa samun maganin shi bare su warkar dashi.

Haqiqa kamar kowa mutuwar su Maryam bata yanke tasu rayuwar ba, saidai babu shakka ta ta6a rayuwar su fiye da tunanin mai tunani.
Haka kuma kamar kowa a yau din ma, farin cikin su ga nasarar Teema bazai misaltu ba.

Ganin autar Ummin cikin jerin daliban likitanci da makaranta ta yaye buri ne da dukkannin su suka dade da taya ta dakon shi a zuciyoyin su.
Ganin ta cikin daliban da suka samu lambar yabo ta jajircewa wajen karatu nasara ce da basuyi hasashen ta ba.
Shiyasa hakan ya kasance abun alfahari a garesu, shiyasa kuma hakan ya sanya musu farin cikin da ya danne kuma yake sosa musu wani baqin ciki na zukatan su.

"Congratulations Tim tim, I'm soo soo proud of u".

Hadeeza ta fada rungume da Teeman a lokacin da aka kammala taron.

"congratulations! Dr fateema Mustapha yareema.
Ina taya ki murna matuqa"

Jiddah ta fada rungume da Teeman, dauke da murmushi a fuskar ta.

Teeman ma murmushin ta mayar mata, tare da fadin "Thank u sisy".
Sannan ta maida kallon ta ga Haidar.

"Wai yaya baka ganni bane? Shine ko magana ma babu?".

Ta qarasa maganar tare da turo baki kamar yanda ta saba.

Hakan yasa su duka dariya, Haidar kuwa qarasawa yayi gaban ta tare da rungume ta ta gefe.

"Congratulations autar Ummi, so nake ku gama tukunna ai. Ni na isa naqi kula babbar likita kamar ki? Wane mutum?"

Girgiza kai Teeman tayi tana dariya,

"Kai yaya? Abun naka har da zolaya?"

Dariya sukayi su duka, kafin Teema ta soma waige waige.

"Wai ku tsaya, dama ku kadai ne? Ina kuka baro Yaya Taha da little?"

Kallon kallon su Hadeeza suka soma, lokaci guda suka canja fuska da har sai da Teeman ta tambaye su ko lafiya.

"So sorry Teema, basu samu damar zuwa ba. Mu uku mukazo garin ai.
Amma dai ya aiko da saqon fatan alheri".

Kallon su Hadeezan Teema takeyi da alamar tambaya, so take su tabbatar mata da abinda Jiddah take fada mata, don kuwa idan har gaskiya ne to murnar ta zata ragu matuqa idan ma bata tafi baki daya ba.

Ita dai tasan Tahan ya mata alqawarin ko me yake yi zai bari ya tabbatar yazo qasar canada don taya ta murnar gama makarantar ta.
Ta dai dade da sanin Ummi ta fada mata bazata samu zuwa ba, saboda kula da Mahmoud da makarantar shi, dadin dadawa kuma tace bata jin dadi sosai.
Amma kuma ta mata alqawari su Deedee zasu taho mata da little, yarinyar da take maye musu gurbin Maryam a zukatan su.

"Kiyi haquri Tim tim, bai samu visa bane shiyasa. Yace a gaida ki sosai".

Ji tayi kamar ta naushi yaya Haidar da yayi maganar, idan har su zasu samu visa meyasa yaya Tahan bazai samu ba?
Bayan kuma shi yayi mata alqawari, shi ya qarfafa mata gwiwar dawowa makaranta.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now