Chapter 4

92 7 1
                                    

*QADDARAR MU CE*

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                     *4*

Parking yayi a bakin gate din wani madaidaicin kerarren gida, fitowa yayi daga cikin motar ya kutsa cikin gidan. Baiyi mamakin jin shiru ba sanda ya shiga gidan sanin cewa babu ko mai gadi a gidan.
Kofar parlourn ya kwankwasa, jin shiru ne yasa shi ciro wayar shi daga Aljihun wandon suit din dake jikinshi, bai kai ga dialing number ba ya ji an bude kofar.

Matashi ne ya bude qofar wanda a kalla zai kai sa'an Hafeez din sai dai shi din ya dan fi Hafeez jiki kadan hakan zaisa mutum yayi tunanin ya bawa shekara 40 baya amma a zahiri kam bai wuce 35 ba.
"Ai da kiranka zanyi tunda kai kurma ne bakajin knocking." Hafeez ya fada yana hararar shi.
Murmushi Ibrahim yayi yace "ko kuma kai makaho ne da baka kula kofar a bude take ba ko"
Ibrahim ya fada Hannun shi rike da Handle din kofar.
"Na fa manta ba gidan masu iyali bane, da na afko kawai"
Hafeez yayi zolayar yana ra6ewa ta gefen ibrahim ya wuce cikin parlourn..

Harararshi Ibrahim din yayi ya dan kai wa Hafeez din duka sannan ya maida kofar ya rufe.
A kan doguwar kujerar parlourn suka zauna Hafeez ya kwantar da kanshi a jikin kujerar ya kuma mike kafar shi a kan centre table din dake kusa da kujerar yana sakin wata ajiyar zuciya yace "kaiii! Na gaji wallahi, yanda sanyin AC nan yake shiga ta kyau kawai nayi bacci." 
Ibrahim dake rike da remote yana  kokarin canja channel din tv dariya yayi yace "ba ku kun rantse sai kunci da boko ba?ko a banza kake matsayin manager banki? Ai yaro wahala bazata kare muku ba sai kunyi retire"
Harararshi Hafeez yayi yace "sannu dan kasuwa, shiyasa kai gashi nan kullum kana gida sai faman narka qiba kake"
"Naji bakomai, gara in zauna a gida inyi dumurmur abu na" Ibrahim ya fada yana girgiza jikinshi.

Dukkansu dariya sukayi kafin Ibrahim ya nutsu yace "Abokina, meke faruwa ne? Ni fa tunda ka kirani kace min zaka zo nake ta saqe saqe, ko wannan karan ma wata matar ka dada nemo min ne malam Hafeezu mai dalilin aure?"  dariya ma ya bawa Hafeez sannan ya girgiza kanshi yace "Ai na sallama ka yanzu, idan ka gaji dan kanka kayi"
Shiru Hafeez yayi ya dan gyara zaman shi sannan ya fuskan ci Ibrahim yace "Ina cikin matsala Abokina, Abubuwa duk sun cunkushe min wallahi."
Remote din dake Hannun Ibrahim ya ajiye sannan ya karkata yana facing Hafeez yace "me yake faruwa? Ba dai matsalar ka da Aysha bane har yanzu"

"Har da shi ma, don ita wannan in da sabo mun saba, Har yanzu kowa yana kan bakan shi daga ni har ita, amma babban abunda yafi damuna yanzu Hadeeza ce"
Kallon Shi Ibrahim yake da mamaki yace "Hadeeza kuma? Ta fasa auren ka ne ko yaya?"
Da sauri Hafeez ya girgiza kanshi yace "A'a ko kadan, amma kamar na dauko hanyar da zata fasa din"
"Listen man! Ka fito 6aro 6aro ka min bayanin abinda ke faruwa duk ka sani a duhu ni kam" Ibrahim ya fada da serious face yana kallon Hafeez.

Hafeez bai bata lokaci ba ya kwashe labarin rashin lafiyar Mahmoud da bukatar Hadeeza akan ya bada kodar shi da kuma yanda tun ranar ya kasa komawa asibitin.
"Ina jin tsoro Ibrahim, kuma sai nake ganin kamar idan naqi banyiwa Hadeeza Adalci ba" Hafeez ya qarashe maganar cike da damuwa.

"Tirqashi!" Ibrahim ya fada yana shafa gemun shi sannan ya maida kallon shi ga Hafeez "To kai yanzu me ka yanke?"
Wani kallon banza Hafeez ya watsawa Ibrahim yace "Kaji min dan rainin wayo, da na yanke wani abu me zai kawo ni wajen ka?"
Dariya Ibrahim yayi sannan ya fuskanci Hafeez
"Abokina gaskiya bazan boye maka ba kana ruwa, Tsundum ma kuwa" ya fada yana maida kanshi jikin kujera yana dariya.
"Bana son iskancin banza Ibrahim, zaka bani shawara ne ko kuwa zaka sa ni a gaba kana dariya in tashi in tafi?"
"Ohk ohk, kayi Hakuri" Ibrahim ya fada yana gyara zamanshi sannan ya maida kallonshi ga Hafeez "maganar gaskiya Hafeez kazo da abunda a yanzu ban san me zan ce maka ba, kaga na farko dai nasan hakan kamar jihadi ne idan kayi, na biyu kuma nasan kana son Hadeeza, to amma abokina abinda ka iya zuwa ya dawo ake gudu duk da dai bama fatan ma wata matsala"
Numfasawa Ibrahim yayi yace "To amma ga shawara, me zai hana kajewa Hajiyar ka da wannan maganar tunda ka ga tafi kowa hakki a kanka kuma zata fi mu sanin abinda ya dace. kasan manya da hangen nesa."

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now